RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA14
Kimanin awanni kusan shida kenan dasu Abba suka baro babban birnin kasar suka yo kauyen su Abdallah, amma tafiya taki karewa,yin ta ake,har yanzu baa karasa ba.
Wannan irin nisa kamar zasubar bar kasar ma gabaki daya?tabbas wannan kungurmin kauyene zasuje,tab."Muna hawa wancen titin shikenan munzo"cewar daya daga cikin yansandan,ajiyar zuciya sauran sukayiyyi don babu karya kowa ya galabaita anji jiki an gaji,donma dai an tsatsaya ahanya masu sallah sunyi,wayanda zasuci wani abun sun samu sunci,Amma banda Abba babu abinda yaci don hankalinshi baa kwance yake ba,yadaiyi yiyyi sallar.
Wani mai mota dasuka gani lokacin dasuke gab da shiga garin suka tsaida,dubada yadda yaketa shara gudu kamar zai tashi sama,kuma tun dazu suke tafiya kusan tare dashi.
Tambayoyi suka shiga mishi akan inda ya nufa don sunga kamar ma binsu yake,shikuwa ba binsu yake ba shima tafiyarshi ce tadaban,ganin dai bazasu sassauta mishi da tambayoyi bane yasashi fadamusun inda yanufa agarin,yace kuma Shine wanda yake kai Abdallahn birni duk sanda zaije yanzu haka ma tun wancen satin dasuka hadu yace ya tabbata yakaraso daidai wannan lokacin don su tafi duk yadda akayi ma yanzu yanacen yana jiranshi,yace,duk abubuwan daake zargin Abdalahn da aikatawa yansanda suka mishi bayani,kuma tunda yace kamar direbanshi yake duk shiga da fitarshi shi yake kawoshi yakuma maidashi bazai rasa masaniya ba kenan akan abinda suke nufi,tabbas yana tunawa watanni kusan shida dasuka wuce shiya daukosu daga tasha ya kawosu nan,shida wannan din(farida)daaka nuna mishi hotonta,yakuma ce mishi amaryarshi ce ya auro acen Najeria,"meyake cewa ne"Abba ya tambaya cikeda kaguwa don duk maganar sunayinta ne cikin yare,duk abinda yafada da yaren daya daga cikin yansandan nasu nacen maijin turanci ya fassara,"karyar banza,wace irin amaryace zaa aurota daga cen a kawota wannan dajin?"Abba yace cikin fada,inda sauran jamaun suka shiga bashi baki don ganin yadda ya hasala,ana cewa yayi hakuri abi komai ahankali,"yadaina bata mana lokaci yakaimu muyi abinda yakawomu daallah"yasake cewa,motar tashi shi direban suka shiga shi da yan sanda guda biyu,aka tasashi agaba akace kuma kar yayi birki a ko ina in ba gidan aka je ba.
Ai kuwa dai hakan akayi, basu tsaya ko ina dinba sai agidan.
