21

879 28 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
      MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)

Page 67 t0 68

....gabadaya Kasa xaman office din tayi, ta shiga ta fita ta yi haka yafi sau ba adadi, ga tarin aiki birjik a kasa zaman jiran sanya hannunta amman kasa  aiwatarwa saboda  ji take kamar ana xuba mata tafasasshen ruwan xafi a jikinta, idan tayi yunkurin zama a kujerar kuma sai taji kamar ana sukarta da allura, haka ta dinga sintiri tana shiga tana fita, yayin da kuma su tahir da da ma'aruf da mudassir suke kyalkyale mata da dariyar mugunta.

Mudassir ne ya dafa kafadar Tahir, "mutumina kana ganin matar nan fa gaba ɗaya ta rasa sukunin rayuwarta"

A jiyar xuciya ma'aruf ya sauke tare da cewa "Kai dai bari ai yau ina ganin ikon Allah dama akwai irin wadannan Malaman a duniya, wanda suke aiki kamar yankan wuka, ai ni duk tunanina zancen da muka yi da kai wlh ya bi ruwa, baxa a taɓa samun malamin da xai iya yi mata aiki ba da jikinta zai dinga irin wannan tururin xafin gaskiya malamin nan gaske ne"

"Ai kaɗan ka gani ma domin ni malamin nan ya tabbatar min da cewa Wannan aikin da take tunkaho da takama da shi har take wulakanta mutane a kansa sai ya fita a hannunta, na tsani yarinyar nan saboda irin wulakancin da take yi mana, da sannu sai aikin nan ya dawo wajen mu"

Murmushi Tahir yayi tare da cewa "Fatana aikin nan yana fita a hannunta wajena xai dawo, ni ne xan dawo Manager Kuma bana so ku yi kin baƙin ciki, idan matsayinta ya dawo hannuna fa kamar  komai yana wajenku ne tare xamu juya Kamfanin nan yadda ranmu yake so"

Kallonta suka yi suka ƙara bushewa da dariyar mugunta, haka suka xauna suna ta tsine mata albarka a wajen nan duk juyin da tayi sai sun mata dariya, ta koma sai kace zautacciya, sai kaiwa take tana komowa duk wanda ya ganta sai yayi mamakin ganinta saboda abinda ba a taba gani bane a history din rayuwarta, saboda a kullum me'ad taxo office tana xuwa take shigewa ta xauna sai dai idan wani abu ne mai matuƙar muhimmanci yake fito da ita amma bata irin Wannan zaryar.

Tana cikin wannan halin ne tayi wani tunani, da tsayuwar nan da take yi me xai hana baxa ta kira sudais ba, (sudais aminin fu'ad ne dama kuma sun yi magana da kawarta sajeeda cewa xata kira shi ta faɗa masa matsalar da take ciki a gida ko akwai abinda zai iya yi a kai)

Wayarta ta dakko a gida ta shiga duba number sudais, tayi Sa'a kuwa kira ɗaya tayi masa ya ɗauka,  bayan sun gaisa ne ta faɗa masa cewa tana son ganinsa yanzu a gida akwai magana mai matukar muhimmanci da take so su yi da shi. Amsa mata yayi da xai zo kamar yadda ta buƙata

Suna gama wayar ta nufi bakin motarta da sauri ta shiga tayi mata key ta nufi hanyar gida, tana cikin driving taji wayarta tayi ƙara tana dubawa taga number mahaifiyarta ne, ɗauka tayi cikin ladabi ta gaisheta, tambayarta tayi jikin nasreen, amsa ta bata cewa jikin nata da sauki, magana mahaifiyarta ta cigaba da yi.
Insha Allah da misalin karfe 4:00 xata xo ta sameta a gida tana so ta duba jikin nasreen.

dariya tayi bayan gama sauraron bayaninta kaf "mead am so disappointed of you "Meyasa kike son maida mijinki bawa ko ince mijin hjy ni haka kikaga ina yiwa naki uban dan baki da kunya kike cewa maganar da mijiki ya fada ba maganar arxiki bce.

"ence yarinya bata da lfy likita yace lallai sai daya daga cikinku ya ajiye Aikkns ya zauna tare daita domin kula da yarinyarta amman saboda maseefar son aiki kina kokarin batawa mijinki duniyarki kuma aljanarki rai .

"idan baki sani ba maganar aiziki mijinki yayi miki dayace miki kece yafi dacewa  daki zauna bashi ba domin baki taba ganin inda akayi haka ke ko a garin mahaukata baa taba yi ba miji ya zauna gida ya kula da lamuran gidan.

'YANCINKIWhere stories live. Discover now