RUWAN DAFA KAI 2

1.6K 131 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

19

Yusuf Yana sallah yaji wayarshi na kara alamun shigowar kira,an kira a kalla sau biyar kenan,hakan ne ma  yasa gabanshi yafara faduwa na tunanin ko wani abinne yafaru,dama gashi su Abu  basa nan, yakaisu gidan wata Auntyn shi,Aunty Bilki,irin yanuwan nan,da mutum yake haduwa dasu ko a hadashi dasu  idan yaje wata kasa,tunda sukazo suke zumunci sosai don irin matan nance masu kirki babba ce kwarai da gaske,kimanin shekaru uku dasuka wuce mijinta yayi hatsarin jirgi ya mutu,tun aurenta take a ingila saidai suzo hutu gida najeriya lokaci lokaci yayanta dukkaninsu acen suke wasu sunyi aure wasu basuyi ba a halin daake ciki jikokinta zasuyi kamar hudu haka,hakika tasu tazo daya sosai dasu yusuf din tanasonsu sosai,shiyasa ma suke yawan zuwa gaidata akai akai,da yusuf din yanata tunanin wanda zaa sa yajewa Abun dan Babba dai idanta haihu,tunda dole zata bukati taimako ai,sai Allah ya hadasu da Aunty,damuwarsu takau ta wannan babgaren.
Wannan kenan.

maida hankalinshi yayi kan sallar ya nutsu yana kuma  adduar Allah yasa dai komai lafiya,tunda haihuwar dai ko yau ko gobece.

saida ya idar yayi adduoinshi tukun sannan ya dauko wayar zuciyarshi sai bugawa take dakarfi kamar zata tsaga kirjinshi tafito,ahankali yadan danna don ganin kiran daga waye saidai kuma me zuciyarshi ce tafara harbawa dasauri dasauri ganin numbar data  kikkirashin,"aa wannan numbar  ai number farida ce da ya riga ya  dade da haddaceta ko a tashinshi akayi  daga bacci  zai iya kawota da ka,yace aranshi tareda bata raj afili "wannan,wannan?ko mekuma takeso yanzo oho?"yafara zancen afili"shikenan kuma  Allah ya taimaketa ya bayyanata  zata fara neman masifa yadda tasaba,to ni banida lokacin iskanci da neman magana"yace tareda  jefar da wayar bayan yasata a silent donma karta dameshi,to inba dai neman magana ba meye zata dinga jera mishi kira kamar tabashi ajiya,  mezata cemishi ma mtsw yaja tsaki.
Tareda tashi ya fita yabar wayar adakin.

"Hmm dama nasani,ba lallai bane yataba yafemin gashi inata kiranshi yaki dauka kuma na tabbata yagani,"tafara zancen zuci,tunda dai ita kanta tasan da ita dashi sun dade da haddace numbobin juna,babu yadda zaayi ma yace wai yamanta numbarta daukan ne dai bazaiyi ba kawai,
"to amma ko me zaimiki ai ke kika jawo yanada ikon dazaiki daukan wayarki dubada irin  abubuwan dakika aikata mishi,shi me ma yamiki har yanzu fa baimiiki komai ba, ki lallaba kawai kibi ahankali kicigaba da hakuri kawai"sakon text message tarubuta ta tura mishi kamar haka,"Assalam Alaikum,Barka da warhaka ina fatan kuna nan lafiya,na kikkiraka baka dauka ba watakila ko baka kusa da wayar ne,tunda wayar bata samu ba zanso nayi amfani  da wannan damar wajen baka hakuri dakuma neman yafiya a wajenka dangane da duk irin abubuwan dana aikata maka a baya,don Allah don Annabi yusuf ka yafemin kayi hakuri,hakika na aikata maka abubuwa dayawa dani kaina yanzu tunosu ma basonyi  nake ba saboda yadda nake shiga damuwa don Allah ka manta da baya ka yafemin,kar in mutu da alhakinka akaina,ka turomin numbar zainab itama don dole in bata hakuri,idan kuma hakan bazai samu ba,kace da ita ina mai neman afuwarta don Allah,nagode,ka huta lafiya kagaidamin  Su ita da Amin,ta tura.

Dama bata ma sa ran ganin reply ba amma dai bazata gajiya ba harsai tasamu yace ya yafe mata din tukun.

Baissake bi takan wayar bama sai dare saboda  zaije ya daukosu Abun,"wai to a ina ma tasamu numbata ne mtsw dazata addabebi"yace,ganin uban rubutun data aiko ne yasashi sake jan tsaki,dahar bazai karanta ba zaiyi deleting saidai kuma yadan duba yaga abinda ta rubuto din,yana karantawa yana  jan tsaki don shi aganinshi duk zantukan nan nata bakomai bane illa tsantsar karya,farida cefa?tayaya zaayi ms ya yarda tab,sanin hali,aikin banza to kuma sai akayi yaya ko dama nace na rikeki ne ni azuciyata  bamanida lokacinki"yayi zancen afili tareda zura wayar a aljihu yafice.

