💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*MARYAM ALHASSAN D'AN'IYA (MAR'OB)*page 88
...tunda fu'ad ya fice daga d'akin ,dad'y ya tsura mata idanunsa yana kallonta ,har lokacin mamakin abinda ya faru yake, ayi ciki har na tsawon wata uku acikin gidansa batare da saninsa ba ..
"hakika ya cika babban sakarai da yayi tunanin hargaginsa na wancan ranar zai yi tasiri a zuciyar fu'ad, a she ihu kawai yake baya ga hari, yana lalla'bowa ya more diyar da yake da burin rabata da rayuwarsa.naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske, lokacin guda kwalkwaluwarsa tashiga caji domin neman mafuta, dan dole yasan abunyi kafin ruwa ya karewa d'an kada, kar abubuwa suzo suyi masa tsamari.
" da ala'mun yaron na son ganin bayansa ne a dalili shishigi dayake masa cikin lamarinsa.
"Shi duk cikin lamarin ma shi yafi ganin laifi me'ad domin sai bango ya tsage kadangare ke samun guri 'buya ,duk laifinta ne anan Sam yaron bashi da laifi .runtse idanunsa yayi sosai yace "ina alkwarin da kike min me'ad na zaki cire fu'ad acikin rayuwarki?
"ni shikenan kullun ni ke da fad'uwa, shi yake da galaba akanki ?
"da fari yayi nasarar akanki yanzu ma kina k'ok'arin sake bashi wata damar, koma nace kin rigada kin bashi..
"Yanxu kin kyauta min kenan?
" gabadaya kin rusa min shirina akanki kinsa karfin gwiwata ta raunana .
"me yasa tun farko kika nuna min zaki rabu dashi?
"Me yasa kinsa bazaki iya rabuwa dashi ba kika zabeni akansa?"zaki sake tozartani a karo na biyu a idanun safwan ?"me kike son na cewa safwan?
" fad'a min, fad'a min abinda kike son na fad'a masa akan tsinancin da kika yi ?
ya bud'e idanunsa da suka canza kala tmkr garwashin wuta tsinuwa kuwa har lokacin bai dana yiwa fu'ad ba.
kuka take sosai har sanda momy tashigo d'akin a fusace tace "enough is enough idris yaya da wahala haka?
" ina fa guje maka karshen inda taurin kanka zai kai rayuwarka, da iliminka da komai kake jayayya da ikon Allah,ka hakura ka daina nuna karfin ikonka dayawa akan lamarin nan ,saboda kai ba kowa bane ,yanzu idan Allah ya gamada zai iya d'aukeka a doron duniyar gabadaya muga karshen taurinka .
" haba wasu abubuwan fa boyesu ake a danne zuciya domin rayuwar ta tafi yadda ake so ..
A matukar tsawace ya dakatar da ita ,ta hanyar d'aga mata hannunsa "ya isheki haka , karkiyi tunanin zan yi gun da bakina na boye abinda ke raina, dole na fito na fad'a saboda bana sonsa...
Kirjin me'ad ya buga da wani irin matsanancin karfi tayi saurin runtse idanuwanta saboda d'acin kalmar da mahaifinta ya fad'a ,
"tun ranar farko dana d'aura idanuna akansa naji muguwar tsanarsa ta dira a kahon zuciyata ,Wanda har yau ban daina jin hkn ba .
bana son sa kuma banga mahalukin da zai sani dole nasoshi ba ,Dan haka karki sake saka bakinki acikin maganata da ya'yana...."Magana kmr nayi nagama tunda ba kai kad'ai ka haifesu ba ,
" kuma ina son in sanar da kai wani abu ,zaka so fu'ad a lokacin da shi son bazai maka amfani ba, domin zakayi nadamar abinda kayi ,yayinda ni nadamarce bana son kayi shiyasa kake ganin kullun nake nusar da kai."ni na d'auki cikin me'ad na tsawon wata tara da kwanaki tara, nice wace idan na tsine mata take tsinewata zatayi tasiri akanta sabanin kai , Sam Sam Sam me'ad bata aikata tsinanci ba illa ibada ga ubangijinta wanda kai kaima kasan da wannan,
daga yanzu ina adduar ta haife wannan cikin lafiya, fu'ad ya sake yi mata wani, idan ka hanata rayuwar aure a gidanta ,tayi rayuwar aure anaka gidan,tana gama fad'ar hk ta juya ta dubi me'ad dake kuka tmkr ranta zai fita "kingani ba, kinga abinda d'an burouban abinda taurin kanki da kika gada na wahala ya janyo miki ko, "kullun nake gaya miki illar abubuwan dakike yi Amman baki ji saboda mugun halinsa da kika d'auko.
" ina jin kmr na cire hannuna acikin lamarinki na barki da damuwarki ki karata saboda duk rashin jin maganarki ne ya janyo faruwar komai..
Da sauri me'ad ta duro ta durkusa gaban mumy tana kuka "Dan girman Allah mumy karki cire hannunki cikin lamarina, idan kika cire hannunki rayuwata zata sake taggaya. .
"Dady kayi hakuri ka yafe min a karo na biyu ba Dan na sa'bawa umarninka ,dady kayi hakuri ka sausautawa fu'ad wannan kiyayyar ,wallahi fu'ad mutun ne gari abun alfahari ,dady kayi hakuri ka yafe min kabarni na koma gidana nacigaba rayuwa da mijina saboda har yanzu ina son shi takarasa mgnr wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata.
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.