RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA28
"Hmm lallai,dan Adam,babu na yadda,rayuwar nan h...."mine don Allah don Annabi kaci abincinka, tunda muka zauna fa kake nanata zance daya gashi duk ya gama hucewa ma"cewar Abu cikeda damuwa don Abin yana neman ya shallake hankalinta kuma tun dazu daya gama waya yake sambatu,dayayi shiru sai ya cigaba,yanzu haka yazauna ma ya nutsu yaci abincin abin ya gagara babu abinda yake tunani,sai wannan zance daya daure mishi kai tabbas babu yadda zaayi yabari ayi wannan auren,kuwa saidai wani ikon Allah,don ahalin daake ciki yasan bash bazai saurareshi ba,Amma tunda yana matukar ganin girman Hajiya ita zai kira yasanar da ita komai akan ta kira bash din tamai nasiha,akan Wannaan abun dabai kamata ba dayake shirin aikatawa(shi bash din),"nice one"yace afili cikeda jin dadi,don tunda yaji zancen nan kawo yanzu hankalinshi baikwanta ba kamar yadda yasamu sauki yanzu dayayi wannan tunanin,haba da kanshi yawani kulle?,ga hanya mafi sauki,yasan babu yadda zaayi hajiya tasaka baki bash yace bazai janye zancen nan ba sai dai kuma idan itama zaiki jin zancen nata ne,"to wai duk dakake wannan abin idan yafasa auren nata kai zaka aureta ne?"wata zuciyar tace dashi,"anya kuwa zan wani aureta,ta auri kowa dai banda bash shine kawai"yasake cewa aran nashi tareda sakin murmushi Afili,yadauki cokali yafara cin abincin,itadai Abu tanata kallon ikon Allah,hmmm.
Adaren yaso kiran Hajiya amma daya tunofa lokacin ba daya ba,sai ya fasa don watakila bacci ma take kuma bazaiso yakira ya tasheta ba,ta wani bangaren kuma haka kawai yakejin nishadi muryar farida nayi mishi yawo akai,to meyasa ma yake wani farinciki gameda hakan,bayan ba damuwa yayi da ita ba,ganin baccin ya gagareshi ne yasa yatashi yayi alwala yazo yafara gudanar da salloli tareda neman zabin Allah daya idar.
Bayan ya kira Hajiya sun gaisa ne ya zayyane mata duk yadda abin ya faru,"Shi Bashir dinne ya gaya maka haka ko kuwa ya abin yake"Eh wallahi shi yafadamin dabakinshi itama kuma tafadamin dabakinta don bama sako na tura ba kiranta nayi mukayai magana"ya kara,"kunyi maganar da ita kenan,to mashaallah,nikuwa sai nake ganin fa kamar wannan bawani abin tada ahankali bane ai"Kamar yafa hajiya"yace har muryarshi na rawa,"eh mana,menene abin tada hankali aciki haka,don amininka yace zai auri tsohuwar matar ka dakai kace bazaka iya maidata ba,yusuf kwana biyun nan fa bana gane ka yaushe kazama haka ne bansanka da kyashi ba da bakin ciki fa"wani tas zuciyarshi ta bada kardai hajiya na nufin bazata saka baki ba alamarin nan,amma yazama dole ya ganar da ita iyakar iyawarshi,don ya fuskanci kamar gane lamarin ne batayi ba,"Bahaka nake nufi ba Hajiya,abinda nakeso ki gane shine Bashir fa aminina ne kowa yasan da haka,to indai ba ya shirya cin amanar abota ba tayaya zaayi ace macen dana saki kuma bayan duk yasan yadda abubuwan suka faru kuma wai yadawo yace ita zai aura kiduba lamarin fa kigani,kuma ma bayan wannan mutanen duniya tayaya zasu kalli abin haba,don Alalh