RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA27
Zantuka yacigaba dayi afili cikeda tsananin mamakin aminin nashi,lallai Bash yaci amanarshi,hasalima bai taba tunanin koda amafarki ba zai taba aikata mishi haka,duba dayayi kuwa dasanin duk irin abubuwan dasuka faru,to inbama zakewa ba irin tashi meye nashi aciki?meye nashiga tsakaninsu sashi akayi?har yawani ce wai bazai iya jurar ganin ana wulakanta ta ba,anya kuwa dama ba ya dade ba dawani abin ba acikin ranshi?tayaya zaayi yace zai auri macen dashi(yusuf)din ya taba zaman aure da ita,kai?agaskiya ya dade baiji abinda ya rikitashi ba kamar wannan ko daa tarihine kuwa,jin yana zance shikadai ne yasa Abu data zo wucewa tsayawa tambayar ko lafiya,don ankusa minti nawa yana abu daya tun tana jiran taji shiru harta gaji,"mine lafiya dai kaketa magana kai kadai?"ta tambaya cikeda rashin fahimta don yadda yake zancen kamar shida wani sukeyi alhalin kuwa shi kadai ne,"hmm bakomai fa"kawai yace mata anma duk yabi yarasa sukuni ga tashin hankali nan a bayyane karara a tattare dashi,"bakomai kuma?haba mine tun dazu fa nakejinka kanata zance kai kadai"tasakecewa,"hmm kedai bari kawai"kamar dai kar ya fada mata dafari,saidai kuma kawai yaga dai gwara yafada din koya dan samu saukin abinda yake ji aranshi,ta jajanta mishi itama,saboda abin yamishi yawa shi kadai kam,"Duk yadda sukayi da bash din ya kwashe mata kaf bai rage komai ba baikuma kara ba"ikon Allah,Allah sarki,ashe dai dagaske take g...."tayi saurin shiru,don tayi zancen ne batareda ma tasan tafada ba,"dagaske take?ita wa din!"ya titsiyeta cikeda rashin fahimtar zancen nata,"uhm,bakomai"kawai tace zata juya tabar wajen,"ina zaki,baki bani ansa ba,nace ita wa din?kuma me akayi dakikace dagaske take kinsan da zancen ne dama?"ya watso mata tambayoyi,to yanzu ita tayaya zata bada ansoshin wayannan tambayoyin bayan batason yasan abinda ga aikata,ganin dai ya titsiyeta,yakuma dage akan sai yasan abinda take boyewa ne yasa tafara magana,don harga Allah ita maganar dasukayi da farida bata taba burin yasani ba saboda tasan yadda ranshi yake baci akan abin, kuma duk abinda zai bata mishi shi take gudu,ganin dai har yana neman hasala akai,ga kuma abubuwan dasuka mishi yawa dama,hakan yasata fara magana takuma fadamishi duk yadda sukayi kwanaki, ,"yaushe kika fara boyemin abu zainab?"yace cikin wata irin murya cikeda danuwa,"wallahi ba haka bane manufata,kawai dai nasan idan na fada maka ma tun farko bazaka bari ba,nikuma harga Allah inaso ayi sulhu tadawo shiyasa nayi hakan batareda saninka ba,kuma ni wallahi bansan Bashir zata aura ba,tace min dai kawai takusa aure,Amma don Allah don annabi ka yafemin"tace bayan tayi narai narai da idanu,"hmm,shikenan ya wuce"kawai yace.
Ai bash cikin saa yanemi numbarta,dama yanata Fatan Allah yasa baiyi deleting ba to ashe kuwa tananan,yana dubawa kuwa yaga tana watsapp da ita,babu bata lokaci kuwa yamata magana suka fara chatting aka dan gaggaisa,tanata mamakin dalilin dazaisa yamata magana,saida hirar tadanyi nisane yake fada mata duk yadda suka shirya abun dakuma mhimmiyar rawar dayakeso ta taka,"don Allah don Abbabi karkice aa"yadinga rokonta yana hadata da Allah,"Bashir,yin hakan bawai abu bane mai wahala awajena amma abinda nakeso ka gane shine zaman aure ni bama yusuf ba kowaye nagamayi dashi,banida saar aure"ta tura mishi,"don Allah don Annabi kiyi hakuri ki daina fadar haka ,wallahi yusuf yana mutuwar sonki, yanzu haka zancen nan danake miki dazu don bakiga yadda hankalinshi ya tashi bane matuka don harga Allah yadda namishi zancen ya zata dagaske nake,don Allah ki manta dakomai,ki karbeshi hannu bibbiyu don yana nan tafe zai dawo gareki ni nasan da haka "ya tura mata da irin wannan emoji din mai hannuwa ahade gudabbiyu alamun roko,(🤲🏽),hakuri tacigaba da bashi akan bazata iya komawa gidan yusuf bafa, koma wani namiji nadaban don,ita tasan zaman aure bai karbeta ba,gwara tacigaba da zama gaban iyayenta,ganin dai bazata yarda din bane yasa dole bash din ya hakura cikin sanyin jiki ya ajiye wayar.