Suna zaunevsuna kallo,ita dashi Amin yayi bacci,suka fara dan taba hira yanata tsokanarta akan cikin don har wata kiba tayi,ta cicciko sosai  kamar ba ita ba kayanta duk sun mata kadan amma fa tayi kyauciki kyau yamata ba muni ba tabbas,saura kwana biyu haihuwar a hasashen maaikatan lafiyar asibitin datake zuwa,saboda haka nema suka bada shawarar ta shirya ta tafib tun gobe saboda gudun  kada labour yakamata agida ko cikin dare haka tazo duk kafin aje tabgalabaita,hakan kuwa akayi don ahalin daake ciki ma tariga ta hada kan dukkanin kayayyakin su,itada jaririn dazasu bukata,komai unisex suka siya don sunki yarda aduba mexata haifa din sunce basason susan kome zasu haifa din,duk abinda Allah yabasu karba zasuyi hannu bibbiyu.

"Baby na tun dazu kiketa nuku nuku kina inda inda wai menene?"yace da ita ganin tun dazu fa akwai zance abakinta amma takasa fada,"hmm bakomai"kawai tace tana dan murmushi,"nasan wannan bakoman taki fa,tabbas akwai komai kuwa mai kike boyemin bakyaso in sani ne  yar matata?"yace cikin wasa,"saikamin allawarin idan nafada bazakayi fushi ba"tayi maganar tana yar dariya,"fushi kuma?kema dai to tayaya zaayi zancenki yasani fushi habibty haba ni duk kinma bani kunya""bahaka  bane kawai dai bansan ya zaka dauki zancen bane"hmmm waishi wannan wane irin zancene ne daaketa jamin aji akai haka"yace,gyara zama tayi sannan tasaki  ajiyar zuciya tafara kallonshi,"mine"Naam Abuwa ta"hakan ne yasasu dariya dukansu,"Kakuma isuhu ba"hehehe wato abin hakane kenan"yace yana kara rungumota jikinshi  cikeda shaukin kauna,"eh mana kowa ai yanada sunan gargajiyar" tace,"to naji yanzu dai idan kinaso kisani farinciki kifadi abinda yake ranki  nayi alkawarin bazanyi fushi ba shikenan?"yafadi hakanne ganin  ta dage na bazata fada ba har sai yayi alqawrin rashin fushin nan,"hmmm,inata tunanin Aunty ne wallahi"Tunanin Aunty  kuma?ba dazu kuka rabu ba?Yar dariya  tayi "bafa Anty Bilki ba,Aunty dai nake nufi maman Amin"uhm kinada abin mamaki wato,kina nufin har  yanzu tunanin nata kike kina tausaya mata kenan, bayan ta dade da komawa gaban iyayenta tana jik dadinta,tama riga tamanta dwata  ke aduniya tuntuni amma kinansn bakida zance sai nata ko?to shawarar dazan baki itace ki manta da ita kawai kishiga harkarki  bama nasan kidinga  saka damuwar wasu  aranki ke dakike  dauke da dan  mutum ajikinki"yace,bayan sarai shima bawai daina tunanin nata yayi ba text din data mishi dazu ma ya tsaya mishi  arai,"eh duk nagane amma fa tunanin danake nufi na daban ne,"sai kuma tayi shiru ton tana tunanin yadda zai karbi abin dakuma abinda zai biyo baya,"inajinki  tunanin me kike?"ya katse mata tunani,"dama,dai,to gani nayi idan bazaka damu ba da dai wai kadawo da ita dakinta"koba daki ba?"ya kakkafeta da ido hakan neyasata kasa danata gudun bacin ranshi,"don Allah kayi hakuri idan zancen bai maka dadi ba kuma kai kacefa kayi alkawarin bazakaji haushi ba ko ka manta?"eh ni nace hakan amma karki sake min wannan zancen,babu inda zan dawo da ita haka kawai muna cikin zaman zamanmu aikinkfi kowa sanin halinta,harda wani wai Aunty ke ko wani iri ma bakyaji wato,ke kike rokon wannan tadawo kuyi zaman kishi dakanki, ke wace irin macece,ni sai naga ma kamar dainaji kikayi dani kika kuma daina kishina shiyasa ma harkike tunani  gayyato wata h..." "aa wallahi kawai dai n...."kawai dai me?Karki kara min zancenta,yanzu ma abinda yasa kikaga  banji haushi ba don nayi alkawari ne amma karki kara.

"Toh nadaina Allah ya huci zuciyar mijina"tadan kwanta  ajikinshi,"Amin matata,yakara kudundineta.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now