43

1K 18 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
*HUSAINA,D'ANLARABAWA (YAR PARTY ABBA GIDA GIDA)*🤩🤩

page 92

....kallo daya fu'ad yayiwa sajida yayi saurin d'auke idanunsa akanta, sakamakon tuno  abubuwan da suka faru abaya, sannan ya nuna musu  gurin zama da hannunsa, ya mike tsaye yana mai mika wa Khalid hannu suka gaisa cikin sakin fuska, itama sajida taso gaisheshi amman tsoron abinda zai biyo bayan gaisuwar  ya hanata , ta sunkuyar da kanta k'asa dan wani irin maseefaffen kunyarsa ce tayi mata diran makiya ta rufeta gbdy  tayi mata dabaibayi.

fu'ad wanda ke sanye cikin farin yadi fari sol mai shara shara wanda ake iya hango farar singlet dinsa  yace wa khaleed yana zuwa tare da shigewa ciki inda me'ad take.

ahankali ya tura kofar d'akinta yasanya kansa yashiga wani ni'imataccen kamshi ne na musamman ya doki hancinsa ,ahankali ya lumshe kyawawan idanunsa saboda wani sanyin dadi daya ziyarci kirjinsa, lokaci guda kuma soyayyarta dake daskare acikin zuciyarsa ta sake ninkuwa .
yana mugun kaunar kamshin turaren da take amfani dashi ,a duk sanda ya shakesa sai ya jisa cikin wani yanayi na bugawar zuciya.

a zaune akan kujerar mirrow dinta ya sameta tagama shirya kanta  cikin wani ratsantsen less mai ruwan yellow da zanen fulawa Baki baki ajikinsa , wanda akalla kudinsa zai kai kamanin 70k anyi mata dinkin doguwar rigar wanda yasha aikin tsone work sai sheki  take zubawa tana fitar da wani sihirtaccen kamshi .
  ya k'araso zuwa inda take cikin haukinta ya rankwafo ya d'aura ha'barsa asaman  kafad'arta ,ta cikin mirrow ta d'ago tsumammun idanunta dake d'auke da Zara zaran gashin ido ta kalleshi tana mai kashe masa idanuwanta da suka sha ailine "honey har bakin sun karaso ?
ya kashe mata idonsa daya alamun eh yana yawo da hannunwansa duka ajikinta yana cigaba da kallonta "ok bari naje naga wad'an bakin da tun jiya nasha dogon wa'azi akansu ta fad'i hk ne kasancewar ya sanar mata da zasuyi Baki sai dai bai  bayyana mata ko su waye ba.

"my love muje ki gansu but karki manta da alkawarinmu, duk wad'an da ki kagani amatsayin bakinmu ki amshesu hannu biyu, sannan abinda suka  nema gurinki ki tabbatar da kinyi batare da wani bata lokaci ba ,ina son  komai zakiyi kiyi saboda a Allah da kuma ni"
"karka damu honey matsayinka ya wuce  haka ,ya wuce kace ga abinda zanyi nace maka a'a, duk yadda kace haka za'a yi muje kawai ta yunkura ta mike tsaye tasoma tafiya ya riko tafin hannuta ,tare da janyota ya  manneta da kirjinsa ya d'aura  hannunsa daya  Kan cikinta daya soma fitowa yana shafawa  ahankali kana ya lumshe idanunsa " my love ina matukar son bby nan ,ina jinsa tsaye cikin raina ,ban sani ba kodan an sameshi a cikin wani  yanayi ne ?

ta d'aura hannunta saman nashi kana tace "A tunanina duk son da zaka yiwa wannan bby ba zai ta'ba kaiwa na nasreen ba ...
Yayi murmushi wanda ke sake fito da ainihin siffar kamalarsa ta cikakken namiji mai kyau da haiba ya sake gyara tsayuwarsa kana yace " haka ne  fa, nasreen daban take  acikin zuciyata ,ina jinta tmkr mahaifiya kanwa yayye da komai nawa ,itace duniyata, itace farkon farinciki Dana soma samu arayuwa ,Amman duk sa haka wannan bbyn ma ina jinsa araina.
"Ka rike nasreen na rike wannan bby ,kina sonshi saboda yadda samuwarsa takasance ko?
"Uhmmmm  "me'ad  tabashi amsa da hakan."ina son wannan bby ya zamto lafiyayyen namiji kmrka ,ya d'auko komai da komai irin naka  "har yadda nake chanis dake akan bed?
tayi murmushi tana sune kai "kiyi mgn mana.
tana murmushi tace "kwarai kuwa har dashi domin ina son matarsa taso shi fiyye da yadda nake sonka, saboda kai din jarumi ne ,sannan sadauki agurine ga rayuwata gabad'aya, ina alfahari da samun masoyi kmr ka, a kullun ina godiya ga allah daya bani ikon mallakar nmj daya tmkr da dubu, ina sonka mijina, ina fatan na mutu da sonka , sannan mukasance tare har aljanna mad'aukakiya ,ina sake neman yafiyarka ka yafe min abinda nayi maka abaya .
"nima hk  me'ad ina tsananin sonki
tun tuni nagane soyayyarki tana da Rana agareni , sam Sam komai zakiyi  baya kona min rai sai dai ya faranta raina , soyayyarki ce takore min tarin damuwata ada can baya , shinyasa a kwanaki da kika  dinga mun abubuwa na dinga  adana damuwata akan abubuwan da suka faru  "na yafe miki duk abinda kikayi min har da wanda zaki min anan gaba ni dai    yanzu "Dan Allah idan mun fita kiyi control  karki nuna komai ..
Jikinta yayi mugu mugun sanyi kwakwaluwarta tashiga tunanin ,"su waye hk da yake mata magiya akansu?
kiss ya sake manna mata a wuya " I love more than everything take tsigar jikinta ya tashi yanayinta yasoma sauyawa saboda abubuwan dayake mata ba duk mace zata iya jurewa hakan ba . muryarta a sanyaye tace
" I really love you too ,nasani honey kana sona sosai, kai ne hasken idaniyana farinciki rayuwata duk abinda kake so shi zanyi a yanzu sujjace kawai bazan iya maka ba, abban nasreen kaga ma min komai arayuwata.
Muje muyi attending bakinmu mu dawo  akwai special  darasin zan yi maka   mai mahimmanci  "Allah honey? "karki fa kisa tun yanzu na zauce
"idan ka zaune ba sani nima ka zautar dani ba " muje ta fad'i haka had'e da zare jikinta daga nasa ta kamo hannunsa.

'YANCINKIWhere stories live. Discover now