RUWAN DAFA KAI 2

1.9K 138 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

11

A daren ranar Abba ya dira a maiduguri bayan kuwa babu yadda mama batayi dashi ba akan yayi hakuri,yazauna tunda zuwan babu wani amfani amma ya dage saboda hankalinshi yakasa kwanciya tun faruwar wannan lamarin a nashi tunanin idan yaga motar tata watakila yadan sami sassauci.

kai tsaye kuma ofishin yansanda ya wuce inda aka kirashi dazu,suma mamaki ne ya cikasu,na wannan muttumi,wannan wane irinso ne  tsakaninshi da yar tashi?bafa cewa akayi anganta ba,aa motarta kawai akace angani  amma shine ya rikice haka  saida yazo, kodayake ai dama mai kudine shiyasa  bazai damu da asara ba suka dai dinga gulma,don bazasu taba gane yadda alamrin yakeba,dole aka kira shi wancen bawan Allahn daaka siyarwa motar ya bayyana a station din tunda  su dai bazasu  iya kamashi ba tunda bashida wani laifi siyan mota  yayi da kudinshi,zuciyarshi daya,baisan haka alamarin yake ba hasalima wanda yasiya din daga wajenshi shima baisani ba.

Wayyo,tabbas motarce kuwa,Abba yace aranshi bayan yafito,ai kamar jira yake sai kuka yana share hawaye kamar karamin yaro,sudai mutanen kawai binshi suke da kallo cikeda mamaki,"nacuci kaina nacuci yarinyar nan"yadinga sambatu yana kuma zancen zuci.

Haka ya shafe kwanaki kusan nawa a garin maiduguri,wai ko Allah zaisa a dace amma inaa babu wani sabon labari,an rasa wancen mutumin wanda shima ya sai mota kafin yasiyarwa  nayanzu,don ko wayarshi ma bata yi,(to dama ya zaayi tayi,bayan shima dan congo ne tare fa suka tafi,kyal kyal kyal),dole haka Abba ya hakura yanaji yana  gani ya juyo yadawo gida ya tattara dukkanin lamarin ya fawwalawa Allah don yanzu ya saddaqar yasan Allah ne kawai zai kawo mafita,su ahalin daake cikima ko gawarta suka gani zasu dan sami sauki tunda ko ba komai sunsan su suka binne kayarsu.

"Ke wato haka kika raina suma ko,daga anyi abu saiki wani yanke jiki ki fadi kamar an cire miki batir"yace cikeda rashin mutumci bayan ta farfado  ta fara zare idanu,don tuni ma sauran jamaun sunyi  tafiyarsu sun kwanta sadiya ma tana cijewa bazata tafi ba uwarta  ta daddaketa ta jata ta tafi da ita.

Kuka kawai tafara,cikeda tausayin kanta don hakika hankalinta in yayi dubu ya tashi  ta riga tagama tsorata,"kinji ma nagayamiki idan kika sake wannan iskancin(suman),kyaleki zanyi,idan kinga dama karki farfado,ki tafi daga cen ba damuwar kowa bane,to inbama iskanci ba da harme ma yafaru dazaki wani suma me akayi?nace meaka miki" ya daka mata tsawa,don ko kawowa ma baiyi ba arai wai sadiyar zata fada mata wani abu dahar zai tsoratar da ita haka,ita kuwa tariga ta gama tsorata babu abinda take sai kuka don ta saddaqar da kubutarta daga wannan wajen,,,mikewa yayi bayan yaja dogon tsaki,cikeda bakinciki zai fita,"meyasa kakemin haka don Allah,mena maka,idannayi maka wani abund  ka yafemin kayi hakuri kabarni haka don Allah h..."wani wawan mari ya kwasheta dashi  jini yafara fita daga hancinta,"ke idan taurin kai kikeji dashi fa  ni nafiki,dan ubanki sau nawa zan gargadeki akan wanann tambayar ta iskanci ko ni saanki ne,ko kuwa tsabar rainani dakikayi ne?"ya hayyyako,"bamagana nake miki ba"yasake mata kafa,"ban rainaka ba Wallahi kayi hakuri"tace dakyar cikin kuka"naji dadi dakika fada da bakinki,idan bakida hankali,kisake maimaitawa kiga idan zaki kara dadewa a duniya"yajuya ya fita(hmmm,jahilci baiyi ba,rayuwa dai da mutuwa duk a hannun Allah suke,sai sanda yaso yake karbar abinshi).

Bazata taba kuskuren gaya mishi ko tabari yasan wai tasan  inda take ba,aa ayita tafiya ahakan har sai sanda Allah ya kawo mata mafita,don idan ta kuskure tabari yasan tasani tofa komai akan sadiya zai kare,watakaila yamata wata illar tunda ba hankali gareshi ba babu abinda kuma yamai zafi nawai ko don ita yarshi ce shiya haifa,aa baruwanshi ganin yayan ma sun mishi yawa bai damuba,takuma tabbatar da rashin hankalin nashi ne ta  yadda yake hora yaran,to  bama su ba har iyayen nasu ba kyalesu yayi ba,don idan ya fara jibgarsu kamar zaisa su bakunci lahira.

Sanin inda take dinnan bawani sassauci yakawowa rayuwarta ba,saima sabon tashin hankali datashiga,don yanzu ta kara saddaqarwa tasan indai ba wani ikon Allah ba,to fa ita kuma anan zata dawwama,tunda ta ina zata gudu?ga gida babu mafita,idan ma tasamu ta fita din fa?ta tabbata awani kasurgumim kauye take,dababu mota babu komai kafin tagama neman mafita ma watakila akamata,itakam tasan tata ta kare.

