RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA8
Wasu manya manyan robobi irin na tara ruwan nan iya tace adauko daga maajiyarsu akawo tacikasu, don a kalla zasuyi bakwai, tacikasu sarai da ruwan rijiya tunda ba abinda take sai aikin kuka kuma ai baa barta haka ba dole tadan taba wani abu na daga aikin gida tunda dai itamafa matar gida ce kamar sauran,duk matar gida kuwa su a wajensu da bauta aka santa,idan kuna neman mata marasa gata marasa yanci ko kadan a duk fadin duniya to kuzo wannan gari kusha kallo,mace bata sanin dadin rayuwa saita haifi da namiji,shikuma idan yayi aure matan dazai auro su zasu dinga mata hidima,da gidan baki daya,idan kuwa duka yayanta matane tofa babu wannan gatan,tabbas suna cikin wani karni na jahiliyyah kuma wai ahaka an karbi musulumci kwanan nan hmmm,Allah yasa mudace.
tabdi to ita tunda take ma ta taba jan ruwan rijiya ne,kai jamaa to a ina ma zata ganta ma ita kanta rinjiyar dama?,"wallahi tallahi ban iya ba"tace da iyan,cikeda marairaicewa,"baki iya me ba?" Tayi maganar baki bude bayan ta zaro ido,"wai ni wannan yarinya daga wace irin duniya kike ne?"tace cikin fada don gabaki daya halayyarta tasha banban da irin tasu,don dukkanin abubuwanta baki ne su a wajensu,yazama dole asaita ta, adorata ahanya,ace komai bata iya ba?sauran matan ma kowacce binta da kallo tadingayi cikeda mamaki,da bakincikin haushi, don yanzu insunada makiyiya bata wuceta ba,dama sudinma ya aka kare azaman nasu kowacce tana fama da dan kishinta,tunda dai duk inda akace namiji yanada macen data wuce guda daya dole asamu kishi, babu dai yadda zasuyi ne kawai,don haka aladarsu take, dolene miji ya auri mace fiyeda daya,shiyasa ake zaman ana hakuri da kai zuciya nesa kar abatawa miji,don idan mace tabata ran miji su awajensu har takaiga yakai kararta gida wajen iyayenta tofa muguwar shahararriya ce kuma iyayen ma tafi karfinsu kenan,don zasu iya kamar tsine mata zamuce,su fatattaketa, kuma duk danginta babu mai karbarta tunda ta raina miji,(kamar fa sabon Allah suka dauki lamarin)wannan dalilin ne yasa koda wasa mace bata taba bata ran miji,koda kuwa shi mijin yana gasata ne yanakuma yankar naman jikinta yana cinyewa,da dai mutane sukita,a dinga hantararta gwara ta shanye duk irin wulakancin mijin kuwa.
tabe baki suka dinga yi suna tsaki,wato tana nufin rijiyar ma bata sani ba kenan,bakuma ta taba jan ruwa ba,wai ita yar birni,to acen dawane ruwan suke amfani?tab ai kuwa zasu koya mata hankali.
