RUWAN DAFA KAI 2

2.1K 158 6
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

18

Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa kuma mai komai,Su farida an dawo gida Najeriya,hakika ta wartsake kwarai sai dan abinda baa rasa ba,tanata dai shan magungunnata,tabbas shigowarsu gidan nasu  keda wuya ta fashe dawani matsanancin  kuka mai cikeda dalilai masu tarin yawa,dubada irin gatan data taso ciki amma aka dauketa aka kaita daji inda ko abinci bata samu aka wulakanta mata rayuwa.

Irin Wayannan koke koken nata,zuwa yanzu dai,bawasu sababbin lamura bane a wajen yangidan nasu,saidai kawai  idan tanayi  adinga bata baki ana rarrashinta,masu aikin gidan mata ne,suka dinga bullowa don murnar ganinta,agaskiya kamanninta sun chanja kwarai da gaske,amma dai akan yadda ake fada,ai ta farfado takuma yi kyau,mutanen da da basu isheta kallo bama bare  magana,wai yau itace harda rungumesu,tab suma abin mamaki yadinga basu,tabbas halayyarta gabaki daya ta chanja to kodai watace aka musanyo?shine abinda yadinga daure musu kai,amma inaa babu wani musanya ita dince dai kurenta kawai tagane ta kuma nutsu.
Sabuwar waya Abba ya dauko yabata,da layinta daakayi swapping aciki.

Iso suka mata har kofar daki,don mama tace yakamata taje tadan watsa ruwa ta kwanta,ta huta,shigarta keda wuya kuwa  ta turo kofar tareda saka key,tazube a kasa,tafara rusa kuka,wai donma kar ashigo ace zaa bata hakuri,kwanciya tayi a kasan dakin tafara  karewa dakin kallo,ga komai nan a tsare a gyare, ga makeken gadonta mai matukar kyau,ita data saba da irin wannan gatan aka kaita daji tana kwana a tantagaryar kasa,acikin bukka,saida dai tayi kukan mai isarta ta gode Allah sannan ta tashi tashiga watsa ruwan.

Ahankali dai damuwar nata raguwa amma fa har yanzu bata bar firgitar nan ba cikin dare,saboda hakane ma tadaina kwana adakin nata don har tsoro takeji,saidai ta tafi wajen safina su kwana tare.
Gashi yanzu har aikin gida wai  take,yau itace da gyaran gado  idan ta tashi ta gyara daki,tayi shara hardasu wanke wanke,da girki,hmmm duk dai abubuwan da da bayinsu take ba saboda gata daya mata yawa yanzu yi take saboda tsananin kwarewa,tun abin na basu mamaki yangidan har sun fara sabawa,kuma kullum cikin Hijabi take ko Abaya,hmmmm yanayi kenan ,bazadai muyiwa wasu fatan shiga kangi da wahalar rayuwa ba irin wanda tashiga,amma irinsu farida shi kadai ne yadace dasu don ko bakomai hakan shi  yayi sanadiyyar saituwarta.

Haka dai rayuwa tacigaba da gudana masu aikin gidan har gulma ake ana cewa kamar ba ita ba duk tabi ta chaja yanzu tazama mai kirki,tunda wani lokacin idan suna hira har sa baki take,ko kuma idan suna wani aikin ta tayasu,hmmm.

"Samira Wannan abokiyar Aikin taki kuwa tazazzo kusan sau nawa ma,yakamata kije mata kuwa "cewar mama  suna zaune duka ana dan taba hira,tunda yanzu taji sauki sosai har tana iya fita ma amma ba ita kadai  ba da driver,"Allah  sarki samira,Kawa tagari zanje mata kuwa inshallah".
A hirar dasukeyi ne ma maman take fada mata Hajiyar yusuf ma tazo,kuma tayiyyi waya ma,Allah sarki mutanen arziki kenan,"cewar mama,"Allah sarki ta kyauta ai angode kwarai da gaske,"itama yakamata kije ki gaidata kuwa don ko bakomai dai ta nuna tadamu dake"hakane zanje inshaallah,"kawai tace,don kozataje dinma ba yanzu ba gaskiya sai an dan kwana biyu idan akwai  wayanda take kunyar gani duk duniya to fa Yusuf ne da Hajiyarshi,zancen zuwa ganin Amin tayi,mama take fada mata ai bama sa kasar,tabbas jikinta yayi sanyi Amma ya ta iya.