don Annabi kisa baki tunda ni ya rainani,"yace a marairaice,yar dariya tayi afili yadda bazaiji ba don tariga ta fuskanci inda zancen ya dosa,duk yadda akayi akwai lauje cikin nadi,"ni yanzu mekakeso nayi wai?"ta sake jefo mishi tambaya,"kice ya fasa aurenta kawai,idan auren ne ya damu yayi ya nemi wata,ko kuma idan taimakon dayake ikirari na gaskene dahar yake zancen bazai iya jurar ganin ina wulakantata ba,to yaje ya nemi wata bazawarar ai ga zawarawa nan cike agari"yusuf kasan mekakace cewa kuwa?"ta katseshi,"ni zan kira bashir in gaya mai wanann shashancin?",baki bude ya tsaya yana jinta,cikeda mamaki,"kamar fa goyon bayan abinnan take ma kenan?"yace aranshi,"ni abinda nakeso kagane shine shifa wannan abu dake shirin faruwa(auren)bafa haramun bane,to akan me zan hana yusuf,so kake in haramta halal kawai saboda kada ranka ya sosu?Bashir dinnan fa dana ne shima,ka duba lamarin nan mana dakyau,kuma ma duk ba wannan bama idan yace yafasa din kai zaka aureta kenan ko?"shiru yayi kamar baiji ba,"naam"yasake maimaitawa,abinda tafada tasake fada,"Ni wallahi ko bazan aureta ba kawai dai inga baayi abinnan ba don Allah don Annabi Hajiya ki taimakeni wallahi ina cikin wani hali"ikon Allah,ni na taba ganin abu irin wannan?,bakin ciki kiri kiri,kai kace bazaka aureta ba kuma wani zai aureta zaka hana bayan sarai itama ta aminta dashi,kacire wannan tunanin daga zuciyarka fa,"hmmm Hajiya dai na nufin bazata taimakeshi ba ko?to shi zaiyi komai da kanshi"yace aranshi,"kana jina dai ko?nace ka zauna ka nutsu kabar wannan zance,banaso ma nasake jin ka tada shi,abu ko dadin ji ma babu,kagaida iyalin"Ta kashe wayarta"wannan yaron yaushe ya koyi taurin kai ne haka?kanason mace amma wai kaki yarda,ka dawo da ita dukda dai ansan dole kaji tsoro dubada irin halayenta na baya to amma ai ta chanja?kuma ma saboda son kai yanzu amininka yace zai aureta shine zaka tada hankali wato wai kai mai kishi ko?,"tayi dan murmushi,sannan tadauki waya tafara kiran bashir din don jin takamaimai wai ya,abin yakene,bayan sun gaisa ne take tambayarshi,inda yashiga mata bayanin komai kuwa,bai rage ba bai kuma kara ba,yar dariya tayi sannan takwashe mishi duk yadda sukayi dashi awaya yanzu,shima bash din dariyar yasa,cikeda mamakin yusuf din,"ni dama nasan da walakin ai,kyaleshi ba ya tsaya jan aji ba,"tace,"ai Hajiya na rasa ta inda zan bullowa lamarin ne wanann ce kawai mafita ta karshe shiyasa, nayi nasihar nayi fadan amma a banza"ya kara,"Tabbas kai amini ne na kwarai daka damu da shi haka,Allah yakaro karfin zumunci,kucigaba da wanashi har sai ya dawo kan hanya tunda yadainajin shawara"tace,dahaka dai sukayi sallma.
"Hmmm Hajiyar dayake takama da ita zatayi ruwa tayi tsaki,akan lamarin,gashi ta watsa mishi kasa mai tsakuwa makuwa a idanunshi,hmmm bakomai zai dau mataki dakanshi, don wannan aure indai akaga ya faru saidai wani kadari na ubangiji, amma daranshi da lafiyarshi bazai bari ba kai idan takama ma yakoma Nigeriar,daaketa rokonshi yadawo yaki saiya koma indai zai cimma burinshi.
