RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA25
Duka kudadenta dawasu kadarorinta data dade tana tarawa,ta yanke shawarar gina makarantar islamiyya dasu,babbar makaranta fa sosai,mai bangarori iri iri,na yara,matasa dakuma matan aure.
Kodata gabatarwa da iyayenta shawarar basuyi wata wata ba suka goya mata baya,dari bisa dari sukayi naam,don abune mai kyau tabbas, ba bata lokaci kuwa suka shige mata gaba aiki yafara gudana.
To ta zauna tayi tunanin duniyar nan tayi harta gaji taga fa cewar bazata kara iya aure ba,aikin ma bazata iya ba bare wata sanaa,tunda dai tana gaban iyayenta Babu abinda tanema ta rasa,ga uban kudade data tara to meye amfaninsu?mezatayi dasu? Gashi ita duk wasu kyale kyale na duniya ma ba birgeta suke ba yanzu,bare tace zatayita siyayya,itafa mutuwar nan fa babu wanda yasan lokacin dazatazo, ko yau tafadi tamutu shikenann fa,tata ta kare,wannan ire iren tunaninnikan ne sukasa ta yanke wannan shawarar,na gina makarantar da zaa dinga karatun addini kyauta,dakuma tallafawa marayu,yin hakan tasan ko bakomai idan ta mutu Allah zai dinga bata lada.
Hakika aiki yayi nisa matuka kuma ita dakanta take zuwa a kullum don ganin irin cigaban daake samu dukda dai akwai wasu maza cikin yanuwa data wakilta,amma kunsan hausawa nacewa zuwa dakai yafi dan sako,shiyasa take zuwa dakan nata don tabbatarda cewar fa komai yana tafiya yadda akeso,batareda wata matsala ba,tunda Alhamdulillah tana iya fita ita kadai yanzu.
Dayake a kusada wani supermarket ake ginin,tana fitowa sukayi kicibis da Bash yazo siyayya,mamakin ganin juna sukayi sannan suka tsaya gaisawa,"aka dinga cewa ta rame ta chanja kamanni baa ganeta,amma gata kuma naganta tayi kyau tayi bulbul"yace aranshi yanata kallonta,kamar yaga wata sabuwar halitta ta daban, babu abinda yafi birgeshi da ita kuma kamar yadda ta nutsu ga shiga ta kamala kamar ba faridan daya sani ba,sallama sukayi don sauri ma take,hakan ne yasashi tambayarta ko metake a wajen ginin,tace mishi cewar ai nata ne,tabbas yadda take magana ma salon ya chanja,kai agaskiya ta mugun chanjawa,yacigaba da zancen zuci yana sake sake.
Koda ya karasa gida Amina yabawa labarin duk abinda yafaru,"faridan?"tace tace cikin tsananin mamaki ,"wallahi fa ina gaya miki tasha hijabi har kasa,a nutse kamar ba ita ba duk babu wannan tsiwar,ina gayamiki abindai sai wanda yagani kawai,har cewa tayi in gaisheki dakyau"Tab lallai,amma ya akayi haka kuwa?kodai wancen auren ne yasa ta nutsu haka?"ta kara,"Allahu aalam,kodai auren ne ya nutsar da ita ko kuma itace tayiwa kanta fada oho"lallai to Allah yasa dagaske ne har zuciya,tunda Kace har ginin makaranta take"eh wallahi Katafariya ma kuwa"ya kara "kaga yanzu lamarin nata ne babu tabbas bamu sani ba wannan nutsuwar da shiriyar ko na zuciya daya ne wallahi danayi mata shaawar komawa gidan yusuf don babu inda yadace da ita kamar cen,koba komai itama taje tayi rayuwa da danta"Tab,ai banajin yusuf zai amince fa,nima nayi wanann tunanin amma kuma inaaa,nasan halin kayana bai iya fushi ba,tabbas wannan abune mai kamar wuya kinfasan yadda abubuwan nan suka faru kowa baiji da dadi ba,akayi rabuwar kaca kaca,kuma nima dai dama tun dazu nake tunanin mai magana inji yaya,kinsan lamari irin wannan bazaka tursasa mutum akai ba,shi yafi sanin ta, dakuma abinda yafi dacewa dashi,tunda dai kinga zamansu lafiya sukeyi shida zainab din"Hakane kam Allah dai yazaba abinda yafi alkhairi"Amin yace.
