44

1.4K 18 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~ 

*my baby muwaddat Allah ya raya min ke bisa tafarkin sunnah*

page 93

..ahankali ya k'araso  ,yayi parking yana aika mata da wani irin shu'umin kallo me tattare da shaukinta, gefe guda kuma ,wani irin kishi ne from know where ya caki kahon zuciyarsa, ya fito a sukwane kmr wanda kwai ya fashewa aciki , ya k'araso ya mikawa direban dady hannu suka gaisa tare da cewa "a she kai ka dawo dasu?
direban yace "nine wallahi, ai d'azu ne muka had'u dasu a hanya, shine alhji yace idan na kaisu na tsaya na dawo dasu gida, gashi motar ma cewa yayi sajida ta rike, ta daina zuwa unguwa a motar haya.

khaleed najin hk sai yayi murmushi,yace "a'a amman an godewa dad'y "ya kalli inda sajida ke tsaye tana kallonsa a matukar tsorace yace "iye  ,kaga yar gatan dady, ji tayi kmr ta rungumeshi don murna, dan sam bata zataci zai amince da amsar motar ba  .

Khaleed ya koma motarsa ya ciro cak ya rubuta masa naira dubu ashirin , yace yaje bank  ya kar'ba, tukuici ne, yace "amman kar ya fad'awa dady cewar yabashi.

direban ya amsa yana godiya tare da cewa" to "
ya taho ya machine ya wuce yana murna ,su kuma suka shige cikin gidan  .
a lokacin sajida tasan har yanzu ita din wata ce  agurin mahaifinta  ,ita kuwa yanzu me zatayi masa ,baya ta zauna tare da khaled  tacigaba da rayuwa dashi muddin rai, tunda shine burin mahaifinta  yaganta a gidan aurenta tana rayuwa kmr kowace diyar sunnah.
  a daidai  tsakiyar zauren gidan khaleed ya tsaya had'e da janyota jikinsa,ya rungumeta ta juya ahankali ta tsura masa ido tana kallon cikin kwayar idanunsa  ,a kullun idan khaleed nayi mata wasu abubuwa ta kan yi mamakinsa, tabbas duk kankatar nmj kada mace ta rainashi koda kuwa ta ninka shekarunsa ne a haihuwa .
tsawon minti goma suna tsaye suna kallon junansu sannan ya bud'e baki da kyar yace " kece kika yiwa dady compalain ko.. ?
"akan me kenan kake magana akansa ?  "akan shiga motar haya mana ,i think yau shine Karo na farko da hakan takasance .....

"nasani amman yakamata kasan wani abu bani ce na gaya masa komai ba, "idanunsa ne suka gani, kuma koda zan gaya masa wannan shine karona, na farko bazai  yarda da hkn ba, amman idan motarce har yanzu baka bukatar na hau, ka fad'a min sai a mayar, dan ni tuni na cire  hawa wata mota acikin raina..

"ni isa na sake hana shalelen dady hawa mota idan baso nake na had'u da 'bacin ransa ba ."uhmmm sai dai idan bata raya maka ba, tana gama fad'ar hk ta juya tasoma tafiya shi kuma yana rike da kugunta yana aikin tsokanarta, sukaci sa'ar babu kowa a tsakar gidan yana rike da kugunta har bakin kofar umma yaja ya tsaya yana mata rad'a acikin kunneta .

dogon tsaki yaji an yaja ta bayansa wanda yasa sajida saurin shigewa cikin kuryar d'akin batare da ta tsaya ganin kowaye ba, shi kuma ya juyo ahankali , inda idanunsa suka sauka akan mahaifiyarsa dake tsaye rike da buta, suna had'a ido ,ta sakar masa harara tana takaicin wannan mannewar dayake sajida. "wannan jaraba har ina yaro na nacewa uwar mata hk , tayi mgnr acikin  zuciyarta tana sake banka masa harara batare da tace masa komai ba.
waskewa yayi ta hanyar shafa sumar kanshi yace "umma ina yini?
aciki ta amsa masa da lafiya  ta ajiye butar hannunta tashige d'akinta tana mita.
shi kuma yayi alwalar sallar magrib ya fice daga gidan.

bashi ya dawo gidan ba sai kusan takwas , d'akin aunty amarya ya fara shiga hannunsa rike da farar leda ,sai dai idanunsa baigane masa abinda ya shigowa d'akin dominsa  ba, dan haka bai yi sanya ,a gwiwa ba ya tambayi aunty amarya "ina sajida take?
"tana d'akin umma " tabashi amsa da hk "okay ya fad'a tare da ciro bakar leda guda biyu ya ajiye mata "ga nama nan ki d'auki d'aya kisa akaiwa hjy d'aya "to madalla  an gode Allah yayi albarka yace" ameen ya juya ya fita ya nufi d'akin mahaifiyarsa bakinsa d'auke da sallama inda ya iske parlour'n babu kowa sai karan tv plazma dake aiki acikinsa dan haka yashiga d'akin anisa inda yafi tunanin zai isketa ai kuwa can ya hangota kwance akan gadon ta rufa da bargo ,ta kudundune irin ba yadda ya saba ganinta ba, hakan yasa ya k'arasa shiga cikin d'akin da sauri ya ajiye ledar hannunsa ya hauro saman gadon tare da motsowa kusa daita ya yaye bargon data lulluba dashi yayi kasa, ya kai tafin hannunsa ya ta'ba wuyanta ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sakamakon jin temperature dinta ba kamar yadda yasaba ji ba, jikinta ya d'anyi zafi ,hankalinsa a matukar tashe ya kai fuskarsa daidai nata yashiga busa mata iskar bakinsa ,ahankali tasoma bud'e idanunta har ta bud'esu fess ta tsura masa kwayar idanunta  tana kallonsa durkushe agabanta.

'YANCINKIWhere stories live. Discover now