RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA16
Kafin kuce meye wannan kuwa labarin ganota daakayi ya bazu ko koina duk kafafen yada labarai sun baza,damasu ji mata dadi,ana gode Allah ana sanbarka da bayyanata dayayi, bata mutu ba damasu Allah ya kara gobe ma takuma wannan darasine gaduk masu hali irin nata, Allah sarki rayuwa kenan, inda sunsan abinda tagani dakuma irin halinda ta tsinci kanta a ciki dabasu dinga fadar abinda suke fada ba to amma kuma dan Adam da bakinshi ahanashi magana ne ko bayyana raayinshi?ai hakan bazai ma yiwu ba.
Amma dai har yanzu hotunanta ne baa saka ba,Su Abba sunce aa,a jinkirta babban abu mai muhimmanci dai shine anganta da ranta to a tsaya a haka,saboda lamarin ganin nata ma babu yadda baiyi ba akan adan sakaya shi zuwa wani dan lokaci to amma hakan bazai yiwuba saboda sauran yansanda na cen gida da jamau dasuka tashi tsaye suna faman nemanta,anata addua,baji ba gani to dole a sanar dasu labarin mai dadi ko a samu hankalin kowa ya kwanta.
A irin sanarwar daakeyi ne ma suma su yusuf suka sami labari,Abu sai murna take kamar wata kanwar uwarta aka gano,don kusan kullum sai tayi zancenta saboda ita wallahi tausayi take bata,"saiki zuba ruwa akasa kisha ai,karewar farinciki kenan"shine kawai abinda yake cewa akoda yaushe,tun tana bashi haushi ma harta daina,kawai idan ya kalleta yaga yadda take wannan farincikin da annushuwa mamakine ma shi yake kamashi,ita wannan wace irin yarinyace ne,tsohuwar matar mijinki ce fa ake magana,bayan ke kanki ba kyaleki tayi ba,amma shine har kin manta da komai,duk kikabi kika wani damu da wani batanta haka hmm,tabbas halayyarta ta dababance.
A ranar da Hajiyar yusuf tasami labari saida taje har gida wajensu maman don yin fatan alkhairi donko sanda labarin batan ya risketa ma saida taje jaje,inda Abba yadinga bata hakuri akan duk irin abubuwan dasuka faru abaya,babu komai ai komai ya wuce shine kawai abinda tadinga cewa,tunda dai don an rabu ai bawai yana nufin kuma shikenan an yanke duk wata alaka ba,haba meyasa ne mu mutane bazamu gane darajar yafiya ba,don Allah adinga yafiya ana mantawa da baya,saboda daga Hajiyar harsu maman sunsandai kome zai faru fa babu yadda zasuyi da juna tunda dai aure ne yahada komai kuma ko bakomai akwai rabo a tsakani.
Ko data fadawa yusuf dinma taje jaje a lokacin ranshi baiso ba,don dai babu yadda zaiyi ne,don shifa tanashi bangaren yariga yagama da lamarinsu gabaki daya,baiga dalilin dazaisa koda yana nan dinma yawani je ba ko ya kira waya kamar Yadda Hajiyar tace,ita dai akoda yaushe babu abinda take ce mishi sai yayi hakuri,zaman duniya babu tabbas,yabi komai ahankali,yau in mune gobe bamu bane,kuma duk wanda yace zaiyi hakuri,bazai taba faduwa ba ko yaga badaidaiba da izinin Allah,shine dai zancenta a gareshi kullum.Washegari su mama suka karasa cen congon,kuma dai kunsan abinda zai faru dazarar sun ganta,ai dukansu kuka suka saka,cikeda tsananin tausayinta,don kamar yadda nafada muku ne ai abaya,karyar mutum mai imani yaganta yaki zubda hawaye,kukan nasu ne yasa maaikatan asibitin suka fitar dasu daga dakin.
Anata kara mata ruwa ba kakkautawa, gashi batason cin abinci,har yanzu batayi wata kwakwarar magana ba,saidai tayi murmushi kawai ko hawaye.
