💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*🤝🏻🤝🏻🤝🏻
Page 81
.....kai tsaye fu'ad gida ya nufa zuciyarsa na wani irin tafarfasa,yana shiga parlour'n ya fad'a Kan doguwar kujera 3 siter yana fitar da numfashi me gauraye da zafin ciwon abinda surukinsa yayi masa ,ahankali tunaninsa ya cigaba da gudana lokacin daya sautin kukan matarsa yashiga dawo masa tana bashi hakuri"kabar min yarinyata, idan ka rabani daita mutuwa zanyi ..."Dan Allah kabar min ita ....
runtse idanunsa yayi sosai tare da mikewa zaune da kyar, gabadaya ilahirin jikinsa yayi mugu mugun sanyi, ga wani irin matsifaffen ciwon da kansa keyi akan furucin mahaifinta ga tashin hankali daya barota ciki , da kyar ya iya bud'e idanunsa ya Mike tsaye yashiga zariya acikin parlour'n dafe da goshinsa , yana tunanin mafuta " ya Allah ka kawo min hanya me sauki da komai zai daidata gareni ,Allah kar kasa wannan bawa naka yayi nasara akaina ......."ya dade yana zurfafa tunaninsa ,bai San lokacin daya d'auka tsaye agurin ba, kafin daga bisani, ahankali ya d'aga kyawawan idanunsa ya saukesu akan wrist watch din dake d'aure da tsintsiyar hannunsa, karfe shadaya ta wuce da wasu 'yan mintuna, tsaki yaja "hk kawai wannan tsohon na neman hadasa masa ciwon kai na babu gaira babu dalili ,a sukune yasoma tafiya zuwa d'akinsa yana 'bal'bale botiran gaban rigarsa yana shiga bathroom ya k'asara cire kayansa gbdy ya watsa Kan kujera .Bathtub yashiga ya tsakarwa kansa ruwa, take yaji wata natsuwa ta musamman ta saukar masa tare da bin ilahirin sansar jikinsa ,ahankali kuma yake jin hankalinsa na kara kwanciya ko babu komai yasan halin da matarsa da 'yarsa suke ,bugu da k'ari yasan inda suke Wanda a duk lokacin dayake da bukatar ganinsu zai gansu, wanka yayi shap shap ya fito kugunsa daure da towel fari ,while dayan hannunsa na rike da wani karamin towel yana goge sansar jikinsa dashi ,byn yagama goge jikinsa white boxer and white singlet ya saka yabi ilahirin jikinsa da turaren daya zame masa jiki ,sannan ya fad'a gadonsa zuciyarsa na matukar bugawa da karfin gaske.
"Dole duk runtse muna tare dake me'ad ,ko baki min halicci komai ba arayuwata bazan iya sakinki ba ,da zan sakeki da tuni bamu kawo wannan lokacin ba ,"ka saketa ko mu had'u a kotu maganar dayake tayiwa fu'ad yawo kenan acikin kwalkwaluwa ..dogon tsaki yayi inda zuciyarsa tashiga hasko masa kamannin safwa yayi saurin runtse idanunsa ya d'aura hannunsa akansa tmkr me shirin yi kuka yace" i a m mad iam stupid matukar nayi kuskuren sakin me'ad wa wani katon banza da wofi ..ina sonki matata duk kece silar fad'awarmu cikin damuwa ga wani tashin hankali na shirin afka mana. wayarsa ya janyo ya fara dialling number me'ad domin yaji muryarsa sannan ya kwantar mata da hankali Amman har 5 missed calls bata d'aga ba, tsaki yaja yayi jifa da wayar akan gadon "matsalar kenan taurin kai .
rungume hannunwansa yayi a saman kirjinsa yana kallon saman d'akin ,yayinda zuciyarsa ke hasko masa ita ji yayi hannunwansa daya rungume akirjinsa bazasu wadatar dashi ba ,yasa ya janyo pillow ya matse akirjinsa yana jin tmkr itace rungume ajikinsa, ahankali yana tunaninta ke fixgarsa ya kai hannunsa ya janyo bargo ya lullu'be jikinsa wani irin tsuma jikinsa ke yi tmkr zaki ga joystick dinsa sai mikewa take alamun tana bukatar abincinta wani tsakin yaja mtsssss hade da sanya hannuwansa duka ya dafe saman joystick da kyar yasamu bacci 'barawo yayi awon gaba dashi cike da matsanancin kaunar matarsa ......
Washegari ya tashi tattare da kuzari da farincikinki yashiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya zuwa office ,gabadaya ya nemi tarin damuwarsa ya rasa sai zallar farinciki dake dawainiyya dashi ,haka ma a office aikinsa yake gudanarwa cike da kwanciyar hankali ,a cewarsa matsalarsa ta kau damuwarsa tak'are tunda yasan inda iyalinsa suke Dan shi Sam bai d'auki mgnr dady da wani mahimmanci ba ......
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.