Zama tayi tana rantse rantse,tana koke koke,akan idan fa suka matsa to fa babu tantama zata iya fadawa wallahi,hakan ne yasasu tuntustrewa da dariya don su inda zata fada dinma daya fiye musu,"kofa zaki mutu ne yarinyarnan,saikin debo ruwan nan fa,"iya ta jaddada mata,bayan ta kafa rediyonta a kunne,nuku nuku tacigaba dayi,kafin taji gyaran muryarshi a soro alamun ya dawo kenan,hada ido sukayi da iya tamata irin wannan kallon na kinsan sauran ai tunda ni ban isa dake ba wanda ya isa ya dawo,ko kallonta baiyi bama ya nemi waje kusada uwar tashi yazauna,sauran matan sunata mishi sannu cikeda girmamawa kuwa,"shegu yan iska na tabbata ko iyayen dasuka haifesu basa yiwa wannan ladabin"tace aranta cikeda bakincikinsu,ko aikin uwar me yayi oho mtsw,haka tanufi rijiyar tana tafiya dakyar kamar wadda kwai ya fashewa aciki,sukuma kowa yamaida dubanshi gareta ana jira aga yadda lamura zasu kasance,"meke faruwa ne"ya tambayi iya,labarta mishi duk yadda akayi tayi,hakan ne yasashi kyalkyala dariya,"aa meya faru kuma meyasa kake dariya haka?"cewarta,"iya ba karya take ba bata iya din bane,amma kuma ai kowa da koyo yakan iya"yace bayan yanemi waje ya kishingida,tareda fara bawa iya labarin rayuwar faridan da irin rashe rashen mutumcin data tattapka,hardasu rabuwa da miji don zai mata kishiya,ai kamar jira suke aka fara laantarta ana tsine mata,ayi yare ayi hausa,duk tanaji ita takanta take,suyita magana har bakinsu yacire insunga dama.
Wani tangamemen bokiti tagani da igiya ajiki da alamun dai shine gugar kenan,ita kam ta ina zata iya tsunduma wannan katon abu ya cika ta janyo,ga rijiyar itama irin mai wawakeken bakin nan ce shikenan itakuma tasan tata ta kare, ta tabbata babu makawa saita fada rijiyar nan,tace aranta tareda saddaqarwa ta dauki gugar,sake juyowa tayi jin duk sunyi shiru, taga fa wai itan dai ake kallo aga yadda alamarin zai kasance,wurga gugar tayi tayi saurin ja da baya,ta kankame hannaye,"idan kika bari igiyar nan tafada dukanta, saikin shiga kin ciro",cewar iya cikin fada,ita kuma sakin gugar tayi,don tayi aikinta dakanta taja takoma gefe ta tsaya,"to ni tsoro nakeji,wallahi zan fada"tace cikin muryar kuka,"tareda kama karshen igiyar dasauri, tafara ja daga nesa aikuwa taji mugun nauyi kasancewar bokitin kato,to su wayannan taya akayi suke iya jan wannan katon abin?"tace aranta,tabbas ruwa ya shiga kenan, yacika, tacigaba dajawowa tana haki,cikeda takarkarewa don dukkanin karfinta na duniya tasaka a jawo ruwan nan, saita kusa kawowa bakin ,kusan sau nawa kenan, saita saki don gajiya,saboda nauyi,daya daga cikin yanmatan da iya tanuna mata dazu tace yayanshine,ce takarasa inda take, tanata kallonta cikeda tausayi don ko dazu ma da lamauran suna faruwa idan sun hada ido yarinyar kauda kai take alamun dai abubuwan basa mata dadi don dai babu yadda zatayi ne,ganindai dagaske farida fa bazata iya jawo ruwan nan bane yasa yarinyar karasawa tabarmar iya tareda tsugunnawa cikeda girmamawa yadda suka saba tafara magana,"iya kibarta haka tunda bazata iya ba ni zan d...."ai bata kai aya ba,baban nata ya kwasheta dawani wawan mari da saida ta wuntsila,uwarta na gefe tana murna,tana fatan ya kara mata wani,tunda batada hankali har take neman ta taimaki makiyiyarsu kishiya,"bakida hankali ashe?,iyan tabada umarni shine zaki nuna bata isa ba,to wakika fi tausayi anan?nace har me kika sani dazaki ce zaki tausayawa wata?ko kuwa kinmasan wacece itane?kada in sake gani"ya juya kansauran yaran da matan baki daya "duk ranar daaka sake cewa tayi wani abu (faridan), wani acikinku yanuna wani alamun tausayi,ko da dawasa ne kuwa,ko yace xaiyi wata magana kunsan sauran,"yace cikin fada,"kayi hakuri"shine kawai abinda suka dinga cewa kansu akasa cikeda ladabi, don idan miji yana magana baa hada ido,rashin kunya ne.