Hakika hoton da Abba ya tura nusu Rahma ne ashe akan ido da ido,tabbas lamarin ya shallake tunanin duk wani mai tunani.Acen police station kuwa anata fafatawa da wancen dan iskan,abinda Abba yasasu yansandan su tambayeshi shi suketa tambaya,nacewar yafadi dalilin dayasa yayi abinda yayi,dakuma ribar dayayi shirin samu gameda hakan,sai kuma uwartashi itama tafadi nata dalilin nakin sashi ya maidata datayi dukda kuwa tasan cewar bada izinin su ba(su ABBA),ya daukotan,amma inaaa juyin duniyar nan yaki bada ansa,wai shi mara mutumci, aikuwa dai yanacin duka amma kuma dukda haka bakinshi yaki mutuwa don har cewa yake ai shi aka ma ciwa mutumci aka kuma raina, shi yakamata ma ya kulle mutane,shi daake je har gida aka daukar mishi mata batareda izininshi ba,wane raini ne yakai wannan?,"oh to,mahaifin nata daya haifeta yaje ya ceto yarshi kana neman kasheta shine har kake zancen iko?kai waye?laifukanka fa kara karuwa suke,kacigaba"cewar su,"kunfi kowa sanin ai ni mijinta ne kuma bafi kowa iko da ita mtsw"yacigaba,kai da abu dai yayi abu suka lura dacewar shifa baisan mutumci ba,ga taurin kan masifa, duka kawai yake sha duk sun fasa mishi jiki iya na gefe tana kuka,tanata rarrashinshi akan yayi shiru ko sa daina dukanshi amma yaki yace ai akan gaskiyarshi yake.
su kuma dukanshi suke babu kakkautawa,itadai iya tabada tata ansar tuni,tace batasan wace riba zata samu ba,amma yakamata sugane cewar ai matarshi ce yanada iko da ita,wannan bama zance bane daya kamata adinga tsawaitashi su cen wajensu namiji shine mai yanci,duk yadda aladar kauyen nasu da jahilce jahilcen dasuke tapkawa dai takwashe tas ta zayyane musu,"iya meyasa kike basu ansa,ki kyalesu ki daina batawa kanki lokaci karsu yarda din"shine abinda yake cewa duk sanda tayi magana,"wai kina nufin irin rayuwar dakukeyi kenan a wannen wajen (kauyen nasu)?ku wato ma awata duniya kuke ta daban ko?mutane suna nan ko ina an cigaba zamani yazo amma kuna cen a dunkufe kuna jahilci"ba jahilci muke ba,haka dai muka saba tun kakanni da kakanni,kai yaro karfa ku nemi kumin rashin k........."jikinki fa zai gaya miki don mun riga mun fuskanci dukkanin halayen wannan dan iskan dan naki ba tsinta yayi ba a nono yasha,bawai wani tsufa ne dake cen ba dazaa ce kin wuce duka tsab jikknki zai gaya miki yakamata ki nutsu,ko kuwa don kinga tun dazu kina fadar abinda kika ga dama muna miki shiru?to mun zata kinada hankaline shiyasa muke binki sannu ahankali,to ashe kuskure mukayi"cewar wani officer,"laaa"tace baki bude cikeda mamaki wai yan yara kanana sun sata gaba suna mata rashin kunya"kanaji fa wai ni zasu daka,yau ina ganin abu"tace tareda dora hannu aka,"wani ya tabaki cikinsu mana yaga abinda zanyi"yabata rai cikeda masifa da balai wai shi mai uwa,saboda tsananin rashin kunya,dukan dayafi wanda suke mishi da suka farayi saboda yadda suka fuskanci bashida mutumci,kuma sunsha alwashin sai sunyi maganinshi,duk kurin dayakeyi yamanta hannunshi da kafarshi duk adaure suke,iya dai ta rissina sai bada hakuri take tunda taga abin yafi karfinta,ganindai ba daina dukan nashi zasuyi bane yasa tafara ihu tana kuka,"ku chanja mata cell"wani ogansu yace, ai kuwa babu bata lokaci suka jata aka kaita wani a cen ciki,tana kuka tana rokonsu tana bada hakuri kar arabata da danta suka rufota suka juyo abinsu.
Haka dai aka cigaba da jinyar farida, kullum ana dan samun cigaba amma har yanzu dai batabar firgitar nan ba idan tana bacci hakan kuwa ba karamin tada musu da hankali yake ba,amma dai suna iyakar kokarinsu wajen mata addua
A halin daake ciki dai jira ake tadan kara samun sauki ta warware saboda shiga kotu don Abba har ya shigar da kara, yace sai anbiwa yarshi hakkinta,bazai yiwu ba ace andan saka wancen dan iskan a bayan kanta nawani dan lokaci an sakeshi,shikenan,wato baima horu ba kenan an bashi damar zuwa yasake aikata hakan,inaaa bazaayi wannan lalatar dashi ba,(Abba)wallahi yama rantse bazaici bulus ba,sai an hukunta shi daidai da abinda ya aikata,yadda abin zai zamto misali dakuma darasi ga masu irin halayyarshi ko masu shirin aikata irin haka.