RUWAN DAFA KAI 2

2K 149 1
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

5

Shi yanzu ya zaiyi,hakika yasan bai kyauta ba kuma yaci amanar yallabai,mutumin daya rikeshi da amana shekara da shekaru,ya yarda dashi fiye ma da yanuwanshi,kai yayi danasani wallahi,to amma kuma tawani bangaren ai ba laifinshi bane,waccen yar iskar ce tajawo komai(farida),tunda har ya rabu da ita tadinga bibiyarshi.

"Mtsw"yaja dogon tsaki cikeda  backn rai,a hasale ya nufi inda take din,yafara kunceta,ganin yanata bata lokaci,ga lokacin dai gudu yake,saida yagama kunce hannuwan da kafaffuwan sanann yafara mata kashedi,"bawai kinga zan bude miki wannan tsinananen bakin ba kice zaki gayamin ba dadi,wallahi saina baki mamaki,"ita kuwa jinshi take kawai,amma tariga tasha alwashin duk abinda zai mata fa saidai  yayi,amma saitayi magana tunda taji duka zantukan yallabai.

Ai yana gama kunce bakin tafara fasa ihun dayasan bawai jinta zaayi ba,tsayawa yayi kawai yana kallonta,don yasan duk zatayi ta gama ne,"meyasa kamin karya kacuceni?"hawaye wani nabin wani,"dama ashe kai direba ne,kuma gidan nan ma banaka bane?to wai wanene kai Abdallah,nace wanene k......wani wawan  naushi yakai mata a fuska take ta bingire ta sume,dama duk fuskar ta kumbura hanci da baki kuwa tuni sun dade dafara  tsiyayar da jini.
Yariga yasha alwashin saiyayi maganainta shiyasa  ma bazai iya tafiya yabarta ba yazama dolene duk inda zashi su tafi tare.

Masu siyan kaya yaje ya nemo,dangin furniture,kayan kitchen su tukwane,da duk wani abu dazai iya siyuwa,kafin kuce meye wannan kuwa sun kwashe komai,dadinta ma dai sun siya da daraja tunda komanta mai kyau ne mai tsada,hatta kayan sawa bai barmata ba,don har irin dillalan nan  ya nemo,saboda tantiri ne duk yasan  masu irin harkar.

Motar tata ma da yayi niyyar siyarwa saidai kuma yaga zata mai amfani,hakan ne yasashi  dauko wata numbar mota da yasiyowa yallabai kwanaki ko amfani ma baayi ba ya kunce tatan ya daura sabuwar saboda tsaro.

Duba lokaci yayi,yaga saura  baifi mintina talatin ba cikin lokacin da yallabai ya debar mishi,tabbas yana hanya,kuma yasan idan yabari yazo ya taddashi  bazaiji da dadi ba,hakan ne yasashi kinkimota ya kwantar da ita a seat din baya,ya dauko jakar kudinshi,sannan suka fice daga gidan,ya nufi wani dan chemist abayan layi,yamusu karyar cewar wai  kanwarshi ce mota ta kade,to chemist ne dan karami,dan abinda zasu iya  mata,sukayi, aka sallamesu,babu yadda basuyi dashi bama akan yakaita babban asibiti don su anan wajen din bawasu kayan aiki bane dasu yace suyi kawai abinda yasamu,gudun dai kada su zargeshi ganin sun dage ne suka rabu akan cewar zai kaita asibitin.

Tanaji tana gani babu damar magana banda hawaye babu abinda idanunta ke fiddawa. Don lamuran ganinsu take kamar ma amafarki.
Kara kwantar da ita yayi a bayan,sannan aka dau hanya.

Ta bangaren gidansu kuwa,haka kawai tunda akayi auren nan hankalin mama ya kasa kwanciya kawai tanaji ajikinta yarinyar tata baa cikin kwanciyar hankalai take ba,ganin tana cikin damuwa ne yasa Abba tambayar ko lafiya,inda ta labarta mishi,"hmm Asiya kenan dama akan wannan dalilin ne yasa duk kikabi kika zama haka kika kasa ci kika kasa sha?ni naga ikon Allah fa to yanzu  mekikeso inyi akai?,karki manta fa yarinyar nan dakanta ta kawo yaron nan,kuma aka  musu aure irin na soyayya,kuma sanin kanki ne kinfi  kowa sanin halin farida inda tana cikin kunci datuni kowa yaji don saitazo ta fada ko ta kira awaya,to babu wanda tayi acikin hakan,kuma saikibi ki kasa zaune ki kasa tsaye?"yace bayan ya kurbi shayinshi,"rashin samun wayar tata shine ni abin damuwata tun jiya fa nake kiranta,bana samu,kuma dai baa ce rashin chaji bane ko?,kuma dai kasan maitar waya irinta farida da aturur batada aiki sai danne danne,ace yau kwana kusan biyu wayar batayi,kuma azata lafiya Alhaji?"tace cikeda marairaicewa,"nidai banason naiman magana Asiya,yara sunacen suna  cikin kwanciyar hankali,ki nemi ki tada naki,yau inda itace takiraki tace kaza kaza ke kinsan sainafi kowa shiga wani yanayi to ba ita ta kira ba shikenan daga andan kira wayarta anji shiru,sai adinga tunanne tunane marasa amfani,lafiyarsu ma kalau"yace a hasale,"hakane,Amma dai da mamaki, duka wayoyin fa?"tasake cewa,ganin yaki kulata ne yasata shiru,tareda fadin "Allah yasa dai komai lafiya".

Safina tunda taci alwashi itama,ta samo wani Alhaji mai mata daya, yazo har anyi gaishe gaishen dazaayi saka rana kawai ya rage itama ta kikkkira yaruwar tata don ta cashe mata tayi neman magana amma bata samunta haka zalika ta tuttura mata sakonni a watsapp amma shiru,sai take tunanin ko iskancinta ne ya motsa ta kashe wayoyin gabaki daya tunda amarci takeci.

Itadai batasan ya akayi ba ko kuwa dai ya lamuran suka faru,bakuma tasan dadewar datayi tana bacci  ba,ko ma a sume takenema oho?farakawa  dai kawai tayi taganta awani irin daki,irin ginin kasa dinnan,ta kalli sama taga kamar yar bukka,gawasu  yan sashe jikin ginin guda biyu,wanda babu tantama tasan daya kofa ce daya kuma window,amma dukkaninsu an sakayesu da dan zani,kallon inda take kwance tafarayi,taganta kan wata katifa irin mara rigar nan tayi daka daka,ta shafi kasan dakin taga ta kwaso kasa a hannunta,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun"shine kawai abinda take fada,don tunaninta babu ma tantama saceta akayi,don nan dai yafi kama da gidan yan yankan kai,a rikice kuwa ta mike,har lokacin dai hijabinta na jikinta,tayi  kofar,ta daga labulen,ta leko,inda tayi arba da mata rututu,don zasuyi goma koma sufi,adan tsakar gidan,ga bukkokinan kashi kashi,alamun kowa da nashi kenan,yara na gudu ko ina suna wasa,ga dai kayan jikinsu ma wasu iri,take duk suka maida dubansu gareta,suka fara yare wanda babu tantama tasan faransanci ne,ana kallonta ana kyalkyala dariya.
Kwala wani irin razannanen ihu tayi,tasake faduwa sumammiya.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now