5

1.3K 42 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
      MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)

page 21 to 25

........kwance yake akan makeken gadonsa kiran italy yana sharar  baccinsa hankali kwance  lullu'be cikin bargo me taushi da kamshi ,yaji sautin ringing din wayarsa ta karad'e ilahirin d'akin.

a natse ya farka daga bacin dayake  batare daya bud'e idanunsa ba, yasoma lulubar inda ya ajiye wayar  ,sannan ya bud'e idanunsa da kyar, saboda baccin dake cikinsu,  dan sam jiya damuwa bai barsa ya samu ishashen bacci ba sai bayan da aka idar da sallar asuba tukun yasamu bacci ya d'aukeshi .

sunan wanda yaga yana yawo ajikin screen din wayar ne, yasanshi mikewa da sauri yana yaye bargon daya lullu'ba dashi kana yasoma kokarin amsa wayar cike da muryar bacci "hello sir.

daga can bangaren me gidansa ne ya amsa da hello fu'ad   bacci kake na tasheka .

"no karka damu sir gud morning ya fad'i hkn atare yana runtse idanunsa tare shafa sumar kansa.

"okay ya  lafiyar  jikin NASREEN  hope she's getting better?

"taji sauki sosai sir nagode da kulawa sir .

"karkadamu ammm..., ina bukatar ganinka ogently yanzu idan baka komai.

"babu abinda nakeyi sir ganin nan zuwa yanzu just give me 10 to 15 minti sir .

"alright sai  naganka me gidansa yakatse kiran .

shi kuma ya sauko daga saman gadon  yana mika had'e da yin salati sannan ya nufi bayi yayi yayi burushi tare da yin wanka shap shap   ya fito daure da madaidaicin towel iya cinyarsa wani towel din na rike a hannunsa yana goge sansar jikinsa .
yagama ya tsaya gaban mirrow yasoma shafawa jikinsa lotion tare da bin ilahirin jikinsa da turare me dadin kamshi ,yayi corm din sumar kanshi, ya matsa inda wardrobe dinsa yake ya fidda wasu kaya riga da wando sai farar riga me dagon hannu daga ciki ya d'aure wuyansa da jan kyalle wato tie ya karasa inda jerin takalmansa suke ya d'auki shoe baki wanda zai sanyawa kafafunsa, yakoma ya zauna bakin gadon yasaka ya Mike tsaye cikin hanzari ya d'auki karamar wayarsa ya zira cikin aljihun suit dinsa ta ciki , sai agogonsa na  fata daya d'auka yana kokarin d'aurawa atsintsiyar  hannunsa at the same time kuma yana ya kokarin bud'e kofar d'akinsa .

cikin sauri ya fito daga  d'akinsa batare da ya tsaya tunanin sanyawa cikinsa wani abu ba  , daf da zai karasa bakin kofar fita daga parlour'n .
me'ad dake tsaye a kitchen tana kokarin had'a musu breakfast ta kwaso a guje tana haki ta sha gabansa " kai kai ina  zaka tun da sanyi safiyar nan hk?
takarasa mgnr
tana me daidaita tsayuwarta   a bakin kofar tana jijiga ilahirin jikinta tana dubansa kasa da sama a matukar wulakacin "you can go anywhere fu'ad..we must settle this matter on ground before you go out .

wata uwar hararar ya banka mata sannan yace "wata  magana kenan zamuyi settle?

"maganar  Monday mana.
"yazamuyi ranar monday waye zai zauna agida ya kula da yarinyamu ?
"you know I cannot afford  not to go work ..
saboda rashin zuwana zai haifar da mummunar damuwa, idan baka manta ba, kasan abinda ke faruwa a campany'nmu a yanzu ,amman idan ka manta bari na tuna maka" duk  kuskuren dayasa mutun yayi wasan fashin  zuwa gurin aiki daidai da rana daya, baza'a kar'bi   any excuse ko complaining daga garesa ba, the next thing korarsa za'a yi ....

"an so what? ya furta a matukar fusace

"ina ruwana da korar mutanen da'ake, wannan aikin naki fa kin gadamar yinsa ne ,if not zan iya d'aukar lalurarki batare da kinje koina ba..dan haka karkiyi tunanin ni fu'ad zan kasance daya daga cikin mazajen da suke kasancewa hajiya ba, sannan ni ba bawanki bane da zauna a gida tare da yarinya alhalin gaki a raye baki mutu ba ,dan hk in your dity life don't expecting me to be baby sitting  .
kina mugu mugun bani mamaki me'ad da har kike kokarin  na amshi   abinda yazama *'YAN CINKI*  hakika kin kusan haukacewa akan wannan iskanci da kike kokarin bijirowa dashi dan har abada bazaki ta'ba samun damar meidani mijin haji.

'YANCINKIWhere stories live. Discover now