RUWAN DAFA KAI 2

5.6K 278 6
                                    

RUWAN DAFA KAI 1
Na SUMAYYA DANZABUWA

Yau kimanin sati guda da aurensu kenan,zaman nasu dai sai godiya zamu iya cewa kawai,don Wata irin muguwar tsanarshi takeji haka kawai,dukda kuwa shi tanashi bangaren yana nuna mata kauna iyakar iyawarshi,don duk abinda tanuna bataso yana kokarin kiyayewa,don  ko kwanciyar auren ce ma hakuri yake idan tace bataso wai don duk azauna lafiya,amma inaa duk abinda yayi baya birgeta,(to nikuwa nace dama duk abinda akayi shi ba don Allah ba ai dole kuwa aga ba daidai ba,wane biladama?).

Tunda akayi auren kawo yau,bata taba ganin wani nashi ba,maana abokai,yanuwa,da uwa uba iyayen nashi dayace shi kadai suka haifa,ita kuma sai take ganin dai a matsayinshi na dansu guda daya tilo,yayi auren fari amma babu wanda zai ko leko yau kwana kusan nawa kenan?,"hm to meye nawa ma aciki kada Allah yasa suzo dinma mana,dama waya damu?"sune zantukanta aduk sanda lamarin yafado mata,don hakan bawai damuwarta bane,don ko tambaya ma bazatayi  ba ko a kwalarta,dama basotake suzo bama,bare har ace zaa wani saba,to itada ba dadewa zasuyi tare ba idan tace duk mijin data aura saita saba da yanuwanshi da abokan arziki ai da matsala,hakan ne yasa ake cigaba da zama a hakan baicemata komai ba akan yanuwanshi itama bata tambaya ba,tana daita  nuna bakaken halayenta yana hakuri yana sharewa,don hatta girki ma shi yakeyi,safe,rana,dare,ko fita ma bayayi,saita zama dole,to abinku da CEO daba a karkashin wani yake aiki ba,sai yadda yaga dama,ko wannan yawan wayar dayakeyi kafin aure duk bayayi yanzu yadau hutun angonci.

"Zanfa koma aiki saboda hutuna ya kare,kuma besides ma zaman gidan nan bawai dadi yakemin ba,ya isheni"tayi maganar suna zaune yana janta da hira tana basarwa kamar koda yaushe don duk abinda yace haushi yake bata,shiyasa ma bata taba jin dadin hirar,wani lokacin idan ya isheta da magana kamar tasa abu ta doke bakin ta zubar mishi da hakora takeji,amma dai saita dake takai zuciyarta nesa,to fa agaskiya hakurinta yakusa karewa,anya kuwa wata biyun nan data daukar wa kanta zata iya kaisu kuwa anya?gashi satinsu daya amma ji take kamar an shekara.
"Haba rabin raina abin kaunata,yanzu zama danine kike cewa ya isheki?ni wallahi duk kinbi kin chanja,kin daina sona ko namiki wani abin ne?"yace cikeda marairai cewa,don lallabata yake matuka tunda yasan kadan take jira,duk rashin mutumcin datake yana sharewa ne baya biyewa saboda yanzunnan zaayi dan abu sai tayi zancen saki,shikuwa babu wannan a tsarinshi.

"Niba haka nace ba,zaman waje daya ne dai daban saba ba shiyasa nagaji"tabada ansar tanata wani yatsine yatsine,"kidai dan kara hakuri mu more amarcinmu kinji"yace bayan ya koma kusa da ita,"hm"kawai  tace ta tashi,don zama taredashi ma bata fiya so ba.

Yau kimanin kwana biyar dayin zancen kenan,har yau ya hanata fita,don rannan ma harta shiryo ya kanainayeta da kalamai,yadinga bata hakuri harda kuka,hakan yasa ta hakura,amma da sharadin sati mai zuwa zata koma aiki don cin amarcin ya isheta ita,bawai don son ranta take hakuri ba,aa tana dai yin ne kawai don ta kokarta tagani ko zasu iya kaiwa lokacin data kayyade na rabuwa dashi din,ace kowata baayi da aure ba amma ji takeyi kamar ta shakeshi?wannan wane irin abune?,kai agaskiya bin son zuciya baiyi ba,dama haka auren rashin soyayya yake,Tabbas bataga laifin mata ba wayanda suke kashe mazajensu sakamakon auren dole,don a halin daake ciki itama yanzu,Allah dai  ya kiyaye kawai.

Taddashi tayi kishingide adaya daga cikin kujerun palon yana kallo,yadora kafa daya kan daya akan centre table din,"mtsw,jibeshi daallah sai kace shi yasiya?"tace aranta cikeda jin haushinshi,tariga tagama shiryowa don fita aiki abinta,don bazata iya jiran wani satin ba tana bukatar space,tasha kwalliyarta kuwa kamar koda yaushe tana zuba uban kamshi,don bawai yardarshi take jira ba,"aa ina zuwa haka gimbiyar mata,kika sha irin wannan ado haka?ko ni akayiwa n....."bakai akayiwa ba aiki zan tafi"ta katseshi donba tsoronshi take ba ai,"aiki kuma?haba rabin raina,nazata mungama magana akan cewar sati mai zuwa zaki koma din,bafa mugama cin amarc......"kaga,ni nagaji dawani lamarin cin amarci ni aikina zan koma"tace cikeda rashin kunya danuna isa"to gimbiyata,naji adawo lafiya,Allah ya kiyaye"yace fuskarshi daukeda murmushi,"saina dawo"tace,"Allah sarki,ji yadda yaketa lallabani,kai mutumin nan badai hakuri ba,amma banasonshi ne shine matsalar"tacigaba dazancen zuci tareda nufar kofa,saidai kuma me?Budewar duniyar nan,kofa taki buduwa,tayi tayi,shiru,ganin hakane yasashi tasowa don taimaka mata,tareda fara nuna tashi bajintar wajen amfani da karfinshi amma shiru,"to meya sami kofar"yacigaba da takarkarewa don ganin ta budu,"bakomai bari inbi ta kitchen"tanufi kitchen,abin mamaki itama taki buduwa,"meke faruwa ne?"ta ce cikeda rashin fahimta,"wallahi bansani ba,wannan dai dama baa taba budeta ba(ta kitchen din)inaga shiyasa,amma karki damu zasu budu bari in sa musu grease"yace,"to ka kirawo masu gyara mana"tasake cewa,don tana cikin tsananin damuwa koba komai dai tayi niyyar idan tafita saiya ganta amma daga dukkanin alamu hakanta bazai cimma ruwa ba tunda kofofi sunki buduwa.
"Aa bawani abin damuwa bane ai baby,dama sukanyi haka lokaci lokaci,zasu budu karki wani damu"yace tareda dauko wata roba dabatasan komeye aciki ba yafara tsiyayawa kofofin don taimakawa wajen budesu.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now