RUWAN DAFA KAI 2

1.4K 121 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

20

cikin dare Abu ta farka saboda ciwon daya addabeta,tun tana iya jurewa har takasa,tasa kuka,don ko tashinshi ma kasayi tayi,sai kukan nata ne ya farkar dashi,ganinta  cikin mawuyacin  haline  yasashi rikicewa batareda wani bata lokaci ba ya dauko Mata Abaya ya zura mata ya yafa mata dan mayafi,don yasan babu makawa abinne yazo,sai sannu yake mata  bata ko iya ansawa,Amin ya shiga ya dauko bayan  yakai kayayyakin  nasu mota da ita kanta sannan sukayi asibiti.

Duk da dai  cikin darane wajen karfe uku,amma ahakan  ya kira Aunty  Bilki,saboda koda yaushe saita jaddada mishi akan cewar daga sunga alamu fa su kirata,komin dare kuwa,to hakan kuwa akayi kafin kuce kwabo kuwa ta bayyana itada wata yarta,a asibitin.

Abu ana cen ana shan gwagwarmaya anata fafatawa,donma dai tana dan iya daurewa tayi adduoi,ga likitocin da sauran maaikatan wajen na bata baki,ana karfafa mata gwiwa,cikeda kulawa da tausayi,suma su yusuf din a wajen ba abinda  suke shida su Auntyn banda adduoi,duk hankalinshi yabi  ya tashi ya rikice,tanata dai kwantar  mishi da hankali tana bashi baki akan komai zai kasance lafiya inshaallah,Allah yasa kawai yake cewa amma duk  yabi yafita  hayyaci, ya rikice da lokacin  farida da yanzu bazamu iya banbance tashin hankalinshi ba.

Barmusu Amin din yayi ,aka bashi kaya yasaka shima ya shiga,bayan  tun dazu dazaa shiga akace  idan yanaso yashigo babu damuwa, yace aa,saboda tausayi bazai iya jure ganinta cikin wahala ba,toh yanzu  dai hankalinshi ya kasa  kwanciya yana ganin shigar  tashi ce zata iya kawo sauki.

Yadda yaganta ne yasa zuciyarshi  karaya duk  ta galabaita kamar ba dazu suka gama  hira ba tabbas  haihuwar nan babu sauki dai,gashi bata masan waye akanta ba,amma dai fatanshi yanzu shine Allah ya raba  lafiya,baisan sanda wasu zafafan hawaye suka fara zubo mishi ba,ganin yanata mata magana amma ko ansa bata iya bayarwa ita kadai tasan metakeji.

Har akayi  Asubah ana abu daya dole yafita  yaje yayi sallah yayi adduoin neman dacewa, sannan yadawo,amma shiru,hakan ne yasa yadinga cemusu  suyi abinda yakamata sumata,tadaina wannan wahalar datakesha,idan akwai wani magani ko wani abu da zasu iyayi su mata,kallonshi suke kawai suma cikeda tsantsar tausayinshi dubada yadda yake masifar kaunarta,yakuma damu da ita,baabinda suke cemishi sai yayi hakuri ya kuma kwantar  da hankalinshi  haihuwar  farice dole saitayi wannan dadewar takuma sha wahala  tukun.

Kai abu,fa kamar  wasa har ana neman azahar shiru,suma kuma  lokacin  likitocin sun  fara tunanin mata cs saboda takusa wuce qayyadajen lokacin daya kamata,awa daya kawai suka kara  mata akan indai  har lokacin  yacika bata haihun ba tofa saidai ayi cs din kawai aciro abinda ke cikin nata,don dan ma yafara gajiya bugun zuciyarshi yafara kasa.

Shi bama jinsu yake ba don bama gane abinda suke cewa yake ba,babbar damuwarshi itace kawai yaga  tafita daga cikin azabar datake.
Agaskiya tashin hankalin dayake ciki yanzu yafi karfin tunanin mai tunanin,harda  kuka don ba laifi shima akwai saurin karaya sai hakuri suke bashi ana kwantar mishi da hankali.

Ai kuwa dai babu abinda ya chanja,mintina talatin cikin awa dayan daaka qayyade nayi,aka fara shirye shiryen shiga da ita,don idan aka ce zaa kara daukan wani lokaci komai yana iya faruwa.
Yanaji yana gani yasa hannu shaidar amincewa da yin aikin.

Gani yayi alamun bakinta na motsi tanaso tace wani abu,cikin hanzari kuwa ya matsa kusa da ita,don jin mezatace,"mine mezaayi min?"tace dakyar hawaye wani nabin wani,hakan ne yasashi share nashi dasauri wai don karta gani,"bakomai,Cs zaamiki ki kwantar da hankalinki kinji"yace dakyar,"cs?to idan na mutu fa,ance fa ana mutuwa"tasake cewa,kukane yaci karfinshi yama  kasa bata ansa amma bayason tagani hakan ne yasashi kasa da kanshi,"kiyi hakuri inshaallah bazaki mutu ba,zamu rayu tare har abada kinji,nima don ba yadda zanyi ne shiyasa zan bari ashiga dake bazan iya cigaba da jurar ganinki cikin wahala ba,gashi babyn yafara gajiya shima,"yace da ita cikin karfin hali,"Allah sarki,to kace suyi kokari su tseratar dashi,don Allah ni bakomai ma in na mut...."yayi saurin rufe mata baki,"ya zaki dinga magana irin wannan,kina wani zancen mutuwa kamar kin daina tausayina?idan kika tafi kika barni  yazanyi"zuwa yanzu dukkaninsu kuka suke wiwi,gashi lokacin shiga yayi dama dan karasa shirye shirye ake shiyasa ma suka samu suna zantawa,"ina Amin"tace dakyar,"suna waje dasu Aunty""kace mata nagode"tace don zuwa yanzu ma an fara tura gadon nata,kasa jurewa yayi ya fashe da kuka,to yanzu idan tamutun fa dagaske ya zaiyi shi?komai fa na iya faruwa?babu abinda yadace yayi yanzu kamar  addua, tubda  dai hakanne kawai  mafita a halin daake ciki.

Cikin sanyin jiki ya fito yanemi  waje,yafara sabon kuka hakan ne yasasu Auntyn tsorata suma,"meya sameta?"suka fara tanbaya duk a tsorace,"bakomai"kawai yake cewa yana girgiza kai,bashi  baki Auntyn tadingayi  tana kwantar  mishi da hankali  amma ita kanta  kukan takeyi,ganin kowa na kuka Shima  Amin yafara nashi dama tun dazu yaketa  tambaya ina take suke ta  cemishi unguwa taje ita suke jira tadawo,su tafi gida,dakyar dai aka samu shi yusuf din yadan tsagaita da nashi kukan  ganin babu mai rarrashin wani,sannan ya tashi yadan fita.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now