RUWAN DAFA KAI 2

2K 158 3
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA
4

Tana nan zaune tana nazarin irin rayuwar data tsunduma kanta aciki,taji alamun bude kofar,a tsorace tafara ja da baya ta nanike da bango bayan ta fashe dawani sabon kukan,don batasan kuma wanann karon dame yazo ba,tunda koda yaushe yanada sabon salo,tsaki yaja ganin yadda taketa takura kanta jikin bango,don ko hada ido ma taki yarda suyi taki kallonshi,dube dube yafara kome yake dubawa oho saida yagama tsab sannan ya juya gareta,"ke!"ya daka mata tsawa,ahanakali tafara dago kai zata kalleshi,"ba dake nake magana ba?menace miki dazu?"Ya taso mata,"kayi hakuri Don Allah"tace cikin rawar murya,"idan kinga dama ki sauko ga abinci cen badaban halinki ba,don naga idan nabari kika mutu yanzu,yayi wuri kuma burina bai cika ba"ya juya ya fita,a hankali ta tashi tabi bayanshi da hijabin a jikinta,(da dane datuni tamanta da cireshi don bata kaunarshi,iyakarta dashi sallah,hasalima bata taba fita dashi ba,zamu iya cewa tun zamanin islamiyya,dukda dai shima karatun agida akazo aka musu,shima sai mama tayi dagaske,haka yusuf ma ya karaci fadan da nasihar har yagaji bazata fita da hijab ba wai sawa yake tazama yar lukuta,to yau dai gashi babu wanda yasata don kanta,takejin kwanciyar hankali da nutsuwa tafi samuwa da hijabin ajikinta).

Ko da ta sauko din,abincin tadinga leke tana nema amma bata gani ba,dama bata kalli table ba don bataci buri ba,a cen kan centre table taga wata bakar leda,dawani abu a kofi,sai busashen biredi.

"In...a..abinc...in?"tayi karfin halin tambaya,wani mugun kallo yajuyo yabita dashi,"uban meye wannan a ajiye?ke! bafa nason iskanci,ko donma kin samu?idan kinga dama kici idan kuma kinga dama kada Allah yasa kici duk uwarsu,ubansu daya a wajena,banza,dallah cen ni bani waje"ya hankadeta gefe,hawaye wani nabin wani,ta bude ledar taga wasu sandararrun kosai,guda uku yan kanana don bama suyi kalar na ranar ba,kamar na jiya,sai kofin kokone shima asandare,har kuda yafada ciki ya mutu,bredin kuwa ana tabashi yake murmushewa don abushe yake matuka,tabbas babu abinda zata iyaci anan wajen don ita arayuwarta ma batacin kosai,bare koko,da bredin sabone watakila tadan iya cishi,amma daga dukkanin alamu ahalain daake ciki watakila yunwar ce zata kasheta kawai ta huta.

Ganin tagama bude buden takoma gefe ta rakube ne yasashi tabe baki,"iye,ah lallai samun waje magani na nima ai,gobe ma ranace,wal...."kwankwasa kofar daakayi ya katse mishi zance,shidai yasan baya tsamamnin zuwan kowa,to ko dai yanuwan ta ne?yace aranshi tareda mata wani kallo,don har yanayinta ya chanja tafara dan farinciki don tana tabbacin tasamu ceto,"wallahi idan kikayi ihu,akajiki ko magana daina kasheki,kinjima nagayamiki",yace,gyada kai tayi alamaun to amma taci alwashin yana bude kofar tana kurma ihu koma taje ta shammaceshi ta fita,"mtsw banma yarda dake ba,yace tareda dawowa,wani dogon tsumma ya jawo zatayi ihu, ya nannade mata baki tamau,ya fizgo igiuar labule ya daure hannayenta da kafafu yadda babu yadda zaayi ma tayi kwakkwaran motsi,ba abinda take sai matsananancin kukan dababu sauti a hawaye kawai dakekwaranya,"nace waye ne anan?"yace cikeda masifa jin baa daina kwankwasa kofar ba,a fusace yakarasa yafara budewa,yana mita yana tsaki,ai yana bude kofar yafara zare zaren ido,zuciyarshi na bugun tara tara,take ya zube a kasa duba da mugun kallo da hararar da mai kwankwasa war yake aika mishi,"ranka ya dade yallabai,barka da zuwa as...."zaka rufemin baki ko kuwa,wallahi Audu kabani mamaki kakuma ci amanata,nayi dana sanin yarda danayi dakai wallahi,ban taba ganin wulakanci da rashin mutumci ba irin wannan,in baka ajiyar sabon gidana,in damka maka amana a hannunka amma abinda zaka saka min dashi kenan?menene banmaka ba arayuwarka ta duniya?,nace me na rageka dashi?"Ranka ya d" karkasake magana",ya daka mishi tsawa,"zakabani hanya nawuce ko kuwa"yace cikin fada ganin yadda duk yabi ya babake ko ina,"kayi hakuri ranka ya dade,iyalin nawace baa suturce ba shiyasa don girman Allah kayi hakuri,walahi yallabai sharrin...."inka sake magana walahi saina baka mamamki,nabaka awa uku kafin inje in dawo ku kwashe duk wani abu dakuka sani naku kasan inda dare yamaka,zai sake magana yallabai ya daga mishi hannu,"bazan sake maimaita kaina ba,mara mutumci,kaje ka kawomin mukullayen motocina gabaki daya,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun"ya dora hannaye biyu aka,"zaka bar surutun banza kayi abinda nasaka ko sainaci ubanka,yayi maganar kamar zai kai duka,simi simi yashiga ya kwasosu yazo ya tsugunna ya mika mishi,"Allah wadaran hali irin naka nacin amana da rashin gaskiya,ka aikata abu kamar a littafi ko film tayaya zaayi dama kataba cigaba?Ai indai cuta abin yine to walahi haka zaka dawwama,duniya ce dai gaka gata,duk cikin direbobin danakeyi ban taba yin irinka ba wanda na yarda dashi farat daya,kamar kai,ganin hakane yasa kayi amfani da wannan damar wajen min wulakanci ko,hmm wai nagina sabon gidan dazan tare da iyalina,dazarar na dawo daga tafiya,shikenan don na barmaka jira kamin butulci,wai don tsananin raini kayi aure ka kawo mace,cikin gidana,gidana?,hmmm wallahi kayiwa kanka,daga kai har sallau(megadi),daya biye maka kuka hada baki banason nakara ganinku,wai saboda tsabar butulci irin na yan Adam har kudi yace kana bashi na toshiyar baki daya maka barazanar sanar dani,kullum dubu daya ko?hmmm bazan iya zama da munafukai,azzalumai ba da nasan ni kaina bakyaleni kukayi ba tabbas wata rana zaa iya hada baki daku a kasheni,zai sake magana ya kaimai mai wani zazzafan mari,"awa uku nace nabayar babu ragi ba kari don idan natashi dawowa bazan dawo ni kadai ba wallahi,idan ka kuskura kabari nadawo na taddaku saina sa an daure ku yaniska,ya juya ya tafi a fusace.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now