42

1.1K 21 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
*HUSAINA,D'ANLARABAWA (YAR PARTY ABBA GIDA GIDA)*🤩🤩

page 91

....wani irin kallon  kaskanci fu'ad ke musu alokacin da suke takowa zuwa garesa, yana jin wani irin kwarin gwiwa attare dashi ,gaba d'aya yagama shiryawa yadda zai yi dasu idan sukayi kuskuren kai hannunsu jikinsa .
cigaba da kusanto shi suka yi suna mammatsa yatsun hannuwansu , sai dai tun kafin su k'araso garesa suka ji an kuraye gidan da harbe harbe, suna waigawa ta window, suka ga 'yan sanda  runduna guda kewaye da gidan suna ta faman harbi, suna kuma k'ok'arin shigowa ciki.

wani irin mamaki ne yakama safwan,iya tunaninsa wad'an nan polisawan guda biyu ne kawai sai shi fu'ad din, a she ruf da dugu akayi masa bisa dole ba dan yaso ba yayi saranda da fasa niyyarsa ta farma fu'ad ta karfi da yaji...

ahankali ya kalli fu'ad da murmushi ya bayyana akan fuskarsa yace "ka tsira daga wannan tarkon nawa, sannan ka sake cin narasa akaina ,amman wallahi muddin ina raye sai na halakaka, bazan bari a yanke min hukunci ba,har  sai na kasheka kafin kaga tawa mutuwar saboda nasan daga nan  kisa ne hukuncina , yana gama fad'ar haka yayi baya da hannuwansa duka ya ciro wata karamar pistol da niyyar harbin fu'ad, sai fau!
wani d'an sanda ya harbe hannunsa, sai ga bindigar hannunsa ta fad'i kasa jini ya tsirtu yashiga tsiyaya,  ya rike hannun had'e da sakin wata k'ara, take police suka zagayeshi yana makarkatar zugin ciwo, suka damke su baki d'aya, sai mota babu abinda ke bakin fu'ad sai godiya ga allah daya kubutar dashi daga hannun wannan bakin azalumin  bawan mara imani.

haka dai suka isa police station aka shiga dasu baki d'aya domin tantance masu manya laifi .
     andai samu  safwan dumu dumu da laifin aikatawa dad'y fyade ta hanyar luwadi da kuma safarar kwayoyi zuwa kasashen duniya  ,azabar da'a gana musu ta rana d'aya yasa safwan yace" ya tuba bazai sake aikata makamancin abinda ya aikata ba, amman duk da hakan bai hana shi samun hukunci daga hukuma ba, domin har kotu za'a turasu, safwan ya kalli fu'ad ya girgiza kanshi yana zubda hawaye a zuciyarsa yace "karshen rayuwata tazo kenan  yana ji yana gani aka tura su zuwa kotu ,sai yanxu yake bakincikin halin daya tsinci kanshi yasan dai mafi kaskancin humunci shine d'aurin rai da rai .
fu'ad wanda tunda abun ya faru ya kasa samun sukuni har sai dayaji zance zuwa kotu ya sallami polisawa ya fice byn ya sake musu kyauta ta musamman bisa kokarinsu.

tun sanda me'ad tasan abinda ya faru da mahaifinta ta gaza samun kwanciyar hankali, taki kwantar da hankalinta fu'ad ne ke ta faman aikin rarrashinta data kwantar da hankinta komai ya rigada yazo karshe ,domin rayuwar safwan tazo karshe sai dai wani ikon Allah.

bangaren dad'y kuwa har lokacin yana karkashin kulawar likitoci, sai an kwantar sai antayar dashi ko d'anyatsan bai iya motsowa , magana yake son yi domin yiwa fu'ad godiya bisa kokarinsa garesa dan duk halin da'ake ciki yana ji ,amman  babu bakin magana ,sai hawayen nadama dake tsiyaya daga ciki kwarnin idanunsa yana d'iga akan pillow da kansa ke kwance akai .
Allah sarki bai ta'ba tunanin hk zuciyarsa take ba, hakika ya zalinci ruhin dake tattare da alkhari.

tuni an tura su safwan kotu har an yanke musu hukunci kisa bakidayansu   .haka akayi wannan shari'a kowa yayi farincikin da hakan wannan shine karshen safwan da mukaranbansa .

shi kuma dady yacigaba da samun kulawar data dace ,dan har an daina saka masa pampers din da'ake saka masa,a wannan lokacin likitoci suka fahimci barin jikinsa d'aya yasamu matsala dan har lokacin babu baki, ga wuyansa ya karkace bakinsa ma ya juye ala'mun dai cutar shanyewar jiki takamashi..
gabad'aya ragamar rayuwar gidan dad'y takoma hannun fu'ad da me'ad, duk wani abinda za'a bukata a gidan fu'ad ne wanda hkn ke sake saka dad'y jin kunya, kukan nadama kam yayi shi har babu adadi, a she ba ragamar diyarsa kad'ai fu'ad zai dawo ya dauka ba, har da ragamar gidansa. ...

'YANCINKIWhere stories live. Discover now