RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA
3Baidawo ba sai bayan isha,koda ya shigo dinma bawai kai tsaye yaje duba dakin ba,saida yagama duk abubuwan dazaiyi sannan.
Hankalinshi kwance,batareda wata damuwa ko fargaba ba a tattare dashi nawai ko ta mutu ko tana da rai,ko wane hali zaije yasameta,ya nufi dakin ya bude tareda zaro wayarshi daga aljihu ya kunna torch,don haskawa sakamakon duhun daya mamaye ko ina don babu ko fitila bare fanka,Allah yaso ma baa zafi agari sosai don da ta iya rasa numfashi.
Kwance yasameta shame shame itada matacciya babu wani banbanci,sai numfashi datake fiddawa daidai,"uhm kaga yarinya yar gatan Abba"yace cikeda iskancin rashin mutumci yana dariya bayan ya dallare mata fuska,ahankali ta iya dago idanunta dasuka kumbura sukayi ja tana kallonshi,ga dogon gashinta duk ya barbazu ya sauko ya rufe rabin fuskar,"au yau ba tsiwar ba masifar? bazamakice min komai ba wato?"ya hayayyako mata,wasu hawayene masu zafi suka fara zubo mata,ganin babu alamun tausayi a tattaredashi ko kadan,halinda take ciki ma bai dameshi ba wato?,hmm,"don Allah don Annabi kayi hakuri,kabarni na tafi gidanmu"tace dakyar,don maganar ma bata wani fita sosai saboda bakinta ma a kumbure yake ga azaba datakesha,ita kadai tasan me takeji,"wato ke bakya gajiya da bata bakinki kenan? ,har yanzu bazaki shiga taitayinki ba wato,ki kuma nutsu ki rungumi kaddararki ko?"ya kara matsawa kusada ita,kamar zai kai mata duka,ko gezau batayi ba,wai irin tadan jada baya dinann saboda karya daketa,amma inaa bata iya kwakkwaran motsi sakamakon jikinta dayamata nauyi,"idan kika kuskura kika kara zancen in barki ki tafi gidan nan saina datse wannan tsinannaen harshen daya kware a rashin kunya da rashin mutumci matsiyaciya,"hmm tabbas ahalin daake ciki kalamanshi daduk wasu lamura nashi ma sun daina bata mamaki,don ada kallon irin ajebo dinnan take mishi saboda yadda yadinga nuna mata shi ko bakar magana ma bai iya ba bare akaiga zagi,to amma gashi dare daya hallayarshi gabaki daya ta bayyana, to wai ma waye shi?wane irin mutum ne wannan ta aura?(hahaha, haba malama sai yau zaki damu da bincikar wanda kika aura?lokacin daya dace kiyi ai bakiyi ba saida abubuwa suka baci lokaci ya kure miki?aikin gama ai ya gama,dan Adam kenan).
Tsaki yaja cikeda jin haushinta,"ke ni zancen nan ma dakikayi kin jawowa kanki wallahi,abin kirkin danayi niyya na baki abinci ma nafasa tunda har yanzu bakida hankali kina iya furta min hauka shashasha,kici kanki"yamata wata kafa aciki,"kabani ko ruwa ne don Allah"tasake cewa,"kanki akeji kuma"yaja tsaki ya sake jawo kofar hankalinshi kwance ya garkameta yashiga harkarshi.
"Nashiga uku na jawowa kaina,wannan wane irin balai da masifa ne natsunduma kaina aciki da hannuna?wannan wanenirin abune?ina zamnzamana na debo RUWAN DAFA KAIna,"tacigaba da magana afili tana kuka,ga muguwar yunwar dake addabarta don rabonta da abinci tun daren jiya.