A ranar yadinga kokarin kiranshi baya samu,hakan nema yasa yabar mishi message a watsapp akan cewar yanaso suyi magana idan yasamu dama,koda ya tashi kuwa yagani babu bata lokaci yafara kiran bash din bayan sun gaisa ne yake bashi labarin haduwar tasu shida faridan,"ginin makaranta fa kace"ya katse bash din cikeda mamaki,sanin cewar fa sanda suna tare babu yadda baiyi da ita ba akan ko da wheelchair ce tadaukan marasa lafiya a asibiti ko stretcher tasiya tabayar sadaqatul jariya,da duk wani aikin samun lada idan yabata shawara,tunda shima yanayi,kuma yasan tanada kudin dazatayi amma kememe,sai tace ita kudinta tanada abubuwan dazatayi dasu masu muhimmmanci,(na siyan wayoyi da kayan kwalliya,da kaya,shine aikin kullum),hmmm to dole kanshi ya daure ance mai tana gina katafariyar makaranta ai,"wallahi ina gaya maka da hijabi fa har kasa kai wannan fa wata faridace ta daban wallahi mamakin danaji ajiyan nan bazai misaltu ba"yacigaba,"To ai hakan yanada kyau Allah yasa adore"kawai yace sannan yabawa bash din labarin duk abubuwan dasuka faru na zuwan datayi wajen Hajiya bada hakuri da karbar numbarshi datayi shima ta dinga kira yaki dauka ta tuttura mushi da sako harda cewa wai yabata numbar abu,"haba kaikuwa,baka kyauta ba gaskiya meyasa zakamata haka,ina laifi ma data gane tayi badaidai ba hartazo ta nemi gafararka a matsayinta na mace,haba mutumina kafa dauki lamarin nan da mugun zafi"wane zancen daukan zafi kuma bash, ai abinda yariga yafaru yafaru kuma,duk waye ya jawo?"Nasani abubuwa basuyi dadi ba amma d...."amma me?wai tsaya ma tukun meyasa ma kakemin wannnan zancen ne?wai ni meye ne hadinku ne da yarinyar nan dazakubi ku addabeni kusani agaba da lamuranta,itama zainab tayi tagama,"bangane ba"cewar bash din cikeda rashin fahimta,"atoh haka fa zainab tazo tasakani agaba wai ita mai tausayi kasan halinta, wai dole tana bani shawara nadawo da ita,nikuwa abune daba zai taba yiwuwa ba awajena ainama fada mata"yace,"to nima dai abinda zance dama kenan ai kafin ka tari numfashina"me din?"yakatse bash din cikedamamaki,"na ka dawo da itan mana"hmm koba dawowa ba,ni wallahi har mamaki ma kuke bani,wai tayaya zaayi kawai don mutum yazo yanuna muku wani dan chanji attare dashi dabaku sani ba ma ko na gaskiya ne ko kuwa akasin haka shikenan kawai sai kudinga zaton k......"wallahi bahaka bane yusuf,"bash ya katseshi,"so nake kazauna kayi tunani kadubi abinnan da idon Basira,Dani dakai fa duk munsan kanason farida bakuma zaka taba daina s...."ada kenan"yayi saurin katseshi,"saika fadawa wanda baisani ba ai,mtsw,nasan kanasonta fa har yau bakuma zaka daina ba,nakuma san tamaka laifin dakake ganin ko ka yafe mata bazaka sake iya zaman aure da ita ba ko?"kwarai ma kuwa halinda ake ciki kenan yanzu,shine abinda kuka kasa ganewa nifa na yafe mata wallahi kawai zamane da ita na aure bazan iya ba"yace,"to naji,mai daki dai shi yasan inda yake mishi yoyo hakika duk abinda zaka fada babu wanda zai wani gane saboda kuwa kai kafi kowa sanin halin kayarka,so nake kadinga tunawa dai kun haihu tare kuma wannan yaron itama fa tanada hakki akanshi yazama dolene danta yasan da ita fa ko ba dade ko bajima,ko kuwa kafison kadinga daukanshi lokaci zuwa lokaci kana kaimata shi yana kwanaki kana daukoshi,b....."Ayi hakan Bash ni banida damuwa nasan babu yadda zaayi in rabata da danta,ayi nesa nesan dai yafi wallahi,"dariya bash din ya kyalkyale da ita cikeda tausayin abokin nashi,ganin dai duk ta inda ya bullo mishi saiya kauce,amma ba laifinshi bane dole amishi uzuri,shi kanshi (bash)sheda ne ai,wajen sanin irin wahalar da faridan tabawa aminin nashi,Allah sarki komai lokacine.
"To shikenan tunda haka kace nidai bazan maka dole ba tunda kai kafi saninta,ba abinda zance saidai Allah yazaba abinda yafi alkhairi,zan kuma cigaba da bincikawa wajen ganin an tabbatar da chanjin nata"ato gwara dai ka bincika tunda ka damu,don nasan wannan dai ba taba chanjawa zatayi ba atoh dai,kawai dai conincidence ne,ka hadu da ita tasa hijabi kuma yan masifar basa kanta shine kawai"ya kara,"to koma dai meye zan tabbatar nan bada dadewa ba ai"sai kayita tabbatarwa ai"yace tareda kashe wayarshi yacigaba da mita.
Yarinya sai kace wadda ta asirce mutane,wai duk kowa ya manta da irin bakaken halayenta,kamar ta shafe musu tunani,sai wani sonta ake ana riritata ana nan nan da ita,shiyama taba ganin abu irin haka?haka fa Rannan Hajiya tadinga mishi zancen nustuwar nan tata dasaka hijabi,wai tayi hakali,to saitayitayi ai don kuwa saidai tasamu yardar wasu badai tashi ba,saboda kuwa yasanta sarai,yaudararta daduk wasu salo salo irin nata basu isa suyi tasiri akanshi ba shi kam ayanzu,atoh dai.