Aduk sanda ta tuno da irin yadda ta wulakanta dancikinta data haifa wani bakin ciki da takaici ne suke turniketa,ta dauki ragamarshi gabaki daya ta dankawa maiaiki,taki kula dashi dakanta,bayan sarai bawai sonshi bane batayi iskanci ne kawai da samun wuri yasa,gashi kuma taje cen inda tadingayiwa na wasu bautar daba lada zata samu ba,hmm.

Washegari kuwa ta shirya taje gidan Samiran,inda suka sha farinciki suka sha murnar ganin kuna,"wannan mutumi bazai taba ganin daidai ba arayuwarshi,Wallahi sai Allah ya saka miki jibi yadda duk kika bi kika zama,ni Samira"tace cikeda damuwa,"hmm kedai ayi shiru kawai"cewar faridan,"hmm karki damu ai naji labarin komai,Allah ya kiyaye gaba,mu da duk mun tsorata ma mun zata kin margaya"tace cikin wasa tana dariya,"Allah sarki nima nazata mutuwar zanyi ai To ashe dai lokacina baiyi ba"duk tanayin maganar ne  cikeda  nutsuwa babu wannan tsiwar,itama sammyn duk sai ganinta take wata iri kamar wata faridan ce ta daban aka chanjo,ga hijabi datasha har kasa,"to kinga  dai halinda na tudunduma kaina dakaina aciki,babu irin nasihar dabakimin  ba akan zamana da yusuf, amma inaa saboda dadi yamin yawa gata yana bina na zabi na jefa kaina cikin kunci"tace hawaye wani nabin wani,"ki daina kuka farida ki godewa Allah dabai dauki ranki ba acen ya tseratar dake,ance  mutane nan bama musulmai bane to inda kin mutu acen me kike tunanin zai faru waye zai miki wanka ya binneki akan tsari irin na musulumci? Allah ne yake sonki kawai ya kubutar dake,","hakane Allah ne yakesona  tabbas amma fa naga rayuwa samira"kuka yaci karfinta,"kidaina kukan nan haka don Allah"cewar sammyn bayan ta rungumota tana rarrashi itama hawayen wani nabin wani,,"bazaki gane bane""kiyi hakuri komai ai ya wuce Allah ya kiyaye gaba shine kawai,"sammyn ta kara,dakyar dai aka samu ta tsaida hawayen,"Yusuf bawan Allahn nan na cutar dashi,wallahi ga dana samira shi kanshi ban raga mishi ba,yanzu idan yaron nan ya girma yaji irin abinda na aikata mishi kina ganin zai taba yafemin?"tayi narai narai da ido,"ki daina magana irin haka,kowa fa dakika gani yana aikata laifi saidai kawai nawani yafi nawani,zasu yafe miki dukkaninsu ni na gaya miki,"Anya kuwa,Anya""zasu yafe miki mana ki yarda dani,ke da Allah ya taimakeki yabarki da ranki kinada damar ma neman gafarar,kurenki fa kika gane kika gano kinyi ba daidai ba,har kike neman ki gyara komai,haba zasu yafe miki ma kidaina damuwa kinji"to Allah yasa,amma fa na azabtar da bawan Allahn (yusuf)nan,baimin komai ba fa haka kawai saboda nayi sanadin ya kara aure nadinga hauka,kai! Ya Allah ka yafemin,bai taba min ko mugun kallo ba bare akaiga bakar mana,ko zagi,amma naje nadinga mai sharri a wajen mahaifina nace har dukana yake,"tafara hawaye,"to ai duk wannan da ne farida komai ya wuce,idan abu ya wuce ya wuce,saidai a duba gaba kuma,yanzu dai abinda zaayi shine ko numbarshi ce kisamu tacen din tunda kince baya kasar ko?saiki kirashi a waya kuyi magana ni ina ganin hakan zaifi komai sauki"cewar sammy,"hakane kam,Allah yasa dai ya saurareni"ta matairaice,dan murmushi sammy tayi,"karki wani tada hankalinki,komai zaizo yazama tarihi inshallah,kuma itama  Hajiyar tashi  ai yakamata kije ki gaidata ki kuma bata hakuri tunda  itama ai kin mata badaidai ba"haka ma amma tace, zanje amma wallahi kunya nakeji "yar dariya sammy tayi "da kunya don kunya amma dai zaifi kyau kicere ita kunyar kije kiyi abinda yakamata kinji,"toh zanyi inshaallah"tace kawai.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now