RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA12
Tana bukkarta tafaraji kamar ana kuka kasa kasa,saita share don kuka bawani sabon lamari bane agidan,saboda babu wanda ya tsira daga muguntarshi sai iya,kowa duka ake,shiyasa ma babu wani abin damuwa aciki.
Ji tayi ihun ya karu hakan ne yasata lekowa,mezata gani sadiyarta ce yake duka baji ba gani,yarinyar nata birgima akasa,kowa yana kallo,ai dasaurinta ta karasa ta fara kokarin kare yarinyar ya hada da ita tunda dama itace dalilin dukan ai,yayi yayida yarinyar tafada mishi mai tace mata jiya,taki fada,har cewa yayi zai kasheta taki fada saboda ai ita ba mahaukaciya bace,tasan tana fada mishi zaiyi wani haukan to wai rashin fadar nata ne yasa ake mata wannan mugun dukan,tunda ansha gargadinta tayi nesa da ita,amma harda zuwa bukka suna zantawa.
"Allah yana kallonka fa duk abinda kakeyi,wallahi bazan daina gaya maka gaskiya ba,kai mugune Azzalumi"tace cikin kuka,amma ina yama bar kan sadiyan yakoma kanta ita kawai yake zubawa bulalar yana dukanta baji bagani,"kadinga abu kamar dabba,to ko dabba dai ai tasan danta,wallahi kaji tsoron Allah,Duk abubuwan nan dakakeyi......"ni kike gayawa haka? Nine dabba?Ya yarda bulalar tareda shaketa "nace ni kike gayawa haka?"amma inaa bata ko iya magana sai kakari datake har tafara saddaqarwa don a halin datake ciki yanzu mutuwar ma zata fiye mata komai,ganin dai idan yakara wasu yan mintuna zai iya kashetane yasa ya yarda ta gefe,tafara numfashi sama sama dakyar duk shacin yatsunshi sun bayyana a wauynata.
Haka dai aka musu farraqu itada sadiya,kememe aka ma hana yarinyar fitowa daga bukka,idan kuwa tafito to wanka zatayi ko bandaki zata shiga,shima uwarta na biye da ita,iyakacinsu da juna kallo da ido.
Haka dai rayuwa taketa gudana abubuwa sai wayanda suka karu,itada baiwa batada maraba, don batada wani amfani a wajenshi daya wuce tayi bautar gida,ga gorin da iya ta tsiri yi mata kwana biyu na rashin haihuwa wai ita bata haihuwa kenan yau wata nawa da aure amma har yazu shiru itakuwa bata cewa komai,don Addua take a kullum Allah yasa yacigaba da mantawa da ita karya mace zai kusanceta har asamu matsala,a Najeria Allah ya ceceta tasha tunda akwai kwayar hadiya,amma ananfa?idan fa tasamu ciki dolene ta haifeshi.
Allah dai ya taimaketa har yanzu bai waiwayeta ba,dasunan kwanciyar aure,amma daga tadanyi abin dabai gamsheshi ba ko iya,sai duka dacin mutumci,haka kawai ma ko batayi komai ba yaga tadan huta kwana biyu bai taba lafiyarta ba sai subirbida to ahalin daake cikima wasu kalamanshi dawani duka ma tadaina jin zafinshi ta saba.Duk wanda yasan farida ada yaganta yanzu karyarshi yagneta,saboda yadda tayi baki ta rame kamar kamar me,to ga malnutririon datake fama,duk hakora da kasusuwa sun fito dama jiki ba jiki ba,babu shakka idan takara wani dan lokaci acikin wannan yanayin babu abinda zai hanata karasawa (mutuwa)saidai wani ikon Allah,tana dai dagewa da ibadarta da addua baji bagani,tayita kuka kuma tana burin Allah yasake hadata da iyayenta da yanuwanta uwa uba tsohon mijinta yusuf data ganawa azaba baiji ba baigani ba bawan Allahn dayasota tsakaninshi da Allah duk mugayen Halyenta kuwa,Allah sarki masoyin kwarai,tasan yanacen suna rayuwarsu shida Abu,Allah sarki itama abun ta zalumceta,yarinyar da babu laifinta acikin duk abubuwan dasuka faru,amma tabi duk ta tsaneta,hmm,data zauna tayi hakuri sunyi zaman kishiyoyi datuni tanacen hankalinta kwance amma tazabi rabuwa dashi duk sonda sukewa juna kuwa,saboda shedan ya rinjayeta ga gata daya mata yawa,yau ina gatan,?gatanta bai tsinana mata komai ba sai wahala,tunda gashi ma har yanzu duk irin kudina mahaifinta yakasa nemota a duniya.
kai agaskiya tayi abubuwa dayawa itakanta tasani "ya Allah nasan nayi laifi abaya,na kuma tuba yanzu,Amma nasan dukkanin abubuwan dana aikata ne suke bibiyata kaji kaina ka kawomin sauki ya Allah,shine adduarta a kullum".
