RUWAN DAFA KAI 2

1.7K 127 12
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

23

Haka dai rayuwa tacigaba da gudana,Abu har tagaji damagana don bama sauraronta yake ba indai akan zancen farida ne,hakan neyasa ta hakura dayi ganin duk sanda tayi din ma sai yashiga damuwa to saboda azauna lafiya dagudun damuwarshi ta rabu dashi tacigaba da addua akan indai zaman nasu akwai alkhairi itada faridan Allah ya tabbatar ya kuma kawar da fitina,idan kuwa babu Alkhairi to Allah yazaba abinda yafi alkhairi,tadamu ne matuka gameda lamarin nan don ita aganinta idan faridan tadawo dakinta saita fi kowa farinciki saboda dama abin ya dade yana damunta na ganin cewar fa suna zaman zamansu ta zo ta hargitsa komai,don tayi imanin dabadon zuwanta ba,da yusuf zai cigaba da hakuri ne kamar yadda yasaba da matar tashi,to amma inaa kunsan mutanen duniya da gulma da tsugudidi ayita gutsiri tsoma akan abinda baa san yadda yake ba,wayanda basusan yaya akayi lamuran suka kasanceba cewa akeyi tazo ta kwace miji ta kori matar gida, tabbas hakan babu dadi ko kadan,to amma kuma yaya mutum zaiyi kaddara ce fa tariga ta faru Allah ya tsara haka dolene haka ta faru babu wanda ya isa ya chanja hakan.

Har anyi bikin safina,ta tare agidanta babu abinda zamu musu sai fatan Alkhairi.
Lokacin bikin ma Allah kadai yasan irin mazan dasuka dinga kawowa faridan Hari,anga yar fara mai kyau,dukda ma dai bawasu shagulgula akayi ba,kamune kawai da mothers eve sai daurin aure,kuma duka events din farida shigar mutumci tayi,don ko su atampa ma bata saka ba,Abayoyi ne kawai masu kyau tadinga amfani don tafi sakewa,tunda wani yin dinki da fitoda sura da matse jiki a wajenta yazama tarihi.

Duk wanda yazo mata da zancen soyayya saidai ta bashi hakuri,don su mazan ma duk zata suke budurwa ce ganin ta da dan jiki,indai ba fadawa mutum akayi ba babu wanda zai taba tunanin ma ta haihu,to haka dai aka gama biki aka watse,batareda tabawa kowane namiji fuska ba.

"Yanzu farida shikenan haka zakiyita zama kuma?rayuwa fa bahaka take ba"mama take mata fada,bayan anzo ance wani yana sallama tace ace bata nan,saboda kusan kullum akwai wanda zaizo wajenta amma bazata taba bada fuska ba barema har ta fita ace zaa saba ayiwata maganar aure,kunsan mutuniyar badai farinjini ba mashaallah,"mama don Allah don Annabi ki bar lamarin auren nan,wallahi ni yanzu banki ba daga nan har karshen rayuwata inyi zamana ahaka saboda babu wani namiji dazan sake yarda dashi ni Allah ma yasani"tace cikeda ladabi kanta a kasa,"naji nakuma gane abinda kike nufi amma ni abinda nakeso ko gane shine ai ba duka aka taru aka zama daya ba,don mutum daya yamiki abu shikenan saikiyiwa kowa kudin goro?haba ke kuwa"cewar maman cikin rarrashi,yar dariya tayi kawai,tabbas mama bazata taba gane manufarta ba,amma dai bakomai,dasannu zata gaji da magana har tayi shiru don itakam bawai wasa take ba namiji ya fitar mata arai tagama zaman aure.

Tana zaune tana dan taba kallo wayarta tafara kara alamun shigowar kira kodata duba hajiyar yusuf tagani,cikeda ladabi kuwa tadauki wayar ta kara a kunne tareda sallama,inda Hajiyar ta ansa daga dayan bangaren,sannan suka dan gaisa,"ni kuwa inataso inji ya kukayi da yusuf ne farida?"Cewar hajiyar ganin watanni kusan nawa kenan dataje gidan nata hartabata numba,amma har yanzu bataji wani labari ba mai gamsarwa daga dukanninsu su biyun,hasali ma shi cewa yake ma wai haryanzu bata kira ba,idan hajiyar tamishi zancen don ya riga ya fuskanci inda ta dosa,shi mamaki ma yake wato har yanzu tana sonta kenan?yazata abubuwan dasuka faru zasu sa ta rage sonta ashe yanzu ma tafara ji da ita hmm,wai dayace ma bata kirashin ba Hajiyar harda cewa wai shi to ya kirata mana,yace bashida numbar tata,Babu bata lokaci Hajiyan ta tura mishi numbar tata tace ai watakila ita faridan nauyinshi take ji shiyasa,shikuwa bazai kirata bane kawai,amma bazai bari Hajiyan tasan da haka ba,(Hmmm su Malam yusuf),ita kuwa farida tanata bangaren duk yadda abubuwan suka faru ta kwashe tafadawa Hajiyar, tun daga kiran datake baya dauka har tura sakonnin,"ah ah,amma meyasa yusuf zaiyi haka kuwa"tace aranta,"karkiji komai inaga dai abubuwan ne suka mushi yawa,ko bai gani ba,amma nasan ya dade da yafe miki kinji,karkisa komai aranki ki kwantar da hankalinki"cewar hajiya,dan murmushi kawai tayi"haba bakomai ai,Bashida laifi don yaki daukan wayata Ko yaki bani ansar sakonnina hajiya,yanada ikon dazai nuna fushinshi"tace cikin nutsuwa,"Allah sarki ki kara hakuri dai kinji komai lokacine,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"sai lokacin ma take jin labarin haihuwar Abun,inda tayi Allah ya raya takuma yiwa Hajiyar godiya, duba da yadda take nuna damuwarta agareta,sannan sukayi sallama ta kashe wayar.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now