Shikuma har angama shiri (Abdallahn)an fito yana karkasin bishiya yana jiran mai motar,har bacci ya daukeshi."Ko tsayuwar motocin ma baiji ba saboda baccin mutuwa irin nashi daya saba,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun wallahi shine wannan "cewar Abba yana mai nuna shi,tareda daukan wani katon ice ya nufeshi,"kayi hakuri Alhaji muyi aikinmu"wani dansanda yace tareda jawoshi,"ku kyaleni in hukuntashi in huce haushi,dakunsan bakin cikim da wannan shashsahn ya tsunduma mu dabakuyi magana ba"mai motar akasa yaje ya tadoshi,zuwa yayi kuwa ya tasheshin harya fara mita wai ya akayi ya dade gashi saboda jiranshi dayake tayi har yayi bacci,shidai baice komai ba mai motar,ya yo gaba,Abdallahn ya biyoshi abaya da yar jakarshi a hannu,saidai kuma me ganin yansanda mota mota dakuma Abba ne yasashi yarda jakar hannun nashi,harda juyawa wai zai gudu,inaa inbanda ma wauta da kama kai tayaya zaayi ma ya iya guduwa anan wajen,"idan kasake kokarin guduwa sai mun harbeka"daya daga cikin yansandan yace dashi bayan sun sakala mishi ankwa,"ina yarinyar mutane take?"suka fara watso mishi tambayoyi,shiru yayi yaki magana,yaki kallon Abban dukda kuwa magangnun dayake jefo mishi,ai bai ankara ba Abban ya kwasheshi da wasu marika guda biyu ,"nace ina ka kai min yarinya,?"amma Kememe yaki magana don ganin komai yake kamar ma amafarki,shi abin dayafi daure mishi kai ma shine tayaya ma akayi akasan tana nan,kodayagabawan Allahn daya saidawa mota a maiduguri take yasamu ansar tambayoyinshi tunda babu makawa yasan shine,to amma ko shi dinne yafada ai baisan wajen nan ba,saidai kuma ko yansandan,kasan bindiga sukasa suka fara dukanshi saboda rainasu dayake nemanyi ana magana yayi shiru,icen dazu Abba yadauka yafara zuba mishi shi kuwa ta ko ina cikeda bacin rai,yansandan na rikeshi gudun kada ya mishi wata illar kuma suzo ayi biyu babu su basu samu biyan bukata ba ga zuwan banza,"ku kyaleni in kasheshi yadda ya kashemin yata"Abba yacigaba da fada anata ririkeshi,"wannan ne zai zama karo na karshe dazamu sake maka magana ina yar mutane?"dansandan kasar tasu yace dashi cikin yare,"nifa ba saceta nayi ba matatace na aura to kuma don na dauketa na tafi da ita wani wajen shine nayi laifi nida mallakina?ban fishi iko da ita ba (Abban)"?yabada ansar cikin yare,yanata wani babbada fadi yana cika yana batsewa,"idan kasake magana da wannan yaren ina wajen nan saina fasa maka baki tsinanne"Abba yacd cikin fada,inane wai gidan nashin ya kara,"munafuki ina ne gidan nashi nace" ya juya ga mai motar amma baisan mai Abban yake cewa ba saboda bayajin hausa,hakan ne yasa sauran yan sanda juyowa gareshi tunda wancen dai(Abdallan) da alamu dai ko zaa kasheshi din bazaiyi magana ba saboda tsananin taurin kai,ai yana nuna gidan Abba ya tafi gadan gadan,tunda ko kofa babu,wasu daga cikin yansanda suka rufa mai baya wasu kuma suna tsare dasu Abdallahn a waje,wayannan yan iskan karnukan mai gadin ya sako,saboda duk abinda yake faruwa akan idanunshi ne tundaga zuwansu kawo yanzu,ai yan sandan nan basuyi wata wata ba sukasa bindiga suka harbesu,shima mutumin aka saka mai ankwa.
wannan harbin bindigar da mutan gida sukaji ne yasasu duka tsorata saboda basu tanajin irin hakan ba,to wace kara dama zasuji banda ta tsawa idan ana ruwan sama.Ita tanaji tasan karar bindiga ce amma kuma bata wani saka buri ba aranta,don tasan idan ma masu bindigar a waje suke saidai sugama abinda zasuyi har su tafi ba iya fita zatayi ba,hakan nema yasata cigaba da iza wutar murhu abinta,sannan tadan shiga bukka.
