RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA26
Wajen sau nawa Bash namishi zancen dawo da itan,amma inaa,yayi kunnen uwar shegu,tun yana fada har yadawo nasiha amma a banza kamar ma kara zugashi yake,hasalima daga ya kirashi yaji ya dauko zancen sai yayi kwana,ko kuma idan ma yaga kiran abokin nashi yaki dauka,hakane yasa Bash din kyaleshi nawani dan lokaci, yanata tunanin ta yadda zai bullowa alamarin,don yariga ya gama fuskantar cewar fa yusuf din bawai son faridan bane bayayi kawai dai hankalinshi ne yakasa kwanciya dahakandon bawai bayason yanaidatan bane, aa sai don tsoron abinda zai biyo baya kawai,shikuwa Bash amini ne na kwarai yakuma damu da yusuf din shiyasa bazai hakura ba har sai yaga abinda ya turewa buzu nadi.
"Wallahi ina gayamiki fa yana nan akan bakanshi,ni wannan taurin kan nashi har mamaki yake bani,bansan sanda yazama haka ba,tabbas duk yadda muke zaton abin yafi ga haka"Bash yake cewa Amina bayan ta tambayeshi yaya ake ciki,"hmmm,har yanzu dai?,To Allah yazaba abinda yafi allhairi dai kawai" tace,"Amin dai kinji, ni wallahi ma duk na gaji, inaga ma kawai dai gwara nahakura haka nadaina mishi zancen tunda har yanzu babu abinda ya chanja yana nan kan bakanshi saima abinda yayi gaba,"yace,yar dariya Aminan tayi kawai "duk abinshi dai zaiyi ne yagama nawani dan lokaci ai, don idan Allah ya rubuta sai sun sake zama tofa babu abinda zai hana hakan,"hakane fa kuma"ya kara,"to kaga,amma inada wata yar shawara, bansan dai kai yazaka dauki abinba shine"tace tana dariya,"wannan shawarar taki kuwa anya?anya kuwa? naga fa kina wannan dariyar taki"yace cikin tsokana,"hmm,to shikenan bari na rike kayata tunda kafara kushewa"tacigaba da yar dariyar,"a haba,kekuma ai wasa nake miki kema kinsani,fadamin mana idan tayi ai zance tayi tunda shawara ce ai ko?"yace cikin wasa,"to tunda kace haka"sannan ta gyara zama,"kasan dai kowane dan Adam ai yana kishin abinda yakeso ko?to mezai hana kace mishi tunda shi yakita yanata jan aji,kai zaka aureta muji mai zaice,"Nikuma?yayi saurin katseta cikeda mamaki,"aa wani dai ko?"yakara"aa kai din dai,ai abu mukeso mugano ko?kuma mucimma wani buri,to indai yanuna maka kishinshi karara tofa yana sonta har yanzu yana kuma kishinta, kaiwa kasuwa dai kawai yake yana nuna rashin damuwa,idan kuwa yanuna halin ko in kula to fa dole mu hakura,nace kace kai saboda abin zaifi bashi tsoro;"eh kuma fa hakane,dadina dake basira,shiyasa nake kara sonki wallahi,nasani sarai mutumin akwai kishi indai akan iyalinshi ne kuwa,bare kuma ma yana ganin nine nace zan auretan bawai wani ba cen na daban"yayi yar dariya,"aikuwa dai,saidai kuma wani hanzari bagudu ba idan kuma wai duk mu kadai muke dramar mufa itama bason komawar take ba kamar yadda shima bai damu ba fa?"eh to da wannan don wannan,kuma,don ni dana ganta ma wallahi, banga wani damuwa ba ko kadan atattare da ita kinsan dama yawanci lamura irin wannan sunfi shafar wayanda basuda gata,don inda ace tana cikin kuncin rayuwa ne ko cikin bakin ciki da talauci,a gidan iyayenta dashine zakiga tanata neman arufa mata asiri,duk kuma yadda zatayi taga ya maidata zatayi harma inta kama da kanta tadinga bibiyarshi, amma kinga dayake akasanin haka ne tayi zaman ta hankali kwance shiru kikeji"yace,"hakane kam abubuwan dai sai ahankali kawai,Allah dai yakara rufa mana asiri yasa mudace"Amin sukace baki daya.
