RUWAN DAFA KAI 2

1.6K 152 9
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

13

Yau kwana kusan nawa kenan dakama wancen bawan Allahn dan kasarsu Abdallah daya saidawa  mota suka kuma tafi congo tare,shi yama rasa dalilin kamanshi daakayi sai tambayar laifin dayayi yakeyi baa cemishi komai,saidai kawai ace yayi bayani yadda komai ya gudana,yace wane komai ance ai karya yake yace baisan zancen daake ba,zancen daya dade da karade duniya,shidai baigane ba don tun ranar dasuka tafi bai sake dawowa ba sai yau.
To hakane yasa lamarin daure mishi kai,kuma sai cewa ake yayi bayani,shi kuwa  yaki cewa komai yaki basu  bayanin dasukeson suji din,sukuma gani suke tsantsar rainin hankaline kawai ai karya ma yake yace wai baisan mai suke cewa ba, tunda dai ai sunji ance abokinshi ne don haka kuwa babu yadda zaayi yace wai bai san inda yake ba,kuma ma duk wannan  tsahon lokacin daaka dauka ana nemanshin ina yaje?.Ganin rainin nashi yamusu yawa ne yasasu suka fara subirbidarshi tunda haka yakeso.

Saida yaji  ajikiinshi matuka,suka dai tabbatar din dagaske baigane zancen ba sannan sukayi mishi bayanin abinda sukeso suji din,ajiyar zuciya yasaki mai nauyi kanshi duk ya daure sannan yafara fadamusu abinda yasani gameda Abdallan dakuma abinda yafaru ranar  da  sukazo maiduguri shida matar tashi,duk taji jiki,harya tambayeshi ko lafiya yace komai kalau gajiya cedai kawai,ya kuma siyar mishi da motar,saboda yana bukatar kudin,kuma ranar tayi daidai da ranar dashima zaije ganingida hakan nema yasa suka hau mota daya.
Kasancewar kasarsu daya shiyasa suke mutumci kuma hakan kan faru lokaci zuwa lokaci don shi a maidugurin yake dazama,basa ma haduwa da Abdallahn sai zaije cen gida congon ko kuma idan yadawo,har yakan bashi sako ma ko shi ya taho mishi dashi,kunsan dai yadda rayuwar nan take duk ranar daakace yau ba a kasarka kake ba kana kasar wasu kuma ka hadu da wani dan kasar taka to dole akwai wani mutumci na musamman,"wallahi wannan shine gaskiyata shine gaskiyar abinda nasani"yace,"to dakukaje cen din sai meya faru"wallahi bansani ba ,a babban birnin kasar na kinshasa,anan muka rabu,kowa ya sake hawa motar dazata sake sadashi da kauyensu,"yace,"karya kakeyi"suka hayayyako mishi,hakan ne yasashi rantsuwa,Allah da annabi kasancewarshi musulmi akan wallahi iyaka abinda  yasani  kenan kuma kozasu kasheshi bai san inda garinsu Abdallahn yake ba saboda kungurmin kauyene sosai yadai san sunan kauyen shine kawai abinda zai iya cewa.

Ai baayi wata wata ba aka kira Abba aka sanar dashi wannan sabon cigaba daaka samu,kuma ana tunanin tasashi agaba shi bawan Allahn atafi cen congon tunda yafadi sunan garin da yardar Allah zasuyi nasara,"Officer wannan tafiya yazama dolene ayita dani,"cewar Abba cikin wani yanayi dayama kasa  gane cewar ko farinciki ne,ko kuwa fargaba,don kuwa yakasa tsaye ya kasa zaune.

"To shikenan Alhaji,tunda kace haka,"kawai officern yace sanin cewar fa Abba akan zancen yarinyar nan babu wata shawara dazaa bashi nawai yazauna basai yaje ba yadauka,bama zai yiwuba shiyasa yabashi wannan ansar kawai azauna lafiya.

Babu wani bata lokaci yayi booking flight,bayan an mishi visa sharp sharp,ya kuwa ci saa akwai jirgin dazaije kinshasan a gobe da dare.

Sudai su mama babu abinda suke sai addua suna kuma fatan Allah yasa  karshen komai ne yazo,yasa kuma adace.