"Amma tayaya zaayi ma wai tayarda ta aureshi bayan nafi kowa sanin irin tsanar data mishi?"yake zancen zuci,"kodayake ai ko don su kuntata maka sayi haka"hmmm yasaki ajiyar zuciya a fili,tareda jawo wayarshi,"shin in tambayeta ne ko in kyaleta?"yacigaba da sake sake,wai har shi zaa hada baki da Bash aci amana,tab,dan Adam,babu na yarda,(Nikuwa nace wai meye ne nashi na damuwa?kariga fa kace kagama da babinta to meye na damuwa da lamarin aurensu?).
Ai kasa jurewa yayi ya dauki waya yafara kiranta,don wannan ba zancen text bane ko chatting,tana sallah taji wayar na kara,saida ta idar tayi adduointa sannan ta janyo tagani,"yusuf"ta nanata afili,"mekuma yakeso,mezanmishi"tace afili,ita tama manta da zancen Bash,don ba abu bane ma dazata wani saka aranta,ajiye wayar tayi don fita zatayi dama,sai gashi kuwa yana sake kira,cikin nutsuwa,ta dauka tareda sallama,"Ai gabanshi ne yabada wani ras"tabbas farida ce,ga muryar nan tata mai kasheshi,kuma wai yau itace harda ansa waya da sallama ga wata nutsuwa dayaji cikin muryar tata,gaisawa sukayi cikeda girmana juna sannan yafara magana,"Ashe aure zakiyi?"ya jefo mata tambayar,da kamar karta kulashi dubada yadda taji yana wani magana cikin isa da takama,saidai kuma ta tuno da magiyar Bash,"Eh"kawai tace,"ok,gud,kuma ki rasa wanda zaki aura sai aminina Bash ko?,haba farida"yar dariya tayi kawai,don muryarshi karara take bayyana kishinshi akan lamarin,"Meyasa bazan aureshi ba don yana amininka?haram ne a musulumce?"tace,"ow haka ma zakice kenan,to ina mai baki shawara akan ki fasa wannan auren don nafiki sanin ko wayeshi,babu macen dazai tabaso sama da matarshi Amina,kawai dai ya......"Wai meyasa kake tada hankalinka akan hakan ne yusuf?"ta katseshi,"shikenan bazanyi aure ba,kai kakeso ka zabamin mijin kenan ko me?To nidai Bashir yanuna yanaso ya aureni,kuma nima hankalina ya kwanta dashi,mun aminta da juna,Don haka nan bada dadewa ba zamuyi aure,wannan shine abinda zan iya cemaka kawai,Ka huta lafiya"ta kashe wayar,saikuma ta tasinci kanta dayin murmushi,dakuma shiga wani farinciki na daban,hakika tayi rashinshi,ga muryarshi data dade bataji ba,tabbas babu namijin dazata tabaso arayuwarta banda shi,amma lokaci ya riga ya kure.
"Aaa,wato harda kashemin waya?eh lallai"yace afili,yacigaba da zancen zuci,yana mita afili, Abu kuwa na labe tana kallon duk abinda yake,Godewa Allah tafarayi don Babu makawa,burinta yakusa cika tunda gashi yafara bibiyar tata,kuma dasannu komai zai tabbata inshalalah.
Ita dama bata taba yaudarar kanta ba waj akan cewar yusuf yafi sonta akan farida tasan wallahi karya ne ko sau miliyan nawa zai fada kuwa,yana donta itama amma farida yafiso,halayenta ne dai suka sa abubuwan suka chanja.