💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)page 31 to 35
.........diraving kawai yake cike da matsanancin tashin hankali ,yayinda gefe guda na zuciyarsa ke wani irin harbawa, saboda jin bugun zuciyarsa yake tun daga tsakiyar 'kirjinsa har ilahiri sansan jikinsa. wanda hakan ya haddasawa gefen kansa sarawa da 'karfi, gaba d'aya ji yayi jikinsa ya mutu, tu'kin ma na neman gagararsa.
A hankali ya gangara gefen titi yayi parking tare da dai-daita tsayuwar motarsa ya rungume sitiyarin motar had'e da d'aura kansa bisa hannuwansa yana fitar da numfashi me tattare da hucin zafi.
tun daga nesa Sajida wace daga gidan me'ad gidan misna ta wuce, ta hango motar fu'ad parke a gefen titi cike da matsanancin mamaki ta soma rage gudun motarta har sanda ta iso daf da inda motarsa take .
tayi parking ta fito da hanzarinta daga cikin motarta ,hankalinta a matu'kar tashe ta doshi inda yake, tana kare fuskarta da tafin hannuta saboda hasken ranar daya dallare mata idanu , jiki a sanyaye ta 'karasa jinkin motar ta tsaya tare da kai hannuta ta k'wank'wasa glass d'in motar, wanda hakan yasa fu'ad 'ko'karin d'ago idanunsa domin ganin kowaye.A hankali ya sauke kyawawan idanunsa a kan fuskarta dake cike da mamakin ganinsa a gurin , runtse idanunsa yayi sosai yana jin wani irin d'aci a ransa mara misaltuwa ....
da hannunta tayi masa alama yayi warning glass din motarsa, sai da ya furzar da iska me zafi ta bakinsa sannan yayi 'kasa da glass din, kana ya mai da kansa kan sitiyari kamar yadda yayi da farko , shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da zuciyarsa take ciki a kan wannan matsalar dake shirin kunno kai cikin rayuwarsa da al'amuran gidansa.
sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi "lafiya Abban NASREEN kayi parking a gefen titi haka?
"idan ma wani abu ne ke damunka, kamata yayi ka samu ka qarasa gida first, domin samun natsuwar zuciya saboda tsayuwarka a nan is very very risking.. ta 'karasa mgnr tana zagayo wa d'ayan gefen tana me k'wank'wasawa alamun ya bud'e mata .
da 'kyar ya samu ya danna wani abu a cikin motar domin bata damar shigowa ba tare da yace mata komai ba saboda kansa dake cigaba da sarawa.
ta bud'e murfin motar jikinta na rawa tare da janye jakar briefcase d'insa dake kujera me zaman kanta, ta zauna tana masa fari da ido muryarta a sanyaye tace " sannu Abban NASREEN na san duk damuwar nan taka ,baza ta rasa nasaba da matsalar kawata ba?
,"amman ka yiwa Allah kayi hakuri Insha Allahu komai zai zo da sau'ki, me'ad ce bata d'aukar shawara na rasa abinda ke rud'arta....A hankali ya d'ago idanunsa tare da waigowa gefen da take zaune ,idanuwansu suka tsarke cikin juna, suna had'a ido kowanensu ya kafe d'anuwansa da kallo zuciyoyinsu na ayyana musu abubuwa da yawa .
kallon cikin kwayar idanunsa ta cigaba da yi tana jin wani abu na yawo a jikinta ,had'e da hango wani irin tashin hankali kwance a cikinsu , a hankali ya soma kokarin motsa bakinsa " kika ce kin rasa abinda ke rud'ar ta ?
ta d'age masa girarta d'aya tana sake masa fari da ido muryarta a sanyaye tace "eh Abban NASREEN ni dai gsky bansani ba, amman idan kasan abinda ke rud'arta ka taimaka ka gaya min ?
" girgiza kansa kawai yayi ba tare da ya sake cewa daita komai ba, ita kuma ta bishi da mayataccen kallo tana yaba kyawun halittarsa, ganin yadda jikinsa yayi matukar amsar kayan dake sanye ajikinsa ya kara hura wutar soyayyarsa acikin zuciyarta ,ji take tamkar ta shige jikinsa ta rumgume shi sannan ta rarrashsshi a kan tarin damuwarsa .
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.