Ganinshi tayi ya shigo kamar an jefoshi dama babu sallama,"kitashi kije kiyi wanka kizo"yace yana muzurai,bayan ya wurga mata sabulu,dawani dan abu a kwalba daga dukkanin alamu turare ne sai wata yar rexa(tayi shaving kenan,sai kace tunda tazo yataba damuwa yabata wani turare,bayan kullum saidai tayi wanka da ruwa tunda sabulunta ya kare tayi tayi ya hana yace ta goga toka),banza tayi dashi tasake gyara kwanciyarta,"ba magana nake miki ba"ya daka mata tsawa, ko ajikinta saima tsaki dataja,tariga tagane manuafrshi tasan meyazo yi,yau kimanin wata kusan nawa kenan a wajen nan bai taba nemanta ba dasunan kwanciyar aure sai yau,shima yau din ta tabbata don iya tayi magana ne tayi zancen,rashin haihuwa,to ita kuwa yau dinnan saidai duk abinda zai faru yafaru don bazata yarda ba wallahi,ai bai sake mata magana ba sai dukanta daya shiga yi yana kwada mata mari,don tayi banza dashi,"ni zakiyiwa gardama kina matata na biya sadakinki?"Kuka take amma kememe taki kulashi,haka ne yasashi kara hasala,ya fara kokarin rabata da kayan jikinta,ta karfi,dukda dai ba wani karfi bane da ita,amma kokawar takeyi itama don babu abinda zai sa ta rissina dawuri haka,don babu abinda yake kara tada mata hankali kamar daukan cikinshi,wallahi bazata iya ba,ihu tafarayi kamar ranta zai fita ganin yana nemancin nasara,kowa yanajinsu,tunda dare bai waniyi ba,ganin dai dagaske idan ta kyaleshi zata cutu hakan yasata dintso kasar kasan dakin ta watsa mishi a idanunshi,ta fita tsakar gidan aguje,don batayi soro ba ma tasan sauran,"rikicewa yayi don bai taba jin azaba ba irin wannan,hakan ne yaaashi fitowa a daddafe yafara yana ihu shima yana neman ruwa don wanke idanun,duk tana gefe tana kalonshi sai kuka take saboda ita kanta ta tsorata tazata mutuwa zaiyi duba da yadda yabi ya haukace lokaci guda,kafin kuce meye wannan kuwa sauran matan gida sun fito harda iya,rikicewa tayi itama,dubada halinda yake ciki, itace mai taimaka mishi ana wanke ido dakyar da sidin goshi aka samu idon ya budu,amma koba komai yaji jiki,"meyafaru ne?"tace tana sake goge mishi idanun,bayan ta zaunar dashi kan tabarma,"yarinyar cen ce takeson kasheni"Yace tareda nunata tanata rakube rakube ajikin bukka tana kuka," kasheka kuma?to kafin ta kashekani zan kasheta" tace,tasa sauran mata dake tsaye su dauko mata ita sukuma abin nema yasamu suna farinciki suka kinkimota sadiya na gefe zata fara kuka cikeda tausayinta iya ta katse mata tunani bayan tace ta karyo mata reshen nan na bayanta,"bazan iya ba"yarinyar kawai tace tareda juyawa tasshige bukka,batareda ta jira ansar iya ba,baki bude uwar tata tabita da kallo,"kiyi hakuri iya bansan meyake damun yarinyar nan ba duk ta zama wata iri"tace cikeda ladabi kanta akasa,"eh dole tazama wata iri ai tunda kuna kyaleta tana muamula da wannan jahilar" (wai farida) "har dakinta kuka bari tana zuwa dole ta koya mata rashin tarbiyya,ai,"kai karyomin reshen nan nace"tace dawani yaron na tsaye,cikin zafin nama da tsananin bacin rai abdallahn ya mike dakanshi tareda dakatar da yaron,ya karyo wani zungureren ice,yace su kawo mai ita bakin bishiyar tsakar gidan,yashiga yadauko igiya,haka kuwa akayi aka kawo ya daureta tamau ajikin bishiyar nan,bata ko iya motsi sai hawaye,don tasan tata ta kare yau,amma fa gwara hakan akan dai saduwa tashiga tsakaninsu tasami ciki,gwara ya kasheta.