Ai Bash bai jira dare yayi ba,yakira mutumin nashi yasa shi a handsfree,don Aminan tace tanason jin yadda komai zai kaya,bayan sun gaisa yafara,"Nasan kwana biyu ina damunka da zantukan farida wayanda suke sosa maka rai ko?to ina rokonka dakayi wa Allah kamin afuwa kayi hakuri"eh mana,kaima ai kasan nace bana kaunar amin maganarta koda wasa kuwa amma kadingayi"ya ce daga daya bangaren,"au ashe shiyasa kadaina daukan wayata ma kenan kwana biyu ko?"cewar Bash,"eh to,harda hakan ma dai,dakuma network dinku ma dabashi dakyau"yakara,"to Allah yabaka hakuri,bansan abin yakai har nan ba,ni don na damu dakai ne shiyasa nake abinda nake,amma dai duk bama wannan ba yanzu dai, sai kasa ranka a inuwa don inshaallah komai yazo karshe,sakamakon bincikenda nace maka zanyi akanta(faridan)don ganin cewar ko dagaske ne komai dangane da ita na chanjawarta,to alhandulillah nagama nakuma tabbatar dagaske dinne g....."Bash!"ya katseshi cikin bacin rai"wai meyasa ne kake min haka?nace maka bana kaunar zancen yarinyar nan n...."aa,maida wukar malan"shima ya katseshi,"ai nagama dakai kuma,tun wani lokaci mai tsaho,badai zancen ta bane dai bakaso ko?to dama nakirane in gaya maka don karkaji agari kace banfada maka ba,ni bazan iya jurar ganin mutum ya chanja ba zuwa halayen kirki inyi biris,bakuma zan juri ganin ana wulakanta mace mai kima da daraja irin farida ba,shiyasama na yanke shawarar aurenta n......"wat?yakatseshi, kunajin muryarshi zaku fuskanci tsantsar tashin hankalin dayake ciki,"menene kuma?ni nazata addua kawai zaka mana kamana fatan alkhairi tunda dai baka kaunar ta ka tsaneta meye kuma na tada hankali haka?"Cewar Bash bayan sun gintse dariyarsu,"ba bata rai nayi ba,amma wai dagaske kake don Allah ko wasa?"yace don bayason ya yarda da wannan lamari mai cikeda abin mamaki,yasan yace ya rabu da ita,yakuma gama zaman aure da ita amma yazaayi kuma wani na kusa dashi yace zai aureta wanin ma kuma bash haba?tsohuwar matarshi ce fa"dagaske nake man,ko haram ne?nace haram ne?kuma ma ana wasa da maganar aurene?badai kace kai bakaso ba to,meye naka aciki,idan baka so ai masuso dayawa irinmu"ya kiftawa Amina ido,"amma dai don Allah tayaya zaayi ka auri tsohuwar matata bash meye haka h..."shine nace ai wai haramne yin hakan?Kayi shiru?ko dayake dama bawai kiranka nayi don neman shawara ba,ko wani jawabi ba na neman amincewarko,ko wani go ahead aa,nafada makane saboda bazakaji dadi ba idan kaji zancen agari ko ba haka ba?g...."hmmm Amma dai kasan baka kyauta min bako?"yasake cewa,"wai wannan wane irin zancene kakeyi haka kamar na aikata sabon Allah,nifa sunna kawai nakeson na raya shine kawai,kuma zancen gama yagama,munriga ma mungama aminta da juna,kaga ma sai anjima mtsw"ya kashe wayar batareda ya jira ansarshi ba,suka tuntsure da dariya,"Ashe dai da gaskiyarki kinji muryarshi kuwa duk ya rikice dan iska yanaso fa yake wani jan aji"yacigaba da dariya,"eh mana,ga alamu nan,ai shi so na gaskiya baya buya"tace,suna gani yanata kira Bash din yaki dauka,dayaga kiran bazai kare ba ya kashe wayar ma gabaki daya,"ai saina koya mai hankali,"yace,"karkuma yaje fa ya tambayeta ta bata mana shiri,tanuna batasan zance ba"Amina ta kara,"aikuwa dai,kodayake ai inada numbarta dama bari in duba ko har yanzu da ita take amfani,muyi magana"yace suka cigaba da dariya,don Wannan hanyar ita kadaice hanya dazasubi suyi maganinshi sukuma kawo karshen komai.
