38

1.1K 17 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~
*MARYAM ALHASSAN       D'AN'IYA  (MAR'OB)*

page 87

......da sanyi jiki ya matsota sosai kmr zai shige cikin jikinta ,Dan har suna iya jiyo numfashin junansu, da yadda zuciyoyinsu ke bugawa da matsanancin karfin gaske .

hannunsa daya ya kai kan nata  hannun yana k'ok'arin zare hannunsa dake cikin nata , domin isa ga bakin kofar da  har lokacin ake  kan bugawa da karfin gaske ana kiran sunanta.
muryarta  cike da rud'ani da matsanancin kuka tace "Dan...dan  girman Allah abban nasreen karka min haka ,kar ka bud'e kofar nan if possible ma ka bari ni na bud'e ,kai kuma ka samu guri ka 'buya Dan kwata kwata  banason dady ya ganmu tare  .... ta k'arasa mgnr wasu zafafan hawaye na gangarowa saman kuncinta...

Wani irin duba yayi mata mai d'auke da tambayoyi iri iri sannan yace "No no me'ad!!  It can be possible na boye ,at where ?
"No bazan iya ba wallahi ,"ba zan iya wannan lusarancin ba , kamar wani kwarto ko mara gasky zan hiding din kaina "a ina kike tunanin zan buyavacikin dakin nan ?

  "ai ni nama fi son muyi harba dashi ,muyi ido da ido da dady ,so that zai  sake fahimtar raba tsakanin me'ad da fu'ad ba Abu ne mai sauki ba .....
Kuka take sosai har da shesheka jikinta na wani irin rawa ,gabadaya tausayinta ya rufesa , Dan hk Hanky ya ciro daga cikin aljihun wandosa yashiga goge mata fuskarta dake kwararar da hawayen daya rasa dalilin zubarsu sannan  ya kawar da fuskarsa yana kallon kofar zuciyarsa na wani irin tafarfasa "shi bai ga wani  abun damuwa da tashin hankali akan Dan  mahaifinta ya gansu tare ba .

"Abban nasreen ....... ta sake kiran sunansa muryarta a matukar  raunane, ya d'ago idanuwansa ya kalleta da matukar 'bacin rai Wanda yasa jikinta ya sake  d'aukar rawa gbdy ta rud'e ta kasa furta komai illa jikinta daya cigaba da kyarma.
ganin yasoma d'aga kafafunsa tayi saurin kamosa ta rungume shi ajikinta tana wani irin kukan mai ta'ba  zuciya "kayi hakuri abban nasreen  kar bud'e wallahi tsoron dad'y nake yi banason abinda zai sake shiga tsakanina dashi..
ya fizge jikinsa  yayo baya kad'an  yana fuskantarta "hakuri me kike bani ?
"Hakurin kar na bud'e kofar nacigaba da cutar kaina  ?
"Ko kuma hakurin na boye kaina alhalin akan right dina  nake.
"ke bakisan right dina ake kokarin tauye min ba ?
  Hawaye suka sake gangaro mata  ta sake riko tafin hannunsa cikin nata "ina baka hakuri ne saboda dalilai na Dan Allah kayi hakuri kayi yadda nace tsaki yaja tare da  fixge hannunsa da karfi yasoma tafiya kafin tayi wani hanzari tuni har ya isa kofar ya bud'e ,gama Bud'e kofar ke da wuya idanunsa ya sauka akan mumy da dady tsaye suna dubansa.

kallon kallo suka shiga yiwa juna daga dady har fu'ad dake tsaye daga shi sai dogon wando da farar singlet .....
Da sauri me'ad ta dafe kirjinta dake bugawa da karfin gaske ,saboda gabanta dake wani irin bugu ,take gefen kanta yasoma Sarawa tasoma ganin juya, d'akin ya dinga jujjuya mata.
dishi dishi take ganinsu acikin idanunta,  tsawon minti goma fu'ad na tsaye rike da kofar yana duban dady dake watsa masa  wani irin kallo mai gauraye da harara .
banda zallar 'bacin rai da firgici babu abinda fu'ad ke hangowa atattre da dady .
Cike da matsanancin tashin hankali dady yace  "daman abinda kuke yi kenan da yasa kuka ki bud'e mana kofa tun dazu  ?
Fu'ad ya yayi saurin sauke ajiyar zuciya da amsar "Eh acikin ransa .

Ahankali dady ya kallo me'ad dake rike da goshinta tana k'ok'arin kaiwa kasa tana nishi da kyar kmr mai cutar asthma yace "Amman me'ad kinji kunya a gidan uban.......
ai tun kafin ya kai ga k'arasawa ta lumshe idanunta ruf...
numfashin gabadaya ya tsaya cak tasoma k'ok'arin zube kasa   cike da matsanancin tsoro da firgici fu'ad ya tarota ta fad'a jikinsa ya rungumeta tsam tsam  yana kiran sunanta "me'ad!!!
amman numfashinta tuni  ya tsaya
Mumy naganin haka ta bangaje dady dake tsaye a gefenta tayo cikin d'akin tana kiran sunanta"me'ad !!! ......
ai ganin kwata kwata bata numfashi yasa ta fashe da wani irin kuka "shekenan ta mutu fargaba da tsoronka ya bugar mata da zuciya ta  mutu ... "
  ba fu'ad dake tsugune rungume daita ajikinsa ba hatta dady yayi  matukar tsorata ,mutuwar tsaye dady yayi agurin sakamako abinda yaji mumy ta fad'a ..

'YANCINKIWhere stories live. Discover now