zuba mata icen nan yafara,baji ba gani,tafara ihu kuwa iya karfinta,yasamo wani tsumma yatura abakin,wato shi bai kasheta ba sai ita takeson kasheshi,to gwara ya hallakata tun kafin ita ta hallakashi don yaga take takenta.
iya ma baa barta abaya ba bakin cikin zata kashe mata da ko ta makantashi ne yasata jibgarta itama.
saida yayi mai isarshi sannan ya kyaleta yashiga harkarshi yakuma ce duk wanda yagani akusada bishiyar nan shima zai hau sahu.Dahaka duk suka shige bukkokinsu donyin bacci,tunda dare yayi sosai,bayan sun kare mata zagi,masu mari nayi masu duka nayi,don abune dabaa tabayi ba tayi zata hallaka musu miji,tayi sabo,dole ayi maganinta,haka suka shige duka,shida iya nakan tabarma suna zantawa,aka barta daure ajikin bishiya,"ni naji tana ihu dazu daka shigar mata meya faru ne?"iya tace don jin kwa waf,"babu abinda yafaru fa,gani nayi tunda tazo babu abinda ya hadani da ita shine nashiga,take wannan ihun kamar zan cire mata rai"yaja tsaki,"Au dama babu abinda yataba shiga tsakaninka da ita ne?ashe shiyasa bata haihu ba har yanzu,nama zata juya ce"ta tabe baki,"tun kafin muzo garinna acen Najeriyar na kusanceta wajen sau nawa amma shiru,juyar ce dai duk yadda akayi,don yaci ace tasamu ciki ai shegiya"ya kishingida,"toooh idan dama bata haihuwa ma ai shikenann dama basonta nake ba bare abinda zata haifa,kullum tsanarta nake karayi,"yasake jan tsaki,"wai meyasa ma ka auri yarinyar nannne ma?,nafa tsaneta"cewar iya,"nima bansaniba iya don nima bason nata nakeba"yace hankalinshi kwance,wasu zafafan hawayene suka zubo mata ,donduk zantukan dasukeyi akunnenta tanaji,wato dai sagaske baa nigeriar take ba kenan gashi ya kara tabbatar mata da bakinshi?.
Tana cikin tunane tunanen nan,aka fara walkiya hadari ya gangamo ga iska mai karfi,kafin kuce meye wannan an fara maka wani ruwan sama irin mai karfin nan,babu wanda yako keko,bare a ji tausayinta,Allah yaso ma tsawa bata kasheta ba.
Sadiya dataki bacci tana jira kowa yayi bacci tacsaci jiki tafito,jin shiru ne yasata lallabawa,ai kuwa tana tasowa uwar tamata charaf ashe tana lura da ita batayi bacci ba sanin hakanzata iya kasancewa,dole tanaji tana gani ana ruwan nan Farida na daure a bishiya an hanata fitowa.
Har gari ya waye, gashi babu halin yin sallah.Haka jamaar gida suka fito sunata kai kawo hankalinsu kwance,babu wanda yako kalleta,"Don Allah ku kawomin ruwa inyi alwala"tadinga rokar duk wanda yazo wucewa ta wajen bishiyar amma inaa saidai amata mugun kallo ajuya,tunda ta aikata sabo.
Intakaicemuku dai ba shi ya kwanceta ba,sai yamma likis lokacin tariga tagama galabaita, aikuwa igiyar nabarin jikinta ta sulale ta fadi,,"au,au,kika sake kuwa(suman)?to kuwa kinyiwa kanki,tunda ai nagaya miki,babu ruwan dazan sake yayyafa miki wai don ki farfado tunda bakida wani amfani,idankinga dama ki dawo hayyacinki,idan kuma bakiga dama ba kicigaba da kasancewa ahaka har sai anyi ruwa ya dakeki,mara mutumci"ya juya yayi tafiyarshi,tana kwance kamar gawa ,sunata harkarsu,yan yaran dasuke wasansu suna guje gujene dasukaji yana ambatar ruwa suka debo suka suka shiga kwara mata kuwa,su fa wasansu suke suna jin dadi suna nishadi,basusan mesukeyi ba,a firgice kuwa ta farka tareda sakin wata ajiyar zuciya mai nauyi,hakan ne yasasu kyalkyalewa da dariya,sun zata wasa ake,suka cigaba da tsokanarta suna gudu don yau ko wanka ma baa musu ba tunda baiwar asume take.