💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)Page 57 to 58
.........Emran na fita kai tsaye bangaren ummansa ya nufa bakinciki duk ya cika masa zuciya,umma ta sarawa d'an nata lokacin daya gaya mata irin abinda sajida take masa .
Umma da kanta taje bangaren sajida domin yi Mata fad'a saboda tana mutuwar sonta kmr yadda emran dinta ke sonta, Amman abinda sajida tace ya kusan sumar umma dake zaune cewa tayi " hjy ai ba nice kawai mace ba a duniya , idan yaji haushi kuma bazai iya da halina ba ya sake aure tunda yana da kudin da zai iya auren ko mata nawa ne,Dan ni ba ruwana ,abinda nake son ya gane kuma ya fahimta banzo gidansa Dan in yi masa biyayya ba,ko wani bauta, shima yasan da wannan, in karya ne ki tmbayeshi gashi nan zaune agabanki .
Umma ta girgiza kai cike da bakinciki sannan tace "shikenan babu komai tunda da kanki kikace yayi miki kishiya zakuwa ayi da yardar Allah, Dan kuwa zan tabbatar da d'ana emrana ya auro santaleliyar budurwa yar gidan mutunci.
"To ni hjy manene zai dameni ,byn nima har yanzu amatsayin budurwa nake babu nmj daya ta'ba takani , ni da zaki taimakamin ma da kinsa wannan d'an naki ya sallemi na huta...
emran ya yunkura ya mike jikinsa na rawa zai d'auketa da wani gigitaccen mari, hjy tayi saurin taresa "kul karka soma ... akwai abinda yafi duka ko mari zafi arayuwar d'an adam, shi yafi cancanta kayi mata ba mari ba Dan ko ka mareta bazaka huce ba.Gabadaya jikinsa kyarma yake "yanzu har sunzo gurin shi sajida,?wulakantashi da iyayensa zagaye dakin yasomayi zuciyarsa na masa daci da tafarfasa, ita dai umma bata sake cewa komai ba ta tashi ta fita tana jin zafin abinda sajida tayi mata, sai dai tayi kanta alkwarin duk runtse sai ta aurawa emran mata har biyu sai dai idan shine baya so.
Kwana hudu tsakani abinda daya faru da daddare suna bacci kaddara ta fad'o gidan, domin barayi ne sukayiwa gidan diran makiya, saboda jin labarin emran yashigo da wasu makudan kudi masu yawa xshiyasa sukazo dan su amshi rabonsu, gabadaya mutanen gidan suka tara a falo daya, duk sukace kowannensu ya kwanta flat a kasa ,kowa ya kwanta amman banda sajida saboda jin itace diyar acp , taki kwanciya babu yadda emran bai yi daita ba amman taki, babbansu yace" da kyau yar kanwata kinfa burgeni sosai, dan kina da zuciya mai dakiya ke matar 'barawo yakamata kizama bana na maikacin BBC ba , amman duk da hk za'a shafa miki bakin fanti da iya rayuwarki idan kika tuna zaki ji zafi, ke ba iya ke ba har ya'yanki sai bakin fenti ya shafesu, yakarasa mgnr ya kalli wani baki mummuna daga cikin yaransa yace "kai shigar min daita turakar mai gidanta, in sha jinita sannan nayi maganin abinda ke damun kwalkwaluwarta. Take yaron ya isa inda sajida take ya kama hannunta da karfi ya fixgota xuwa jikinsa, tayi waya siririyar kara tare da kiran sunan emran da mahaifinta cikin tsananin tsoro da razana.
Emran yayi saurin d'agowa ya dubi ogan zuciyarsa na beating yace "Dan Allah oga kayi hakuri wallahi duk abinda kake so zan baku in dai zaku kyalemin mata amarya ce ka duba girman aure.
Ogan yayi dryr mugunta yace "kada ka damu abokina zan koyar daita komai sannan zai koya mata hankali da ilimin rayuwar duniya ba cutar daita zaiyi ba, idan kuma ka sake mgn abakin ranka ya afka d'akin daaka shigar daita,shi kuwa emran bai sake cewa komai ba yana jiyo ihun sajida tana kwalla ihu da gudu ya tashi ya nufi hanyar d'akin yana kiran sunanta Amman Kan ya karasa wani ya daki kansa da tsinin bunduga anan ya zube kasa a sume bai sake jin komai ba, sai farkawa yayi ya gansa kwance a d'akin ummansa su km kannensa sun zagayeshi ya dubi umma yaga fuskarta tana cikin damuwa ya sauke ganinsa Kan wasila kanwarsa yace "wasila sun kashe min sajidata ko?
Sun kashe min yar amana," amanarta mahaifinta yabani, sun kashe min ita ko?
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.