RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA30
Hmm,yau da Gobe bata bar komai ba,sannu sannu bata hana zuwa,Abu ta kammala karatunta har sun dawo gida Najeriya.
Kuma dama kafin su dawo Hajiya tasaka aje amusu yan share share da yan gyare gyare kasancewar an dade baa nan,hakika Kowa yayi farin ciki dakuma murnar ganinsu,ga yara duk sun girma sunyi wayo abin mashaallah saidai wanda yagani kawai.
Duk wanda yaga Abu sai yayi magana,saboda yadda tachanja gabaki daya,Har wani haske tayi ita datake baka takara sheki da kyau.Sai bayan kamar sati daya da dawowarsu ma Bash yaji labari wajen wani abokinsu,hakan ya bashi mamaki matuka,don tun wancen lokacin da yusuf din yayi blocking dinshi shikuma yaketa lalubar wayar tashi baya samu ko labarin haihuwar Amina ma duk yadda yaso yamishi albishir hakan ya gagara,dole yaje dakanshi wajen Hajiya don jin ko lafiya, inda ta tabbatar mishi kuwa dacewar komai fa kalau,to anan ne yagano cewar babu tantama aminin nashi blocking dinshi yayi saboda tsananin kishi donma karya nemeshi,kuma shi nemanshi dayake tayi ma fa don ya tabbatar mishi da ainihin zancen ne yace kuma wasa yake,amma hakan bai samu ba,tunda Hajiya tabashi wanann ansar kuma, nacewar wai yana cikin koshin lafiya, gab da zai shigo ma (shi bash) din suka gama magana itada yusuf din awaya,hakan ne yasa ya watsar da zancen ya rabu dashi.
Baiyi wata wata ba yaje har gidan,yayi saa kuwa yana nan,maigadin gidan ya aika yace yace yayi bako ya fito,koda ya sami sakon,saida yafara lekowa ta window tukun ya hango bash din,dan tsaki yaja don tsananin bakinciki da kishi dasuka taru suka turnukishe lokaci guda,komai yadawo mishi sabo,"ko mezaimin oho?bayan cin amanata dayayi,mtsw"hardai zaiki fitowa da, kuma dai kawai ya fito din,fuskar nan adaure babu annuri,rai abace,ya karaso inda bash din yake zaune,yanemi waje yazauna shima ya kauda kai bayan bash din ya mika mishi hannu,dan murmushi yayi kawai cikeda tausayin aminin nashi,"Kai kuma haka akeyi ko?zaka dawo gari bayan duk wannan shekarun amma ko ka sanar dani,h....."akan me zan sanar dakai"ya hayayyako kamar jira yake dama,"nace akan me?"yusuf wai meyake damunka ne?kayi blocking dina bana iya kiranka ko a watsapp ma bana iya tura maka message menayi maka h....."au bakamasan mekayi ba?"yace baki bude cikeda mamakin rainin hankalin aminin nashi,"to ya zaayi insani kuwa,nidai nasan babu abinda yafaru kaine dai kadauki abin dazafi"ya kara,"ok,to nagane cewar zuwa kayi kacimin mutumci, fiyeda wanda kariga kayi abaya"yamike,don bazai iya zama ba yacigaba dajin wanann shashancin rainin wayon,"kadaiyi abin mamaki,to ni nataba ganin irin abu haka"dan tsaki yaja kawai yajuya zai koma ciki,"koba komai dai ai kayiwa madam din magana, akuma nuna min yaran kafin na tafi dai ko"ya kara,jin hakan ne yakara hasala yusuf din yashige ciki abinshi yabugo kofa.
(Bama sanan,Abu ta tafi dasu cen Gumel ganin Gida).Don harga Allah baisan mai Bash yakeso ba kuma ko mezai cemishi bayan irin mummuman abinda ya aikata mishi wanda ko amafarki sai ahankali dai kawai.
"Ya wanu haka ai,kabarshi haka kar zuciyarshi ta buga"zuciyarshi tace dashi,hakan neyasa yayi yar dariya sanann ya tashi ya tafi.Tunda suke da yusuf bai taba mishi irin haka ba tabbas wannan zancen ya bata mishi rai kenan,wai!ansha kishi,ansha wulakanci.
