RUWAN DAFA KAI 2

2.2K 166 7
                                        

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA
7

A kasan tayi kwanciyarta don katifar ma kyankyaminta take,ana ganinta ansan yara sunsha fitsarin kwance akai ta tsumu ta tsufa sai wari take.

Bata farka ba sai safiya,gashi har  gari yayi haske,kallon kanta tayi taga duk  kayanta sunyi daka daka,a hanzarce ta mike,don yin  alwala  tunda ta makara,don tsoron lattin sallah take yanzu.

Zama  tayi bayan ta idar,tadinga jero adduoi,tana tuba tana kuma  neman yafiyar ubangiji akan irin abubuwan data aikata abaya,don a halin daake ciki tasan Allah ne kawai gatanta shi zai iya cetonta,babban tashin hankalinta ma yadda zatayi tabar wajen nan,hasalima batama san a inda take ba,haka tacigaba dazama tana ta nazarin rayuwa,don ko yunkurin fitowa ma batayi ba,dukda dai tanajiyo hayaniyar yaran gidan, sunata wasa ana  guje guje.

Alamun zaa shigo dakin dataji ne yasata takurewa waje daya,tareda dukunkunewa cikin hijabinta,shi tagani,fuskar nan babu annuri,hakan neyasata kauda kanta gefe,"ke mutan gida suna cen suna  aiki shine ke kika shantake aciki?uban waye bawanki,to bari kiji mu anan ba haka mukeyi ba ehe,"ya hayayyako,dahar zatayi shiru,sai kuma ta tuno da gargadinshi,"amma dai idan abin tsakani da Allah ne,tayaya zan iya fitowa,bayan ka rufeni,nace  ta ina kake tunanin  zan iya fitowa ko kuwa ni aljana ce dazan bullo ta bango h...."wani wawan  mari ya tsinketa dashi,tadaiji zafin matuka amma ko kukan ma babu sai hawaye kawai don har tafara sabawa,"zaki wuce ko kuwa,wato har kinsamu damar gayawa kutane maganako,nace bakinki ya bude wato"yayi kwafa "atoh dai ki tambayi duk wanda zaki tambaya agidannan  ansan halina indai ta fannin horo ne nayi fice,ya korota waje.

Mata kala kala tasake gani kamar dai na jiya,kowacce da abinda takeyi,wasu suna bakin murhu,masu daka nayi,wasu na shara wasu wanke wanke,sai yara kanana dasuketa wasansu suna guje guje ko ina.
Wata yar dattijuwa tagani kan tabarma a kishingide ta kafa redio a kunne tana sauraro da alamun kowa karkashinta yake kenan dubada kishingidar kasaitar datayi.

Gefe ta nema ta rakube jikin wata bukkar,sukuma sai kallonta ake kamar anga wata halitta ta daban,ana maganganu kasa kasa"waccen dakike gani mahaifiya tace"yamata nuni da dattijuwar,"iya ake cemata"kara kallonta tayi dakyau,taga fa ko dankwali babu akan nata itama, kamar sauran matan tsakar gidan,"mahaifiya"tasake nanatawa aranta,"wai wayannan wane irin mutane ne?","idan kina kaunar kanki da rayuwarki kina kuma kaunar zaman lafiya to fa yazama dole kibi iya kibini don idan kikace zaki dinga  bijire mana wayyo"yayi kwafa hadeda murmushi,"kinsan sauran",wasu hawayene masu zafi suka dinga zubo mata don bataso abinda take zargi  ya tabbata,wayannan wane irin mutane ne wace rayuwa ce wannan,ya Allah a ina nake?tasake cewa aranta,
"wato ina magana shine har yanzu kike nan,babu ko alamun motsawa ko, duk abinda nafada ma abanza kenan?"ya katse mata tunani cikeda, masifa,"to wai mekakeso nayi ne?bacewa kayi nafito ba,kuma  nafito"ta daka mishi tsawa,ai kuwa duka matan wajen, barin abinda sukeyi sukayi,suka fara magana da yare,mai cikeda nuni da cewar abinda tayi,laifi ne gagarumi,masu hararata nayi,masu zaginta nayi dukda dai bajin yaren take ba amma kunsan dai yadda zagi yake ko a ina ne,da anyi shi zaka gane,hatta iya saida ta ajiye radiyonta tadinga dubanta cikeda mamaki baki bude,"ku kuma uban me kuke kallo,?ta hayayyako musu suma,cikin tsiwa don abin ya isheta kuma,ta shaka dayawa,bakin cikin yamata yawa dane zataji?ai  basuyi wata wata ba,suka far mata,aka mata taron dangi,ashe sarai sunajin hausar suma,dukanta suka dingayi yi baji ba gani,saida ya dakatar dasu sannan,duk iya nakan tabarma tana kallon show,itakuma ba abinda take sai kuka duk sun mata bududubu har hijabin ma ya yage,wata kafa  yasake mata aciki,yaran dasuke wasa da sanda ya karbi daya,yafara tsula mata baji ba gani,sauran matan suna cewa yakara mata tunda batada tarbiyya,birgima  tadingayi tana ihu tana neman  ceto amma shiru babu ma wanda yake kallon wajen,kowa ya koma bakin aikinshi banda dariya ma ba abinda suke duk sanda suka juyo suka kalleta,har ita iyan,saima rediyonta  data karo sauti saboda ihun  yana hanata jin abinda take ji.

RUWAN DAFA KAI 2Stories to obsess over. Discover now