Washegari,yan sanda suka tasashi agaba,akayi mota biyu,suka kama hanyar congo,bayan Abba ya tura musu da makudan kudi,don da niyya yayima duk atafi ajirgi saboda ayi saurin zuwa to amma visa ce zata bata musu lokaci tafiya ce ta kwana biyu,kafin kuce meye wannan kuwa sun kai saboda  hanyar mai kyauce kuma babu wani tsaye tsaye kasancewar motar aikinsu ce.

Sanda suka karaso shi Abba yama riga ya kwana,hakan ne yabasu damar yin waya ta wayar hotel din daya sauka,tunda sun kwace wayar bawan Allahn,to dama numbarshi tacen  aka bawa Abban,suka kuma gaya mishi lokacin dasuke fatan karasowa,inyaso sai ya kira to haka kuwa akayi.

Shidai bawan Allah duk yabi yarikice,tabbas baisan haka alamrin yake ba nawai saceta yayi ya gudu da ita,tabbas wato mugu bashida kama,waye zaice Abdallahn zai taba aikata duk irin abubuwan daakace ya aikata,yana abu simi simi,kullum cikin faraa.

Wajen yan sandan garin nasu aka tafi don neman hadin kansu suma,tunda  dai su bakine basazo kai tsaye ba su fara musu aiki agari dole yakamata su nemi izini da taimako kuma,haka kuwa akayi inda suka karbesu hannu bibbiyu,suka kuma basu goyan baya dari bisa dari,to  masu jin turanci ma kadan ne acikinsu.
A haka  dai aka dinga bayani har suka dai gane halinda ake ciki suka kuma yi alkawarin tallafawa.

"Tsakaninka da Allah nakeson kafadamun duk yadda abinnan yake"Abba ya ce da bawan Allah  bayan sun hadu gabaki daya,yadda yafadawa yan sanda ya fada mishi,"to Allah yana gani dai yakuma san  maigaskiya,Allah yasa mudace."

Babu wani bata lokaci aka kama hanyar kauyen gabaki dayansu tunda yafadi sunan garin kuma yansanda sun gane tunda shi baimasan garin ba bai taba zuwa ba yanadai jin labarin,tunda kullum a kinshasan suke rabuwa ko su hadu.

"Ki taho mu tafi mana,meyasa kike mana haka?kinsan halin damuka shiga ciki kuwa na rashinki?haba farida"cewar mama cikin tattausar muryarta,"mama kiyi hakuri nima nashiga wani hali kamar yadda kike gani amma inason mijina da yanuwanshi dabazan iya rabuwa dasu ba"haba farida dubeki fa kowa yaganki yasan cikin tashin hakali kike,haba,agaskiya bazamu iya barinki cikin wannan halin ba,"maman tafara jan hannunta don tafiya da ita ,"kisakeni nace bazan biki  ba ni anan zan zauna,wajen nan shine rayuwata shine gidana gidan mijina kisakeni  don Allah"tacigaba da kuka tana tittirjewa tareda kokarin fizge hannunta daga rikon mama,"yanzu kin gwammace kicigaba da zama anan ?"maman tace cikeda damuwa,gyada kai tayi alamun eh,"to agaskiya bazai yiwu ba don naga kamar ma kin samu  matsala bakida lafiya"Maman tacigaba da janta amma tana cigaba da tirjewa ita adole bazaa rabata da mijinta ba,har tana kama bango adole bazata bar gidan ba,"kisakeni nace,ni banason in tafi wani waje,don  idan na bar gidannan  bazan iya rayuwa ba,wayyo mijina"tacigaba da kuka,shima yana gefe ba abinda yake sai kuka,mama kuma janta take kawai,"kisake ni nace kis......"innalillahi wa inna ilaihi rajiun,tace tareda zabura tafara zazzare idanu,wannan wane irin  mafarki ne?mekuma yake nufi?saboda yau kwana kusan nawa tana ire irenshi,"ya Allah kasa yazamemin alkhairi"tace tareda daga hannayenta sama,tana mai fashewa da kuka,"tayaya ma zaayi inba mafarki badai wai mahaifiyyarta tazo tafiya da ita afitar da ita daga cikin wannan kangin,amma tace wai ita sai an barta anan,ya Allah katabbatarmin da alkhairan  dake cikin mafarke mafarken nan ka nisantani da sharrin dake tattare dashi, ya Allah tacigaba da kuka.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now