32

873 22 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
     JIDDATULKHAIRI
      MARUBUCIYAR
    MATAR  DATTIJO

Page 80

......'kwa'kwaluwarta ce ta tsaya ta daina processing na wani lokaci kafin  daga baya ta cigaba da bugawa, ji take mgnrsa ba iya cikin kunnuwanta kad'ai suka  tsaya ba har cikin zuciyarta take jin komai ,ta sake matsowa sosai kusa da mahaifinta wasu zafafan hawaye suka shiga  gangarowa akan kuncinta.
   Tafukan hannuwanta ta d'aura a saman  kafafuwansa dady Cikin mataanancin kuka, gabadayan idanunta dake zubar da ruwan hawaye ta tsurawa mahaifinta tana kallonsa tana son ya karyata mata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa, yace "mata wasa yake mata ba gaske  bane ,saboda  d'acin kalmar tafi kowace kalma muni da zafi me  ta'bo zuciya da wuyar mantawa , Amman sake maimaita kalmar da dady  yayi ya tabbatar mata da iyakacin gaskiyarsa yake nufin raba aurenta da fu'ad a.

take  ta dinga furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun  "shikenan ta faru dani takare ta fad'i hk acikin ranta cikin matsanancin tashin hankali" yaushe ne zan sake samu 'yancin da rayuwa mai dadi kmr rayuwarta ta baya ?
,tun kafin jamar gurin suyi yunkurin mgn tashiga fad'i" shikenan shikenan !!! dady naji na  amince na yarda da wannan sharad'in naka matukar zaka ya femin  , domin ni yanzu  nafi son farin cikinka a kan farin cikin kowa, duk abinda kake so shi  zanyi ,bani da za'bin daya wuce naka ..
Tana mgn tana kuka zuciyarta na rawa da  gargadinta a kan abinda take shirin aikatawa rayuwata ..
  "tana son fu'ad tamkar  ranta, kuma bata jin cewa xata iya ci-gaba da rayuwa ba tare dashi  ba,Amman a halin yanzu  ta za'bi farincikin mahaifinta akan ta cigaba da zama dashi ,zata cigaba rayuwarta  babu shi acikin duniyarta , ta gwamaci ta yiwa mahaifinta biyayya a karo na farko ko rayuwarta zata daidaita    ,koda kuwa rabuwa da fu'ad din  zai zama   silar barinta duniya.....
a yanzu ta yarda ta fad'a kowane irin yanayi ne matuƙar dai mahaifinta zai yi farin ciki ya amshita amatsayin diyarsa sa'banin shekarun baya ,da ya fita lamarinta   ......
"xata yi k'ok'arin k'arasa  fitar da ragowar soyayyar fu'ad daga cikin xuciyar tayi rayuwarta da iyayenta da tilon diyarta.
Kanta a sunkuye ta cigaba maimata  mgn    "Daddy na yarda ..,dady  na amince duk Abinda kake so a halin yanzu zan yi, ba ni da wani buri a rayuwata sama da na faranta maka, sama da na kyautata maka nayi maka biyayya a kan duk abinda kake bukata daga gare ni, duk abinda kake so  xan yi maka shi  Daddy....
Takarasa mgnr tana wani irin kuka me ta'ba zuciya kuka take sosai tmkr ranta zai fita gabadaya duniya ta cukud'e mata waje daya bata  ta'ba hk tashin hankali irin wannan da take ciki yake da muni da ciwo ba ,ta d'auka rashin son da dady yakewa fu'ad zai tsaya  a iya hk ne ,ta d'auka rad'ad'in tuni ta tsaya a wancan lokacin ,ta d'auka ko darajar samun nasreen atsananinsu zai sauk'ak'awa zuciyarsa kiyayyar fu'ad .....
Amman da kalamansa  na yanzu ta fahimci komai ya sauya agareta ,ta gane ita din ba kowa bace, tasoma fahimtar talaka marashi da galihu ya fita kwanciyar hankali sau dubu.
yanzu wakilla najma datake kallo mafi kaskancin  gani akanta tafita kwanciyar hankali da walwala .
"yau din tazo mata da tashin hankali da rud'anin rayuwa maramisaltu "ya zatayi da kaddarar data gifta mata da rayuwarta gabadaya? Parlour'n ya d'auki shiru ,gabadaya jama'ar dake zaune acikinsa sun rafka uban tagumi, ban da sautin  kukan me'ad bakajin sautin komai acikin parlour'n .....

Yayinda Mahaifinta yaji dadin jin  kalaman daya fito daga bakin  'yar tasa, a nan take ya fahimci me'ad dinsa ta sauya ,ta  samu natsuwa, ta k'ara hankali fiyye da lokutan baya, sannan da gaske take nufin nadamar abinda tayi masa a baya ,sannan a halin yanzu yasan ko zuwa gaba yace mata "ga abinda yake son tayi masa tayi batare da sa'bawa umarninsa ba.
cike da matsanancin farinciki da jin dadi yace "me'ad na yafe miki duniya da lahira Allah kuma yayi miki albarka, Sannan amatsayina, na mahaifi gareki ina  umartarki  daki   baro hotel din da kika   kama ki  dawo gidan ubanki da zama .

'YANCINKIWhere stories live. Discover now