Hakika yau ga zancen mama yafito,datace kar ayi saurin yarda da Abdallah har sai anyi bincike mai kyau saboda yadda rayuwa tazama, rashin gaskiya yayi yawa,amma ta kekasa kasa, Abba yana goya mata baya sukakijin zancen nata(maman),"kaicona nasan Abubuwan nan dasuke faruwa dani,harda Alhakin mahaifiyata da yake bina,ita data kasance a kullum batada burin daya wuce naganin mun zama mutanen kirki mun sami abinda yadace damu,aamma nadinga bijirewa umarninta ina bin son zuciyata wayyo Allah na mama ki yafemin" tacigaba da kuka,don ahalin daake ciki in da akwai abinda take bukata ruwa a jallo bai wuce na taga mahaifiyarta ba tanemeta gafara.Ko washegarin ma sai wajen sha daya na safe ya budeta dama bai damu da tayi sallah ba don shima rabonshi dayi ya manta,"kya iya fitowa kije ki gyara jikinki duk kinbi kin cika wuri da wari mtsw,"yace bayan ya bude kofar,"wallahi kigodewa Allah don saa kikaci danaji wani imani ya ratsani naji tausayinki,kuma bawai kinga na budeki ba kice zaki sake min shashanci ko kice zaki yunkurin guduwa,wallahi ko kofa kika kalla saina kasheki"yace da muryarshi mai ban tsoro don ko fuskarshi ma tadaina kalla,don yadaina mata kyau kwata kwata yazamar mata kamar dodo,abin tsoro.
"Zakizo ki taso ki wuce ko kuwa?"ya daka mata tsawa,hakan ne yasa ta mikewa dakyar don tana tsoron karta kara bata lokaci yaji haushinta ya sake rufeta,kamar yadda yafada,gashi har fitsari ma tayi ajikinta,tayi iyaka bakin kokarin ta wajen ganin ta rike amma inaaa,dole ta sakeshi taji dadi,yana bakin kofar babu abinda yake sai tsaki,tana jan kafa dakyar tafito yana biye da ita,yana fadar magnagnun cin mutumci yana zaginta,tana hawaye ba damar magana,dakyar dai ta karasa dakin tana kakkama bango.
Bandaki taje zata shiga ya bita,har zatayi magana,taga yazaro wata yar wuka daga aljihu,daga ganinta zatayi kaifi don har kyalli take tana sheki,hakan ne yasata shiru,tafara nufar famfo don shan ruwa,baiyi yunkurin hanata ba,saida tasha iya shanta,sannan tafara cire kayan jikinta yana kare mata kallo,yanemi toilet seat yayi zamanshi, yacigaba da maganganu,wanda rabin maganar zagi ne dacin mutumci,itadai ba abinda take sai hawaye cikeda nadama da danasani tana gudanar da lamuranta,"dallah cen malama kiyi maza ki wanke jikinnan dakyau,bawai don kiganni azaune ba kizata lokaci ne dani,dakikiya,"cigaba da abinda take tayi batareda tace dashi uffan ba,"wato ga banza yana magana ko?shine zaki nemi ki maidani dan iska?wallahi taraki nake idan nasake magana kikamin banza saina c.....ke!"kayi hakuri"tace cikin kasa kasa da murya.
Haka tagama wankan tanufi sink donyin alwala ko ta samu tayi sallah Allah yaji kanta ya tausaya mata tasamu sassauci,"ke mike shirin yine haka?"ya daka mata tsawa,take ta razana tafara karkarwa,"al....wa...l"eh,lallai sabon salon iskanci yaushe kika fara damuwa da sallah?"ya hayyako mata kamar zai cinyeta,ai saita fashe da kuka,"don Allah kayi hakuri"tace tana kare fuskarta,don indai marine fuskar nan tashashi ta gode Allah daga jiya zuwa yau,"nace yaushe kika fara damuwa da sallah munafuka,zaki wuce ko saina hada kanki da bangon nan algunguma"babu damar magana tanaji tana gani ya hana alwalar ya tasota agaba,dresser tanufa simi simi ta dauki spray ta dan fesa,tana datar kallonshi ta mudubi,dataga zasu hada ido saita kalli kasa,komai tsoron yi take tana dardar gudun laifi,zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsoronshi,mai tadauka zata fara shafawa ya sake daka mata tsawa don rabonda yamata magana ahankali ta manta,"wannan bashida wani amfani a yanzu, maza zo ki haye gadon nan"yamata nuni da gadon,bare baki tayi tafara kuka kamar wata yarinya yar shekara uku daaka kwacewa abu,hakanne yasashi kyalkyalewa da wata muguwar dariyar mugunta har yana rike ciki,"yariska har yanzu bakisanni kowaye ba ko?shashasha"yayi maganar yana cire belt dinshi,"zaki karaso kosainazo?"ai jiki na rawa dasauri ta karasa ta haye gadon,don gudun kada jikinta ya gaya mata,dama ba kaya.
