💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)Page 59 to 60
Not edit
........Sajida ta nufi d'akinta ta fad'a kan gadonta cike da matsanancin farinciki ji take tmkr tasamu fu'ad tagama , tunani ne ya fad'o mata a rai ta mike zumbur tayi bathroom tayi wanka, ta canja kaya zuwa wasu hadaddun kananan kaya, riga da siket blue da dan ratsin yellow,tasanya abaya ta yafa mayafi ta fito ,she look very attractive parlour'n kasa ta sauko adaidai lokacin da motocin mahaifinta suka bar gidan,sai aunty nadiya mai aikin da'aka samo musu ce a tun sanda aurenta ya mutu a zaune ,sajida batayi mata magana ba sai ita aunty nadiyar ce tace, dining fa ya kammala .
"No karki damu aunty,zan fita ne but yanzu zan dawo takarasa mgnr idanunta na ga duban agogon bango parloun dake walwalin haske kwan fitila ya sake kara haskawa, karfe 12 na safe yanzu ta wuce, aunty nadiya tace sai kin dawo. .
kai tsaye motarta tashiga ta nufi gidansu misna, kmr koda yaushe momyn misna tana kitchen tana aiki domin akwaita da kaunar girki, wanda hkn ke sata tuno da amminta sam itama hk take da son girkin tsiya dan wani lokacin babanta kance "Kyan 'ya tagaji uwarta amman ke sam baki d'aukota a komai ba...
Ita kuma sai tace masa" ai shi ta gado tunda ba asan nmj da shiga kitchen. ba...
ta gaidasheta kana ta nufi dakin misna straight ,akwance ta tarar daita tana kallo a zeey world misna naganinta ta mike zaune da murnarta ta rungume sajida ajikinta tana jin dadin ganinta cikin koshin lfy bakamar kwanakin baya ba, itama sajida ta rungumeta tana jin dadi aranta, tana matukar jin dadin yadda misna ke nuna mata kauna sajida tace "wani guri mai mahimmanci nazo ki rakani "a tunanin misna ko gurin shakatawa zasu kasancewar tasanta da son zuwa irin wuraren.da azama misna ta diro daga kan gadonta tare da daura after dress akan riga da wando datake sanye dashi domin fitowarta wanka kenan , tare suka fito misna na rolling mayafin after dress akanta umman misna tace "sai ina adaidai wannan lokacin?
Sajida tace "umma fita zamuyi amman yanzu zamu dawo, umma tace " karfe 1 ta kusa kuje kuyi sallah sai ku zo kuyi lunch sannan rana ta fara yin sanyi sai ku fita, babu musu suka bi umarninta suka koma d'akin sukayi sallah sannan suka ci abinci Wanda sama sama sajida taci dan ta matsu bata isa inda zuciyarta ke bukatar zuwa ba,
sun fito suna yiwa umma sallama tace "karsu dade .tafiya suke ahankali sajida ke jan motar muryarta a raunane sajida tace "kawata baki tmbayeni inda zamu ba ?
"tambayar mai zan miki byn nasan wata killa wajen shakatawa zaki."No kin sa'ba tsaitin tunaninki ,domin kuwa ba nan zamu ba ,kina jina ko a watanin baya da suka gabata kin sha ganina cikin tashin hankali da damuwa wanda kowa ke bukatar son sanin abinda ke damuna alokacin, amman naki bada wannan kofar ,sai dai a yau zuciyata ta aminta da nasar miki da damuwata ,bisa aminta da zuciyata tayi dake, me'ad itace wacce tafi cancata tasan matsala fiyye da kowa a duniya, sai dai al'amarin damuwata ya danganceta..kina saurarata kuwa?
"Ina jinki sajida sai dai maganarki tasanya kuzarin jikina yin rauni ."karki damu da furucina nasanki, nasan halinki da zurfin ciki duk wuya duk runtsi akayi sirri dake baza ta'ba jinsa akoina ba shiyasa nasanyoki cikin abinda yashafi sirrikan rayuwata.
Taja numfashi ahankali ta fitar tana mai karya kwana wanda kai tsaye inda tasan fu'ad yake zama tare da abokansa ta nufa daga nesa kad'an da gurin tayi parking ta tsura masa idanunta sosai kmr zata fixgosa gareta, yana zaune tsakiyarsu kabeer suna hira wanda ba kasafai yake sanya bakinsa ciki ba.kallonsa kawai take bata ko kifta ido, ga wani irin kalar murmushi datake masa wanda ita kanta batasan tanayi ba balle wanda ake dominsa, tsawon lokaci tana zaune tana kallonsa taji an hura mata iska a idanunta, tayi firgigib ta dawo haiyacinta tana duban misna dake zaune a gefenta ," misna a yau nake son shearing wani abu daya danganci rayuwata dake "waye wancan dake zaune tsakiyar maza uku din can sanye da t shirt fari da bakin wando?
tayi mata tmbyr tare da d'auke idanunta akanta ta maida kan fu'ad da bai san wainar da'ake toyawa ba .
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.