Sati daya da faruwar haka,Sunje gidan Hajiya shida Abu da yaran Hajiyar take cemishi yafa kmaata yakaiwa Farida danta taganshi,tunda dai Tana raye tana kuma da hakki akan yaron sarai,bawai don an rabu ba shikenan,"Saidai insaka Hamisu(drivern Hajiya)yakaishi"yace atakaice,"aa meyasa bazaka kaishi ba kai dakanka haba yusuf"cewar Hajiya cikeda kulawa,wai hajiya saita dinga zance kamar batasan meyake faruwa ba"nace meyasa bazaka kaishi ba kayi shiru"ta katse mishi tunani,"Gidan Bashir ne bazani ba Hajiya"yace cikin wata irin murya,"au,au to"to ai ita hajiya ma tamanta anyi wannan batu,tunda an dan kwana biyu,sai yanzu abin yadawo mata,lallai ma yaron nan,wato har yanzu baisan shi kadai yake dramarshu ba wasa kawai suka mishi da hankali daga faridan har bashir din,"meyasa bazaka ba"ta sake watso mishi tambaya,"Haba Hajiya,Harkin manta abinda bashir yamin ne?bawan Allahn fa kiri kiri kina gani yanuna min cin amana"ya kara,lokacin hajiya take tambayrshi rabonshi a bAshir din yace satin daya gabata,"kuma daya zo meyace maka"tasake tambaya,"babu abinda yacemin saima rainamin hankali dayasoyi,nayi shigewata na rabu dashi,wallahi Hajiya ban taba tsammanin irin wannan cin amanar daga wajen Bashir ba"yar dariya tayi,don ta fuskanci har yanzu bashir din bai bar mishi wasa da hankali ba kenan tunda sunma hadu wato amma baifada mishi gaskiyar lamari ba,hakan kuwa bazai rasa nasaba ba da lura dayayi abin yayi mishi zafi,"shiyasa kawai gwara Hamisun yakaishi ,"ya katse mata tunani,"Bashir fa bai kamata yazama makiyinka ba yusuf,ni tunda nake ma ban taba ganin aboki mai rikon amana ba mai kuma kaunar abinda abokinshi yakeso ba irin Bashir,tabbas Amini ne na kwarai"Baki bude yadinga kallonta cikeda mamakin kalamanta,"Hajiya wai kina nufin duk wannan rashin mutumcin daya aikata min shine rikon amana da kauna?,hmmm h....."Bafa wani auren farida dayayi,babu wani aure ,"hakika a wannan lokacin kanshi yafara daurewa kuma don yasan tabbas hajiya bazata mishi karya ba ai,"bai aureta ba Hajiya amma fa har katin daurin aure ya turomin kuma ma ita kanta da bakinta tafadamin aure zasuyi"yakara,nan hajiya ta kwashe mishi duk yadda zancen yake da kuma yadda suka hada abubuwan,duk din aga sun dawo tare shida faridan amma yayi kememe,"kuma inba dai aminci yayi aminci ba wane abokine zaisakawa danshi sunan aboki"ta kara,"wai kina nufin Amina ta haihu?"yace arikice,tareda dan zabura,sanin Bash din yariga shi aure sosai amma Allah bai basu haihuwa ba,sunje wajen likitoci kala kala amma baa dace ba,saboda lokacin da Allah ya tsara su haihun baiyi ba,to ashe baisani ba An haihun kuma ma wai sunanshi aka sawa yaron"ya salaam,Amma wane irin wasa ne wannan?gaskiya bawan Allahn nan ya shammaceni"yace tareda fara jin yar kunya kuma duba da duk irin abubuwan daya mishi ya gayyamishi magana,saboda yana cikin fushi,baisan shi yanacen yana mishi kokari ba."Eh wanaka yayi ai yayi maganinka tunda ka koyi son kai ka kuma gagara yafiya"hajiya ta kara,zancen ta ne yasashi sunkuyi dakai yana jin yar kunya,"Ka dauki yaron nan ka kai mata shi,kakuma samu ku daidaita idan bata samu wani ba don ko kwanaki dai nasan batayi aute ba"ta kara"Toh inshaallah"kawai yace ya tashi don shiga yafadawa Abu ta shirya yaran,don tunda sukazo dazu tana daki Wasu yanuwansu yusuf din sunzo suma anata hira,amma kuma me suna tsaka da zancen zataje kitchen tana fitowa taji hajiya na labarta mishi yadda ake ciki,hakan ne yasata dan dakatawa taji komai sannan ta koma,tabbas tayi farinciki da hakan,tawani bangaren kuma abin yazo fa inji mai tsoron wanka,tafara jin tsoron faridan kuma, tunda dai da kunnenta yaji yusuf ya amince zai dawo da itan,shikenan zaman kishi itada farida ya tabbata,to ita dai babu abinda take fata sai Allah ya daidaita su yasa suyi zaman lafiya,shine kawai.
Ai ba bata lokaci tashirya yaran duka tunda duk inda Amin din yayi yaruwarshi na biye dashi bazai yiwu ba atafi dashi shikadai abarta,inba haka ba tayita kuka,hakan ne yasa ya tasasu agaba suka tafi.
A kofar gidan yayi parking bayan da kuwa idan yaje hangame mishi gate ake sarai, ya shige,to amma yanzu fa ba da bace,hanzu sabon neman aure zai fara,yazamto kamar bako agidan,iso aka musu har palon baki,inda aka je aka sanar da ita cewar tayi baki,tunda batasan da zuwansu ba,ta tambaya suwaye aka cemata wai wani mutumi da wasu yara biyu,)kasancewar an sake masu aiki ba na da bane dasuka sanshi),"mutum da yara biyu?"tasake nanatawa,"to kice ina zuwa "taceda yar aiken sannan ta zura abayarta ta yafa mayafi,tafito,su mama ma basanan sun fita.
