💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*MARIAMA ABDOU MAMANE*page 94
....gani khaleed kwance yana bacci tmkr wani baby, ita kuma tana tsaye da d'aurin kirji ,yasa aunty nadiya tayi murmushi ta juya ta tsaya daga bakin kofa ,ita kuma sajida ta fito ta biyo bayanta, aunty nadiya ta kalleta tayi murmushi tace "kije kiyi wanka tukunna sai kizo ki d'auke shi karkije kibashi nono alhalin jikinki ba'a tsarkake yake ba.
wata irin muguwar kunya ce ta kamata, tunda take arayuwarta bata ta'ba jin kunys irinta wannan lokacin ba "aunty ki kawoshi babu abinda mukayi fa "waya tambayeki ko kinyi wani abu ko bakiyi ba ,ke dai kawai kije kiyi wanka kizo ki karbeshi , tun kafin ya fara kuka .
haka ta dawo d'akin tashiga wanka sannan ta fito ta zauna tana tsane gashin kanta dake ba kitso tana tajewa da cum, fad'uwar kum din shi ya tayar da khaleed had'i da sanyi ruwan gashinta data yarfo masa.
da sauri ya mike ya suri key din motarsa yana cewa "a she bacci ya kwasheni ya dubi agogon dakin sha biyu da kusan rabi ta wuce "to yanzu me kake tunani zakayi?
"tafiya mana "ina kenan a daidai wannan lokacin? Ya lumshe idanunsa yana Mika hade da cewa "gida "
"haba khaleed sai kace wani bako ?yanzu ka Kama hanyar gida kafin kaje daya tayi gsky ni ban yarda ba gara dai Ka hakura sai da safe ""Ke kuma ban da abunki daga zuwa sai kwana a gidan surukai "laifin wa ,sannan ba'a kwana agidan surukai ne, ai ni tunanina gidan nan tmkr gidanku ne amman tunda ba haka bane agurinka ga hanya nan ..
to shikenan karkiyi fushi gidanmu ne na hakura sai da safen na tafi ,tayi murmushi tace idan ma kunyar aunty nadiya kakeyi ai tuni tasan kana nan , domin d'azu ta kawo alhji karami ,ya mike kai dan Allah karkice ta ganni?
"sosai kuwa taganka kana sharar baccin nishadi.. "shikenan ai kuma zance ya kare.dryr mugunta tayi masa" ba dai takamar jaraba ba ai ka amayar daita ka kare da kwasar kunya ta sanya hijabinta ta fito tana mishi dariya ta karbo alhaji karami ta dawo tasamu guri ta zauna tana bashi nono tare da sausaron wayar dayake.
washegari tun asubar fari ya fice domin tun dare ake masa kira agurin aikinsa bayan ya fita aunty nadiya tashigo tace sajida dadynki yayo waya yace bai sameki a layinki ba meyasa kika kashe waya?
"jiya ne na kwanta akanta bansani ba ,a she na danne mukanin shine ya mutu.
"tace kya kashe waya mana tunda kina tare da mai gida ta fad'a mata cikin tsigar tsokana "kai aunty ba haka bane ni dai yau nashiga uku da tsokanarki " dadynki yace abubuwan da'aka zuba a sabon gidanku yayi miki ko kuwa , idan kuma akwai abinda kike so kiyi masa mgn .ta dauko wayarta ta kunna Takirasa yana dagawa ta gaisheshi ya amsa sannan yace mata ina son ki fadi duk abinda bai yi miki ba a gidan ki sanar min zan taho muku dashi daga nan .
tace "dady komai yayi wallahi Allah yaja da nisan kwana "amen sukayi sallama ta'aje wayar aunty nadiya tace "yakamata dai ki sake zuwa ki duba gidan kafin ki tare "aunty muje fa da cikin alhji karami "wannan ganin ciki daban don lokacin kina fama da kanki, wani tantancewa zakiyi ,yanzu dai ki kira shi khaleed din yazo ku sake zuwa ku duba ,tace to shikena.takira khaleed nan take yazo dan yana kan hanyarsa ta zuwa gidan ne daga gurin aiki yana zuwa ta sanar masa da abinda dady yace ,haka khaleed ya dauketa akan hanyarsu yake gaya mata dady yace yana son zai biyawa yan gidanmu mutun goma maka ," da wa ,da wa kikaga za'a zaba tayi ,shiru tana jinsa yace bazakiyi mgn ba ?
tayi masa banza tana wasa da yatsun danta .
yana ganin hk yasa Khalid ya kai hannunsa ya tallabo kanta da hannunsa daya while dayan na kan sitiyarin yasoma kokarin kai bakinsa kan lip's dinta, take motar tasoma zaga titi don ma su kadai ne akan titi.
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.