RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA21
Masallaci yatafi kai tsaye,yafara gudanar da salloli cikeda neman dacewar wannan aiki dazaayi yanakuma fatan Allah yasa daga ita har jaririn su kasance kalau,har cewa yadingayi idan dai mutuwar jaririn ce zatasata tasami lafiya ita,ta rayu Allah ya tabbatar da hakan,tabbas yakai kololuwa wajen kaunar Abunshi ashe,da har yake furta irin wannan kalami haka da bakinshi,na zancen jaririn nasu ya mutu ita ta rayu.
Haka dai yacigaba da zama yanata adduoi,hankali tashe idan takama kuma yayi kuka,dan kishingida yayi baisan sanda bacci mai nauyi ya daukeshi ba,bai farkar ba sai bayan kamar awanni hudu haka,aikuwa a gigice ya tashi,tareda dauko wayarshi ya duba,tunda a silent take kasancewarshi cikin masallaci,bazaiji kira ba,kiraye kiraye yagani duk daga Aunty bila Adadin,"innalillahi"yace afilici, a kuma rikice sannan ya bude sakon text din data turo, bayan tagaji da kiran,taji ba ansa,"ina kashige ne sai kira nake,ana nemanka,Ansamu Baby girl"shine kawai Abinda ta turo,"aa to zainab din kuma fa"yace afili adai rikicen,dubada yayi Auntyn bata ma ambaceta ba,cikin hanzari yafito daga masallacin ya wanke fuskarshi sannan yanufi asibitin cikeda zullumi,dajin haushin kanshi na yadda akayi har ya yabari ya iya bacci,acikin wannan tashin hankali dayake,Addua dai yadingayi a hanya na komai ya kasance lafiya.
Yana shiga inda yabarsu dazu yanufa kai tsaye,amma baigansuba,hakan ne yasa yafara lalubar numbar Auntyn,amma shiru,gabanshi dai sai faduwa yake cikeda tsoro,sai kira yake shuru,tambaya yafarayi amma cewa ake baa gane me yake nufi ga,sai a kira nawajen nawa dai dakyar sannan Auntyn ta dauka yaji muryarta kasa kasa,"shikenan"yace aranshi zuciyarshi na bugawa da mugun karfi kamar zata fasa kirjinshi ta fito,don inda akwai wani akusa dashi babu abibda zai hanashi ji.
Kwatancen inda zai sameshn tamishi,"kice min wani abu don Allah gameda Zainab din mana"yadinga tambaya,babu abibda Auntyn take cewa sai yadaizo kawai,cikin anyin jiki da karayar zuciya hadeda saddaqarwa,ya isa dakin data kwatanta mishi,"shikenan yasan yana shiga gawarta kawai zai gani"zuciyarshi tadinga raya mishi,take wasu hawayen suka fara zubowa,masu dumi,hannu na karkarwa ya fara murda kofar,ahankali ya bude yashiga ,ga dai likitoci da sauran maaikatan lafiya sun zagaye gadon,baya ganin komai,yarinyar kuma an sakata acikin dan gado,kallo kawai yabisu Auntyn dashi, irin mai nuni da shikenan fa nasan tatafi kenan dinnan,sannan ya nufi gadon nata da likitocin suka zagaye,masu karatu yusuf ko takan yar jaririyar baibi bafa,ta uwar yar yake tukun,itace damuwarshi,yanaso ya leka yagani amma tsoro yakeji kar ya gamu da gamonshi,ganindai dai yana bata lokaci ne yasashi shahada tareda lekawar kai tsaye zuciyarshi cikeda tsoro bayan ya fawwalawa Allah komai,ganin dai ba motsin take bane yasashi fara tambayar su ko lafiya,"Lafiya kalau,Allurar daakayi matace dai ta bacci bata saketa ba....."Alhandulillah Allah nagode maka"ya katse su tareda zubewa akasa, sai kuma kukan farinciki shi kanshi baisan yanason yarinyar nan haka ba,dariya jamaar wajen sukasaka dubada yadda ya matukar damuwa da ita,tabbas wannan shi ake kira a true love,dukda ai basusan meyace ba bajin yaren nashi suke ba amma dai sunsan Tsantsan farinciki yake da murna,"Bata mutu ba Annty"yajuya gareta cikin zumudi, murmushi tasakar mishi kawai,"Eh bata mutu ba Yusuf kadai tsorata ne sosai,gashi ko yarinyar taka ma baka leka ba,saboda bata ita kake bako?"tace cikin wasa,sai lokacin kuma yaji kunya,to Amma ai ba laifinshi bane dole mutum yanason yayanshi amma wadda tabada yayan ai ita tafi cancanta aso,kafinsu,bare ita Abu datasha wannan irin gwagwarmaya haka.
Yar kyakkwawr yarinya yagani mashaallah,yasa hannu yadaukota cikeda kauna,yafara mata adduoi,amma fa katuwa ce,shiyasa ma Abun takasa haihuwar dakanta.
To masu karatu masu rokona karna kashe Abu,Abu na nan da ranta,ai dama bazan kasheta ba,me akayi kenan😂😂,muje zuwa.....
![](https://img.wattpad.com/cover/179970084-288-k235625.jpg)