RUWAN DAFA KAI 2

1.5K 120 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

29

"Hmmm wallahi nayi hakanne kawai dubada irin magiyar daka dinga  min Bashir kana kuma hadani da Allah amma ai nariga nagaya maka ansata gameda wanann zancen,h...."don Allah kidaina magana irin haka,sanin kanki ne yusuf kamar danuwa yake a wajena,kuma wallahi damuwarshi damuwata ce,h....."cemaka yayi ya damu danii?idan dagaske ya damu dani din ai shi yakamata yadinga wayannan kalaman bakai ba bashir,bafa aikoka yakeyi ba nasani kaine dai kawai kake zuwa kana tsarani,"saikuma tayi yar dariya,"Ba tsaraki nake ba farida,so nake dai kawai naga kin janye bakanki nacewar wai ke bazaki kara zaman aure ba aduniya abun ko dadin ji babu wallahi,ai ba duka aka taru aka zama daya ba sanin kanki ne,kuma azaman dakukayi (da yusuf din)abaya,ai kunyishi ne babu wata matsala babu tashin hankali ko ba haka ba?karki manta fa saida yai zancen kara aurene  abubuwa duk suka lalace,wanda nasan inda yanzu ne kema bazaki aikata abinda kika aikata  ba,ko ba haka ba?"shiru tamishi tareda fara nazarin rayuwarsu ta baya,hakika yusuf yasota yakuma so suyi zaman lafiya itace dai tadinga hauka,takuma jawo komai,"to kinga don Allah don Annabi,idan yadawo gareki ki karbeshi hannu bibbiyu,ku dora rayuwarku daga inda kuka tsaya,idan kuma shi dinne bakya muradi yanzu ni ban isa na tursasa ki ba,amma sakamakon irin zaman mutumci daakayi da,don Allah ina baki shawara idan wani mijin yafito miki na kwarai farida don Allah kiyi aure zaman na naki a......"Naji,nakuma gode Bashir,zanyi tunani akan hakan kagaida Amina"ta katseshi,"to shikenan Allah yasadamu da alkhairi"ya kashe wayar.

Zama tayi tanata tunane tunane,wai meyasa ne kowa saiya dinga bata shawarar wai tayi aure tadaina zancen itada aure har abada,mutumcin ya mace gidan miji,kaza kaza,to itakuma saitake ganin don me akeyin auren ne wai?ba don soyayya bane dakuma neman kariya daga afkawa sharrin zina?wasu kuma don su hayayyafa?to agskiya indai don wayannan wayannan yan dalilan ne zaa dinga matsa mata da zancen aure,ta yafe,don gani take ita kam tsab zata iya hakura da aure indai donsu ne tacigaba da zamanta agida,Tashi tayi ta tafi alwala don an kira sallah,

"Hmmm wato Bash haka yake ashe,nawani yarda dashi,na dauki duka amana da gaskiyar duniyar nan na danka mishi,hmmm dan Adam babu na yarda,tun jiya yake kiranshi(shi yusuf din)baya dauka,yakira hajiya itama amma fa tana nan kan bakanta tace bazaayi shashanci da ita ba,to tunda abin yazama haka yazama dolene su tattara su tafi Najeriyar ayita takare kawai kowa ya huta,tunda dama hutu suke ai(shida Abun).

