RUWAN DAFA KAI 2

2K 158 4
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

9

Dakyar ta iya cika roba daya cikin robobi rututun daakace ta cika,saboda tariga takai makura wajen gajiya Allah yasani bazata iya ba,bayanta har ya rankwafa,hakan ne yasata ajiye gugar tanemi waje tayi dirshen,tana jiran hukuncin dazaa yanke mata,su kansu sunsan da gajiya shiyasa babu wanda ya kulata aka kyaleta ta dan huta.
,ganin hutun nata kuma yana shallake hankaline yasa shi hayayyako mata,"wai wannan wane irin iskanci ne,ansaki abu tun safe, kiyi da jiki bzakiyi ba awa nawa kina abu daya? ke!zanfa...."sai kuma yayi shiru, iya ko uffan batace ba tunda dai yananan yamata maganinta tunda batajin maganarta ita bata isa tagaya maga taji ba,"wallahi,wallahi nagaji kuma yunwa nakeji babu abinda naci fa ga rana"tace batareda ta kallaeshi ba,"ke ni kike gayawa haka,yunwa kike ji kin gaji?to an gaya miki agidannan indai banci ba anaci ne,ko kinga sanda naci ne ni?"yasake cewa cikin fada,matan bakin murhun tasake kalla ta galla musu harara,tunda aikinsu kenan duk sanda suka kalleta suma,"ko uwarsu suke dafawa oho,wannan girkin dai ko tsakuwa ce ai yaci ace yanzu ta rissina tayi laushi,amma shiru bayan ko ita tunda ta fito tagansu a wajen,ko kuwa wani naui ne na nasu irin abincin oho?tace aranta,"nace ko yaran nan basu isa suci ba sainaci bare wata banza ke"kus tayi tacigaba da kallon kasa,"to ni ina ruwana,yayanka ne ai banawasu ba,namasan tun sanda ka tashi ne?ko kuwa ba yanzu ka fita ka dawo ba wayasan ina kaje ko me kaci a wajen?mugu azzalumi,daallah dubeshi wai wannan ne zai zauna jira har sai sanda aka gama wannan girkin mtsw""tace cikin kunkuni murya kasa kasa,don indai ba shiga bakinta zaayi ba alokacin babu wanda zai iya cewa ga wai takamaimai abinda take cewa,anadai ganin bakinta na motsi amma baasan metake cewa ba,"daga dukkanin alamu yarinyar nan zaginshi take kenan tana fadar maganganu"yace aranshi cikeda haushinta,"zaginka take fa yarinyar nan,ko bakaga yadda idanunta suka chanja kala ba,kuma kana zaune kana kallonta ko?wai yaushe ka zama hakane? ,"cewar iya"hmmm naganta ai iya banaso ne in kasheta tun yanzu shiyasa, amma da idan nafara dukanta ko,hmm saidai adauki gawarta"yace tareda nufar wata bishiya a tsakar gidan cikin zafin nama yafara kokarin karyo reshe iya na sake tunzurashi,ai tana ganin haka ta runtuma aguje tayi hanyar dataga ya fita yakuma shigo dazu,dama tun dazun take hararar kofar tana so ta fakaici ido,taje taga meye,amma dama bata samu ba.

saidai kuma me tana shiga soron wani mugun duhu ne dako tafin hannu baa iya gani hakan neyasata cigaba da gudun wai don dai karta karaya saboda taci alwashin saita ga abinda ya turewa buzu nadi,wai wannan wane irin sorone kwanoni kawai take sha,kuma babu haske,ai sanda ta fara hangen haske wasu hawayen farinciki ne suka fara zubo mata batareda saninta ba,donko bakomai dai tasan ta kubuta,ai wato wasu karnika ne narka narka suka bullo tawani daki,suka tare hanyar,da alamun sakosu akayi,ganin sun tsaya cak basu biyo tabbane yasata tsayawa cak itama,wani zabgegen mutum ne yafito daga dakin fuskar nan tashi babu hasken annuri,hannunshi rikeda igiyoyin daaka sakalawa karnukan,don da asake suke babu makawa sai sun gama mata aiki,tsab zasu cinyeta wayannan,duba da irin girman hakoransu dakuma kaifinsu,yare yafara mata wanda bata gane abinda yake nufi ba amma dai kamar tambayarta yake ina zata,kuka kawai tafashe dashi,ganin dai ba fahimta take bane yanata bata lokacinshi yana magana yasashi juya harshe zuwa hausha,"ina zaki nace?"yadaka mata tsawa,"gida"kawai ta iya cewa,jikinta ya dau bari tana karkarwa,tsaki taga yaja yana kokarin kunto karnikan sugama mata aiki,gawani gurnanindasuka fara suna haushi sunga nama,zasuci yar fara,ai babu wanda ya bata shawarar wai ga abinda yakamata tayi,tasake juyowa ta runtumo aguje,tana kuka tafado cikin gidan cikeda tsoro,tana waige waige,tana shigowa kowa ya kece da dariya,harda yaran don dama ba wanda ma yabita ansan zata dawo dakanta,ko suma yaran don bata kula bane tun dazu duk wasansu da guje gujensu iyakarsu tsakar gidan babu wanda yayi hanyar wannan soron,kuma ma wai tana mace ina zata?su ai a tsarin garin da kuma aladarsu mata basa fita,to ina zasu?idan kuwa zaa fita to fa dole tare ake fita duka, mai gida yashige gaba,yayi jagora,haka akeyi.
Kallonta kawai yadingayi yana dariyar mugunta don dariya take bashi inda tasan a inda take data ma daina wahalar dakanta wajen ganin ta gudu.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now