A haukace yashiga gudanar da lamura kamar koda yaushe,yadda yaga dama kuma yakeso,babu wani sasauci,bare tausayi,ko dubada irin halinda take ciki baiyi ba.
Saida ya kammala sannan ya mike yamaida kayanshi don dama babu zancen wanka tunda bai damu ba yafice daga dakin tanaji ya garkameta.Wani irin ihun tafasa,dukda tasan babu wani amfani babu maijinta,amma bakincikin datake ciki yamata yawa,ji take kamar mutuwa ce zata zama hutu agareta ahalin daake ciki,kuka take babu kakkautawa cikeda nadamar aurenshi datayi dakuma irin abubuwan data aikata abaya,don tabbas ahalin daake ciki rayuwarta batada wani amfani,ashe dama haka na iya faruwa agaske kenan,daake cewa duk abinda mutum ya shuka shi zai girba,?idan Allhairi mutum ya aikata zai gani,haka zalika idan sharri ne dason zuciya zai gani,wannan lamarin datake ciki,abune dabata taba tsammani ba arayuwarya ko amafarkinta,ga yusuf shima tasan hadda hakkinshi ne yake bibiyarta,agaskiya babu wanda zata iya cewa ya cuceta sai kanta dakuma mahaifinta tunda shine yake biyewa duk wani shashancinsu tunda aka haifesu,gashi su duk wani abu mara kyau idan sunyi baya nunawa sunyi ba daidai ba,komai daidai sukeyi kuma basa laifi,mama datake dagewa suke ganin kamar takura musu take ashe tafisu hangen nesa takuma fi kaunarsu,"nashiga uku,innalillahi wa inna ilaihi rajiun,ni yanzu ya zanyi"tadinga zantuka a fili wayanda suke kunshe da tsantsar nadama da dana sani,aduk sanda tatuno maganganunshi kuma wani kukan take sake fashewa dashi.
Ganin kwanciyar haka bazata amfana mata komai bane yasata tashi tasake shiga bandakin don yin wanka sannan tayo alwala.
Dama yazaayi masifu suki samunta arayuwa,duba da yadda take wasa da ibada, ko akan auren nan babu yadda mama batayi da ita ba akan tayi istikhara tanemi zabin Allah,tunda ta dage amma taki kememe saboda cin burin datayi na kuntatawa wasu,da biyewa sharrin zuciya"ya Allah...."sai takasa karasa abinda tayi niyyar fada sakamakon kuka dayaci karfinta.
yar doguwar riga tadauko,tazura tasaka hijabinta ta tada sallah,tana zaune tana adduoi da tunanin abubuwan dazata tarar nan gabane ta tuno batasha maganinta ba,wani sabon kukan tasake fashewa dashi,arikice ta tashi ta dauko shi daga maboyar datake ajiyeshi don karya gani,ta hadiya,(tanashan maganin ne don gudun kada mai afkuwa ta afku,don tunda sukayi aure duk sanda ya kusanceta saita sha kwayar ta hana daukan ciki,don dama babu zancen haihuwa dashi a tsarinta,don idan tace duk namijin dazata aura saita haihu dashi ai da matsala dukda ma dai yanzu ba wannan bane agabanta,burinta baiwuce na taga tafita daga wannan mummuna bakin gidan ba,amma dai bazatayi sakaci ba ta bari ciki yashiga tsakaninta da wannan azzalumin).Karkumanta kuyi voting,commenting,😍
Nagode