Karar shigowar message a whatsapp ita tasashi daukan wayar don dubawa,kodaya  duba bash yagani,"daniska,dan neman magana,wato sai yau kaga damar kulani"yace afili,yana mita,da har bazai bude ba saidai yabude,ai a zabure yafara kallon abinda Bash din ya turo din tareda zaro idanuwa,gashinan kati ne na daurin aurenmu,aka rubuto,akasan hoton katin,aikuwa dai katin ne,tunda ga sunanshi gana Farida,kuma wai gobe a misalin karfe goma na safe,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun"yace afili,a halin daake ciki,ranshi yakai kololuwa wajen baci,tabbas wannan abu ya rabasu shida bash,ba makawa,bazai iya cigaba da aminta da mayaudari ba maci amana,mara mutumci,bayajin ma zai sake iya kulashi ma arayuwa ya rasa wanda zaici amana sai shi,hmmm,yama rasa meke mishi dadi hakan ne yasashi dafe  kanshi,cikeda takaici,da haushi,gashi wai  gobene ma,shi dayayi zaton da dan sauran lokaci idan ma zuwan zaiyi har ya je,to ashe shammatarshi sukayi,tunda yanzu har yaushe yayi shirye shiryen dazaiyi yatafi, ai duk saurinshi  daai kafin yaje an daura to me akayi kenan,yayi tafiyar banza?hmmm,"ka dauki abinnan dazafi fa tun farko kaima sanin kanka ne bash mutum ne mai saukin kai dabashi da matsala ko kadan,amma daga fada maka zancen nan mai makon ka lallabashi aa saika dinga zakewa kana fada,"wata zuciyar tace,kasa jurewa  yayi ya dauki wayar tashi yafara lalaubar numbar  bash din,ai yana ganin kiran,yasan kwanan zancen yadinga dariya kuwa, don yanama  office lokacin,saida yabarshi yakira kusan sai nawa sannan yadauka,"sai yau kaga damar daukan wayata  kenan?"yace cikin wata irin  murya cikeda tsantsar  damuwa,"to meye na fadan?tayaya zaayi in iya daukan  waya ina nan abubuwa sunshamin kai,auren wasa ne?kafini sani ai kuma waye zai taimakamin baka nan?nace waye zai tallafamin,nikadai nake komai fa,raina ni kadai"ya katseshi lallai wannan yama raina mai hankali, wato zai aure tsohuwar matarshi sanann yake tunanin inda yanannan ma shi zai shige mishi gaba ma wato hmmm,amma dai bari  ya hadiye  bakincikinshi ko Allah zaisa yaji tausayinshi ya fasa,"Bash,duk ba wannan ba kayi hakuri,kiranka nayi muyi magana ta tsakani da Allah,Don allah Don annabi,bash kar ka auri yarinyar nan,kai ko wani irin ma wai bakaji?ni bansan  sanda kazama haka ba wallahi g....."eh lallai,bama kirana kayi kamin fatan Alkhairi ba wato?,ko kaji a ina zan ajiyeta da sauran shirye shiryen biki danake, bayan kuwa kaga katin sarai,aa kirana kayi kacimin mutumci,ana igobe zan angwance,wanann wane irin abu ne,to bari  kaji ni daga yau ma kashe wayoyina zanyi har sai baba tagani,don mata biyu ba wasa ba,sai anjima"hel...hello.."yaji wayar ta tsinke,"hmmm babu abinda ya dace yayi a wannan gabar kamar rungumar kaddara kawai,don tariga ta faru  ta kare,shikenan ya rabu dasu suje suyi auren,rayuwa ce dai ai.
Dakyar Abu tasamu ya labarta mata komai,sakamaakon ganinshi datayi cikin damuwa,hakika bataso hakan ba itama,zancen bai mata dadi ba,to Amma yazatayi,dole ta rungumi kaddara.

Haka dai rayuwa  tacigaba da gudana,Yariga yagama saddaqarwa,Ko tada zancen ma baisake yi ba,yana nan yagama karatunshi tun tuni Abu kuma baifi sauran  watanni hudu suka rage mata ba,kuma tana gamawa zasu tattaro su dawo gida najeriya,don tunda suka tafi ko leke,rayuwar dai tana musu dadi kwarai da gaske,abin sai wanda yagani yara duk sun girma mashaallah.

Farida kuwa tana nan,bayan ginin makaranta data gama,irin yan kauyuka kauyukan nan masu fama da wahalar ruwa tasa duk ana musu burtsatee,don ahalin daake ciki ma dukkanin kudaden data tara sun shige sadaqatul jariya mahaifinta ne dai yake tallafa mata tana gudanar dakomai,tunda dama ko kafin tafara aiki duk wata akwai abinda yake bata.

Bash kuwa suna  nan suma suna rayuwarsu mai dadi shida matarshi amina Allah ya azuratasu,da dan kyakkyawan yaro,Wanada ci sunan  Yusuf,saboda amincin dake tsakaninsu.

Abin mamaki,tun ranar dasukayi magana dashi ya tura mishi kati shikenan  idan yakira yadaina samunshi, ko a wahatsapp dinma,nan kuwa baisani ba blocking dinshi  yayi donma kar yadinga shaqar bakinciki.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now