RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA
KARSHE
Ko data sanar da Mama abin yamata dadi tabbas,don ko bakomai shi dakanshi yusuf din yadawo kuma yanuna har yanzu yanayi da ita,hakan na nuni dacewar tabbas soyayyarshi agareta ta tsakani da Allah ce,duba da yawan duk irin abubuwan dasuka faru abaya,ko da mama ta labartawa Abba shima yayi murna matuka,donko bakomai fa yusuf mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida da hakan,tun sanda ya auri yarsu kawo yanzu basu taba samun wani labari ba mara dadi,game dashi,duk wanda zaa tambaya halayenshi babu wanda zakaji ya furta wani shirme akanshi saidai ayita yabonshi,hakika irin wayannan kyawawan halayen nashine da kuma nutsuwa sukasa iyayen nata suka sake maraba da abin,amma kuma me?ita fa har yanzu an kasa gane mata kuma abinda suka fuskanta gameda ita ma shine tanafa,son nashi sarai tana kuma son takoma ko don yaronta ma,to amma zuciyarta takasa nutsuwa haka kawai.
Ba abinda iyayen nata suke mata akoda yaushe sai nasiha na ta rungumi kaddararta takuma manta da baya rayuwar kenan,cike take da jarrabawa kala kala,kuma dama komai a rayuwar duniyar nan ai mai wucewa ne babu wani dawammamen lamari,idan tace bazata kara aureba haka zatayita zama abin zai zama babu wanni faida ma kenan,ga sauda ma an fara maganar aure.
Shi kuwa tanashi bangaren,dagaske yake so yake yadawo dakomai yadda yake da,kai fiye ma da da din,don so yake yaga yahada kawunansu idan tashigo sunnzauna lafiya dukda dai yasan Abu batada matsala to amma kuma fa komai na iya chanjawa,jikinshi kuma yakanyi sanyi sau dayawa idan yatuna da rashin bashi ansarshi datayi har yau,gashi ana neman wasu wata biyu kenan dayin zancen,akalla kuma yakai su Amin din wajenta kusan sau Hudu don har yaron ma yafara sabawa da ita dakanshi ma yake cewa akaishi,hakika hakan ba karamin dadi yake mata ba don ayadda tayi tunanin abin da bahaka yazo ba sakamakon addua datakeyi Allah yakawo komai dasauki tunda har yaron ya shaku da ita yadda takeso.
"Toh mudai Allah yasani munyi iya bakin kokarin mu akan wannan lamari,Allah shaida ne ke bazawara ce farida bazamu tasaki agaba ba muce zamu tirsasa ki wai dole saikinyi aure ba,aa,bazamuyi ba amma kuma fa kisani shawarar ma mungaji da baki don mun lura kamar ma batawa kanmu lokaci mukeyi kawai,"cewar Abba,kasancewar yau akazo aka kawo lefen sauda aka kuma saka ranar auren wata hudu masu zuwa,"ni narasa gane irin wannan abu, bafa akanki aka fara irin wannan lamari ba shikenan kuma saboda abu yafaru dake shekara da shekaru,saiki yankewa kanki wani hukunci cen mara amfani?kuma ko bakomai danki ai wani sashe ne naki dayazama dolenki,duk kwanciyar hankalinki agidannan gidan mjjinki yafiye miki ko ina,haba farida ayita zance daya kamar cin kwan makauniya"cewar mama,"yaron nan (yusuf),saibinki yake yana bibiyarki kina watsar da lamuranshi me kikeso farida?wai wannan wace irin rayuwace ?"Abba ya kara,don ahalin yanzu tariga ta dade da fara kuka,don tama rasa meke mata dadi,"Toh nidai nafada miki daga rana mai kamar ta yau nadaina miki zancen aure kiyi duk abinda kikeso"cewar mama tareda tashi zata barwajen,saurin rikota tayi hawaye shabe shabe a fuska,"don Allah don Anbabi kiiyi hakuri,Abba ku yafemin"ta juya gareshi,"wallahi tallahi bansan abinnan yana damunku ba,banida bakinciki duk duniya kamar inganku cikin bacin rai bare kuma ace wai nice sanadi don Allah ku yafemin"ta fashe da kuka,sanyi jikin mana yayi tafara rarrashinta,"Abba ma yana bata baki,"to farida abin nakine mun kasa ganewa, munga bashida ranar karshe kina irin wanan abin ai sai wani ciwon ma yazo ya kamaki"Wallahi na daina, Allah zan koma,zan auri yusuf din"tace cikin kuka wani farinciki sukaji mama ta kalli Abba suka sakarwa juna murmushi,"Allah yamiki albarka yabaku ikon zama lafiya da hakuri da juna"suka dinga cewa.
To masu karatu dahaka dai zamu iya cewa komai yazama tarihi don aranar ma saida yusuf din yazo bayan tace tanason ganinshi inda suka gana suka kuma daidaita hakika shima yayi farin ciki matuka don har ya fara fidda rai ma.
Acikin zantukansu ne yake mata zancen raba gida dukda kuwa gidan yanzun zai ishesu duka amma dai wai shi yana gudun rigima kar azo azauna waje daya asamu matsala yau da gobe tafi karfin wasa,nesa nesan dai kawai,"nayimaka alkawarin zan kasance mai hakuri,zan kuma rike girnana,amma zancen raba gida ka barshi ko don yayanka,banaso kansu ya rabu,amma dai ka tambayi zainab din ita ko tanaso araba,kaga gwara afita hakkinta ai"aduk sanda take magana tanayine cikeda nutsuwa da kamal,hakan neyakesawa ya tsaya yayita kallonta cikeda wata irin kauna mara misaltuwa,don shi ganinta yake kamar an saketa.
