💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)page 49 to 50
....kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu duka uku sajida me'ad malik, shiru me'ad tayi tana kallonsa batare da ta sake yunkurin cewa dashi komai ba ,sai dai gabadaya nadama tattare da kunyar abinda tayi masa a yanzu ya kamata tare da raunata wani shashi na gangar jikinta," ta wulakanta mafi kusanci ga zuciyarta bisa ga mummunar d'abi'arta...."me yasa tayi saurin marinsa?
"why why why!!! me'ad?
"why did you slap him..?
tana nan tsaye jikinta na rawa har malik yakaraso zuwa inda take tsaye jikinta nacigaba da kyarma ya miko mata diary dinta ......nadama ce fal dankare da zuciyarta "hakika ta cuci kanta ta cuci rayuwarta ba zata ta'ba yafewa kanta abinda ta aikata masa ba matsawar yayi silar rasa fu'ad dinta....."ki amsa ko nabawa kawarki ne?
jin sautin mgnrsa yasa tayi saurin dawowa cikin haiyacinta domin natsuwar tasoma barin gangar jikinta, kallo daya zaka mata kagane kalar damuwar datake ciki.
sai daya sake mgn sannan jiki a sanyaye tasanya hannuta ta amshi diary dinta, shi kuma ya juya tamkar wanda kwai ya fashewa aciki yasoma tafiya , har ya kai gurin mashin dinsa yana shirin hawa yaji sautin muryarta ahankali "tsaya dan Allah sannan tasoma kok'arin takowa zuwa inda yake, jikinta a matukar sanyaye .muryarta na rawa tace "dan...dan girman Allah kayi hakuri ta furta hkn tana mai runtse idanunta kasancewar wannan shine Karo na farko data bai wa wani mutun hakuri ,bayan iyayenta da suka kawota duniya "kayi hakuri ta sake maimaita kalmar muryata a raunane tare da bud'e idanunta fess akansa tana kallon yanayinsa da gbdy ya sauya, a yanzu dayake gabanta ganin take tamkar fu'ad dinta ne tsaye a gabanta cikin matsanancin damuwa , "hakika nayi abinda bai dace ba ,da rashin kamata gareka,
tun ranar farko dana soma ganinka a gidanmu nayi tunanin kmr nasan fuskarka amman alokacin na kasa tuna inda nasanka, sannan lokacin dana ganka tare da fu'ad a boutiq shima ban tantance alakarku dashi ba amman dai kayi hkr dan Allah." babu komai ,komai ya wuce Allah ya kiyaye na gaba, hk daman rayuwar take ,da nabi shawarar fu'ad da ban jawo wa kaina wulakanci ba, domin babu abinda ya kai wulakanci kmr a tsinkaka ta hanyar mari..... ...amman babu komai "me'ad yakira sunanta ,nasan kina mutuwar son abokina fu'ad duba ga yanayin nadamarki bayan kinsa alakata dashi, amman shi mutun ne me matukar kamewa ,kai tsaye hk bazai ta'ba fuskantarki ba ....
"nasani ....nasan da haka amman ko zaka iya taimaka min plz takarasa mgnr muryarta na craking ?
domin zan iya yin komai akansa ,"da fari dai ka taimaka min da number wayarsa tare da sake bashi hakuri.
"sajida plz ki matso kusa mana ki bashi hakuri kema bawai ki wani ja kin tsaya kina kallonmu ba."me zance masa me'ad?
"me kike son nace masa after kingama aikata son ranki ?
"i think kin bashi hakurin kuma yace ya hakura."eh amman ni dai kice masa wani abu dan Allah har yanzu akwai damuwa a tattare da shi.
"dole kuwa kiga damuwa atare dashi me'ad , bashi ba koni kika karewa kallo zakiga ala'mun hk atare dani "ta yaya daga ambatar sunanki zaki maresa?
" tun ranar farko daya kira sunanki na gaya miki definitely wannan mutumin yasanki wani guri amman kika nuna min sam ba hk bane yanzu wa gari ya waya?" komai sai kin saka zafin rai aciki, sosai sajida tayi mata fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba har sai da malik ya nuna abar zance ya isa hk "kuma har ga Allah komai ya wuce daga karshe ya karanto mata number fu'ad bayan tayi tsore, tace yabata nashi yabata sannan ya wuce .
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.