4

1.6K 44 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
      MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)

page 16 to 20

.......aguje  suka karasa shiga cikin d'akin, kowannensu na rige rigen isa inda take zaune dafe   da kirjinta tana cigaba da tari tamkar ranta zai bar gangar jikinta, da sauri fu'ad ya haye saman gadon ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta yana kiran "sorry baby!!!

yayinda gabadaya ilahirin jikin me'ad ya d'auki rawa  "tarasa me ma zatayi ,sai sambatu take "me kuma ya sameki baby nah ?
"some one should help me plz "wa meye hk ne.. ..?

zagayowa tayi dayan gefen  ta haye gadon tana  maimaita "me yasa meki baby nah ?"dan girman allah ki sausautawa zuciyarmu bazamu iya jure kallonki cikin wannan tashin hankali ba. "ya ubangijin ka taimakeni kabawa yarinyata lafiya tayi rayuwa kmr sauran yara.

NASREEN tayi tari da karfi tare da cewa "da..dady wa...water..

a matukar  firgice yace  " watare me'ad give me water plz .....

me'ad wace ta sake rikicewa tace uhmmm water ?

"dan Allah malam kije ki kawo min ruwa yanzu yayi maganar a fusace .. "sorry honey, ta  duro daga kan gadon  ta tsaya sanya takalmanta .

"a fusace yace run now.

" i am runing "im runing  !!

ta bud'e kofar da karfi ta fice batare da ta tsaya rufo kofar ba.

"ahankali fu'ad yashiga jijiga NASREEN "sorry my baby  ,"Inshaallahu zakiji sauki,yashiga shafa kirjinta yana  dubanta.

da matsiyacin gudu me'ad tashige kitchen, madadin ta bud'e fridge  ta d'auko ruwa kmr yadda ta shigo da niyyar yin hk, sai kawai ta hau zariya acikin kitchen din tana zagaye kayayyakin amfani tsabar rud'ewar datayi..
da kyar Allah ya taimaka tasamu ta bud'e kitchen cabinet ta d'auki cup sannan cikin sauri ta dawo ta bud'e fridge ta d'auki robar ruwa nestly water ta fito da mugun sauri .

NASREEN  kuwa tarin datake sai gaba yake, gbdy ta kamkame  ajikin dad dinta, tana tari babu kaukautawa abun gwanin ban tausayi, jikin fu'ad  na rawa yace  "kiyi sauri mana kin ... bai karasa  ba, sai gata ta  shigo  d'akin da sauri , ta mike masa cup dake cike da ruwa, ya amsa ya kai daidai bakin NASREEN "sorry baby take some  water kinji, NASREEN  tasoma kur'ban ruwan ahankali ahankali. .

me'ad ta zauna  tare da raku'bewa  agefen fu'ad tana duban yadda yarinyarta tasoma galabaita  .

NASREEN tasha ruwa  kad'an tana sake yin tari "sorry my baby "ki d'an kara shan ruwan  kiji, inji cewar fu'ad still tana makale ajikinsa .

jiki a sanyaye me'ad" tace sannu baby nah Allah yabaki lfy, sai da fu'ad ya tabbatar data sha ruwan sosai sannan ya tambayata "ruwan ya isheki ?
ta d'aga masa kai ala'mun  eh sannan ya mikewa me'ad cup din batare daya kalli inda take ruku'be ajikinsa ba .

ya rungume diyarsa tsam ajikinsa ,yana shafa mata baya yana sake yi mata sannu , itama me'ad kwantowa sosai tayi jikinsa  tare da d'aura hannuta a jikin NASREEN  tana mata sannu, banda sautin sannun da suke mata baka jin sautin komai a d'akin ,gabadaya hankalinsu da natsuwarsu yabar gangar jikinsu ,ya tattara ne  ga tilon diysrsu ,kowanen daga cikinsu ya kasa d'aukar ciwon nata da sauki, ciwon NASREEN a zuciyarsu  yake , sai dai dukkaninsu sun kasa aiwatar da abinda likita ya fad'a musu akan  nuna wa yarinyar soyayya da kulawa har ma da bata natsuwar zuciya shine zai sa tasamun cikakkiyar lafiyarta .

'YANCINKIWhere stories live. Discover now