Abba da yansanda kimanin guda biyar ne, suka karasa cikin gidan,hannayensu rikeda bindiga,inda suka tarar da mata rututu da yara kowa da sabgar dayake,sai iya akan tabarma ai dukkaninsu suna ganinsu saida suka razana,wanann wane irin yanayi ne dasuka tsinci kansu,wayanan wane irin mutane ne wannan?yansandan ne suka fara tuhhmar su akan faridan sannan suka sanar dasu cewar su yansanda ne masu hukunta mutane marasa gaskiya,donsunga alamun ma basusan ko suwaye ba,suka kuma sanar dasu cewar Abdallahn ya shiga hannunsu,zasuyita hukuntashi har saiya fito musu da wadda suke nema idan kuma ya kasheta ne to fa su sani suma dukansu sai an hukuntasu abin ya shafesu,"yau kuma su waye suka shigo gidannan? abinda bata taba gani ba tunda tazo"tayi zancen ne afili tareda dan lekowa,"nace ta mutu ko kuwa tana nan ?"yansanda suka cigaba da watsa musu tambayoyin, suna kuma musu hotonta,amma sunki magana,iya kuwa tariga tarikice taji ance a capke Abdallah,"Abba"tace bayan ta fito,a hanzarce ya juyo jin muryarta,tareda nufarta cikin sauri,amma kafin ya karasa ta fadi,saboda tsananin shock,"farida,farida ki tashi kinji,kiyi hakuri dana makara haka na dauki tsahon lokaci ki yafemin"Abba yace cikin kuka,"officer itace wanann,wallahi"yajuya ga yansandan,yana hawaye,kallonkallo suka fara yansandan suna kuma duban hoton nata dake hannunsu,suna kuma dubanta,"Alhaji ka tabbata kuwa?wannan ta jikin hotonfa ba ita bace wannan wannan fara ce"sukace,"ya zaku dinga min musu nida yata,kunfini sanin ta ne,nace wannan ce,ko bakuga yanayin inda take ba,wannan ma kadai ai ya isa yasa ta chanja kamanni"yace,sudai mutanen gida kawai kallo suke don sunma kasa gane meke faruwa,iya kuwa sai ihu take harda biyosu officer waje,sauran matan suka rufo mata baya don ganin yaya lamarin zai kasance.
Suna karasowa soro suka tarar da gawawwakin karnukansu a yashe,dasuka karasa waje kuma sukaga Abdallah da ankwa yanacin duka,ga maigadin nasu shima an daure.
Cikin yaran harda wayanda basu taba fitowaba tunda suke,ita kuwa sadiya dadi kawai take ji mata,dama tace (ita faridan)tasan Allahnta zai dubeta ya ceceta,duk daren dadewa,kenandagaske Allahn yanajinta yana ganin halinda take ciki kenan?wayannan sune tambayoyin data dinga yiwa kanta.
Ana kokarin shiga dashi motane iya ta taho aguje tana rikoshi,"ku suwaye dakuka isa kuce zaku hukunta min yaro?har akwai wanda ya isa yace zai mai hukunci "tacigaba da surutai,"meyasa suke maka haka?"tacigaba da tambayarshi shidai babu abinda yake cewa saboda tsananin mamaki ga farida yana gani an fito da ita ansata a mota,wato dai taci nasara kenan mahaifinta yazo ya nemota hmm,"wai wannan din wacece ne datake neman bata mana lokaci?"Abba yace cikin fada ganin iya tana hanasu tafiya,"wai mahaifiyarshi ce"daya daga cikin yansandan yace,"mahaifiya?to kuwa shashasha ce ke baki kuma san yakamata ba,wace irin uwace zatayi abinda kikayi?" Danki ya sato yar mutane yakawo bakisan kisashi ya maidata ba"yace cikin bacin rai ,"officer kusa mata ankwa daallah mai kuke jira"dama dole ai atafi da ita tunda indai mahaifiyar kwaraice ai yakamta ace tabashi shawara ko ba komai sanda yace mata ya taho da yarinyar nan batareda sanin iyayenta ba amma tayi shiru suka cigaba da azabtar da ita dabaki daya"cewar dansandan,wani marin Abba yasake aikawa Abdallahn dashi,yajuya yashige mota.
To haka dai lamuran suka kasance,aka sakawa iya ankwa itada danta akasasu a bayan mota da maigadinsu,sai direban shi daaka sallama bayan an mai fada akan ya kasance mai nutsuwa dasaka ido akan aikinshi,bawan Allah kuma mutumin maiduguri aka sashi a mota ta daban suka kama hanya.
Su kuwa mata da yaran gida sunma rasa me zasuyi,don basu masan inda zaa tafi dasu iyan ba,sai yau suka gane takamaimai dalilin zuwan faridan gidan wato ashe kawota yayi bada saninta ba,ko na iyayenta.