"Tabas mutumin nan bashida imani sam,zai iya kasheta wannan wane irin abune tsakani da Allah ka auri mace kuma ka gudu da ita baa san inda kuka tafi ba,kuma ance har dukanta yake fa,haba"tayi zancen fuskarta dauke da damuwa saikuma tayi shiru,babu abinda yake cewa sai uhm,uhm yana latse latsen wayarshi,"mine bakacewa komai"kallonta kawai yayi yacigaba da abinda yake,"hmm Allah sarki,wallahi na tausaya mata,amma babu komai akwai Allah,Allah yafishi a......"

"Nifa kinga matsalata dake kenan,"ya katseta,"daukan damuwar abinda ba shafarki yayi  ba ki dorawa kanki ina ruwanki?,kiyi addua kawai kiyi shiru,"yace tareda kauda kanshi gefe don tasan cewar fa yayi fushi kuma abinda  tayi baiji dadinshi ba,ita batasan meyasa ba tunda taji labarin abinnan take matukar tausayin faridan shikuma bayason hakan,tazata an dan kwana biyu da rabuwar tasu daya kamata ace ya manta dakomai,amma bayason ko zancenta ayi,"Don Allah kayi hakuri Mine,karkayi fushi dani,kasan dole zan shiga damuwa,saceta fa akayi bawai mutuwa tayi ba,kuma don Allah fushin nan dakakeyi da ita,ka yafemata kayi hakuri haka don Allah"harda yar kwallarta,"ai nasani sarai  babu dadi  amma meye  naki ke kina nan daga samun labari sai zakewa?Kinbi kin dauki abu kin saka arai,duk abinda yake faruwa da ita ai ita ta tsoma  kanta aciki bawani ba,kuma dama ai nafada mata sai Allah yamin sakayya idan har ni na cuceta azaman mu,sai tazata abin wasa ne,gashi tun baaje ko ina ba,kuma zancen hakuri da yafiya dakikeyi ai ni na dade ina hakuri,nakuma yafe mata,amma Allah ai ba azzalumin bawanshi bane,bazai yiwuba tayi badaidai ba kuma shikenan tayi tunanin taci bilis,inaaa,bazai yiwu ba ai"yace tareda cigaba da latsa wayarshi,"hakane,ka kara hakuri don Allah kaji,Allah dai ya bayyanata shine kawai"Amin"yace kawai don bama son zancen yake ba dubada yadda labarin yacika duniya kowa yasan metayi,don mutane dayawa ma sun kikkirashi wayanda basusan sun rabu ba,to shi kam mezaice meye amfanin magana,adduace kawai ta dace da ita,"wayyo Allah kowane hali take ciki yanzu? kai rayuwar  nan acike take da mugaye"ta katse mishi tunani,banza yayi da ita,hakan neyasa ta tabbatar da tabbas yayi fushi tashiga bashi hakuri,tareda dan kishingida ajikinshi.

Su zainbau abu kenan ana cen rayuwa sai kara chanjawa take,tayi wani kyau da haske ta ciko tayi bulbul kamar ba ita ba,Abin dai sai wanda yagani,tanata zuwa makaranta abinta har karatu yayi nisa tanata kara kilewa tana wayewa,ga Amin da babanshi suma  sun kara fes dasu sun kara kyau don rayuwa ce sukeyinta  cikeda jin dadi da kwanciyar hankali basuda wata damuwa,kullum karajin kaunar juna suke azuciyoyinsu,don duk yadda yake buri yake kuma mafarkin samun rayuwar aure cikeda jin dadi yanzu Allah yabashi babu abinda yake sai godewa Allah babu dare ba rana.

A halin da ake ciki ma dai yanzu har dan yaron ciki ne da ita dabai wuce watanni  biyu ba zuwa uku.sai muce dai Allah ha raba lafiya.

Alhajin da aka gama magana safina zata aura,dai an janye maganar aure,duba da halin dasuka tsinci kansu yanzu,Na ganin rashin yin bincike shiya tsundumasu cikin damuwar dasuke,dakanta tasami Abba tace yakamata a bincikeshi dakyau don haka kawai tafara jin yana fitar mata arai,saboda istikhara da mama tasata tayi,(yanzu fa jin maganar mama akeyi,kamar kamar me,tana fadar abu zaa aiwatar cikeda ladabi da biyayya).
Tabbas tun kafin ma tayi magana Abban yasa an fara binciken kwakkwafi batareda sanin kowa bama,to ilai kuwa Ashe irin matsolon nan ne,bazaaci kudinshi ba,bayan Allah ya wadata shi da  arziki sarai amma iyalinshi ko oho,babu cin yau agidan bare  na gobe,bayan babu abinda ya nema ya rasa,kuma ya hana matarshi aiki bare sanaa,ya dunkufeta agida,shikuma atitir yana aikin yawon zagaya duniya yana shanawa,daga yaje waccen kasar sai ya tafi waccen,ga neman mata kamar kamar me,don duk kasar dazaije idan bai tafi da karuwarshi ba to zai nema acen,kai mugayen dabiun Alhaji Tanimu dai dayawa,hakan ne yasa aka janye maganar auren, don bazai yiwu ba Abba yanaji  yana gani yasake tsunduma yarshi cikin halaka yazo ya kara dana sani,angama wannan dashi.

Hakika abubuwa sun chanja matuka agidan daga yaran har Abban kowa ya nutsu,don yanzu mama tanayin magana ake bi,tana bada shawara zaa karba,Zama lafiya akeyi kwarai da gaske,kowa ya chanja halaye,yazama mai kirki,Allah sarki rayuwa kenan,mama tasha hakuri,yanzu take cin ribar abin.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now