Muryarshi kawai tajiyo yana yiwa yaran magana tagano shine,zuciyarta tafara harbawa da karfi,dakyar ta karasa cikin palon cikin sallama,ya ansa tareda juyowa yafara kallonta fuskarshi daukeda murmushin nan mai kasheta,batasan ya akayi ba dai sai tsintar kanta tayi da maida mishi itama sannanta nemi waje tazauna,kasa magana tayi ta kalli kasa,kamar yau ta fara ganinshi,tabbas dagaske ne wannan sabuwar faridace,bawadda yasani ba abaya yace aranshi,ganin shirun yayi yawa ne yasa yafara magana,"ga yayanki nan nakawo miki,kigansu suganki"yace tareda dan turasu gareta to ancedai tsakanin da da uwa,abin mamakin Amin kwata kwata baiyi wata kyuya ba,baikuma wani ki zuwa wajen nata ba kasancewar baisanta ba,saima shigewa jikinta daya dingayi,kallon yaron kawai tadingayi bayan ta rugumeshi cikeda tausayinshi dakuma jin haushin kanta yadda tayi sake wata ta rainar mata shi ba ita ba,bayan da ranta da lafiyarta sarai,ai batasan sanda ta fashe dakuka ba,kallo kawai yusuf din yadinga binta dashi don dama yasan zaayi haka,wannan kukan nata bakomai bane illa nadama,saida tayi mai isarta sannan ta dakata,tafara yiwa yaron wasa,shikuma yanata jin dadi,ganin akwai alamun magana abakin yusuf dinne yasata cewa wata cikin masu aikin tadebowa yaran kayan wasa ,(na dan gidan safina ne),da kayan ciye ciye,ba bata lokaci kuwa ta lodosu yaran suka dukufa cikeda nishadi suka dinga gudanar da lamuranu,hakan ne yabasu damar zantawa.
Duk abubuwan dasuke ranshi yafito dasu ya gudanar mata,tareda nema amincewarta wajen sake aurenta,"amma idan kinsan Kinada wani wanda yakeanta miki don Allah don Annabi kisanar dani,don bazan miki dole ba,inaso dai in sake zama dakene amatsayin matata saboda kaunarki dana fuskanci bazan taba dainawa ba"ya kara,"hmmm anzo wajen,to yakamata dai zuwa yanzu ta fawwalawa Allah komai,akan lamarin auren nan,tunda gashi yau dakanshi ya tako yazo har inda take yana neman amincewarta wajen maidata,kuma fa itama tanasonshi ga danta dabazataso takara nesa dashi ba,kuma shi yusuf dinnan shikadai ne fa namijin data yarda dashi takuma yarda zata iya zaman aure dashi amma dai,...."bakice komai ba"ya katse mata tunani,dan murmushi tayi,cikeda jin kunyarshi kuma wai,"to zanyi shawara"tace kanta akasa,"To tunda kince haka mashaallah Allah yasa muji allhairi"yace,sannan suka cigaba da dan taba hira,dazasu tafi ji tayi kamar abar mata yaran,karsu tafi,tunda dai basa kyuya,cewa yayi karta damu zaa dinga kawo matasu,akai akai,kayan ciye ciye dasauran tarkacen yara ta hado masu yawa tabawa yaran,sannan ta rakosu tace ya gaida zainab,hardai suka tafi su mama basu dawo ba.
Koda suka tafi hanya babu abinda yadingayi sai tunaninta,kyakkyawar fuskarta na mishi gizo,Allah yasa dai karta watsa mishi kasa a ido bawai tace zatayi shawara ba,ya Allah kadubeni yadinga addua a ranshi sannan yawuce gidan Bash.
Ai bash naganinshi yasan tabbas yaji asalin yadda zancen nan yake don haka kawai yadda yakejin haushi nan nashi bazai tako yazo gidanshi ba,"daniska uban han kishi"yace bayan sun gaisa,dariya kawai yadingayi sannan yashiga bashi hakuri akan duk irin rashin kyautawar dayamisshi cikin rashin sani,to ma wai kai inbanda abinka tayaya zaayi kataba tunanin zan maka haka,?ni fa naga wautarka matuka,kuma amma bawani abu bane yajawo haka illa mutuwar son dakake mata kawai"cewar bash din,"hmm kaidai bari kawai, kasan ni akwai kishine wallahi yanzu ma daga cen muke nakai mata yara"yakarasa,"aa kaga maigida yallabai Alhaji mai mata biyu"bashi yadinga tsokanarshi suna dariya.
"Allah ya tabbatar da alkhairi dai"shine kawai abinda zan iya cewa,sannan suka karasa ciki don yasamu su gaisa da Amina yakuma ga takwaran daaka mishi.Lamuran dai sunyiwa kowa dadi,don Yusuf yakara tabbatar da wannan amincin nasu,dubada yayi da duk abinda aminin nashi yayi yayi ne don farincikinshi,dakuma dan shi dayaci sunanshi hakika hakan ba karamin dadi yamishi ba tabbas babu makawa bash naji dashi kuma masoyine na har abada.
Basu suka baro gidan ba sai bayan Maghriba saboda hira daaka tsaya yi na an dade baa hadu ba.
