40

1.4K 27 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
*hajiya maryam jikar kulu*

Page 89

......numfasawa malam isa yayi had'e da sauke naunayen  ajiyar zuciya,still yana duban dady dake fuskantarsa .
A hankali malam Ibrahim shima yashiga  janyowa dady  ayoyi da ingantatttun hadisan dake raunata zuciyar d'an adam da duk inda ya kai ga kangarewa ,
take jikin dady yayi mugu mugun sanyi ,idanunsa suka kad'a sukayi jajir, nadama ta shigesa mara misaltuwa, sosai sukayi Masa ruf da dugu gurin lalasa zuciyarsa har suka samu  zuciyarsa ta sauko gabad'aya ya amshi wa'azinsu da hannu biyu biyu  wanda  ad'azu  yaso yayi musu taurin kai .
cike da matsananncin  nadama dady yace  "shikenan na yarda na amince ta koma garesa su cigaba da rayuwar aurensu, amman kusani bafa zan ta'ba son fu'ad acikin zuciyata ba.
saboda shi wannan son halitta ne da Allah ke hallatawa bayinsa acikin zukatansu ,to ni sam sam    ba'a halitta  min soyayyar  fu'ad acikin tawa zuciyar ba . sannan koda ina son fu'ad wannan soyayyar ba zatayi tasiri ba, sakamakon abinda diyar cikina tayi min akansa, ta fifita shi akaina, tayi sa'insa dani akansa.. to ta yaya kuke tunanin zuciyata zata iya soyuwa da soyayyarsa?
  "kar kace haka alhaji  akwai kyautatawar dake saka shakuwa mai ilhama  har ta zamo soyayya mai karfi ,yaran wannan lokacin daban suke akan makauniyar soyayya ....
zasu iya komai akan abinda zukatansu ke so, hakuri zamuyi dasu tare da yi musu addua , kama godewa Allah da ban d'an  iska dan shaye shaye takawo maka gida ba, sam sam wannan yaron bash wani laifi ko aibun da za'a ki bashi mata ya aura, saboda yana da nagarta data dace illar dai rashin sonsa da bakayi ,amman dai kayi hakuri a hakan ma mun gode kwarai da gaske daka fahimcemu   .
,Allah ya k'ara sanyaya zuciyarka, su kuma Allah yabasu zaman lafiya mai d'aurewa ,abu na karshe da zance anan shine kayi hakuri ka rage kiyayyar yaron acikin zuciyarka, domin annabi muhammadu saw yace idan zaka ki mutun ka kisa kad'an  saboda wata rana zai iya zama masoyinka, haka zalika idan zaka so mutun kaso shi kad'an saboda wata zai iya zama makiyinka. mlm isa na gama fad'ar haka suka mike tsaye atare shi da mlm Ibrahim suka yiwa junansu misabaha sannan suka  fice suna sake tautaunawa akan lamarin dady atsakaninsu  .

bayan tafiyarsu shiru dady yayi zaune agurin kwakwaluwarsa na dawo masa da abubuwan da suka faru a baya da kuma wad'an da suka faru a yanzu, bai ta'ba tunanin zuciyarsa zata raunana a daidai wannan lokacin ba, sannan bai ta'ba sanyawa ransa zai amince da komawar me'ad ga fu'ad ba, ya dad'e zaune  agurin yana tunani yana girgiza  kafarsa daya ,zuciyarsa tayi masa nauyi , yasoma tunanin ta yadda  zai fahimtar da safwan ya fahimcesa batare da wata damuwa ko tashin hankali ba ,gabadaya zuciyarsa tagama karanto masa ya nasanar masa da komai kawai Amman sai  bayan me'ad din ta koma gidanta ,da wannan shawarar yasamu natsuwar zuciyar daya yunkura ya Mike tsaye yashige d'akinsa.

bangaren me'ad kuwa ita sam batasan da zuwan baki gidan ba, tana kwance lamo akan gadonta kiran Dubai max-zoniya,ta lullu'ba cikin laulausar bargo ,iya kanta ne kawai a waje idanunta na kallon saman d'akin tana tunanin mai tattare da kewar mijinta da tilon diyarta mara ishashiyar lafiya,"ko a wani hali nasreen da fu'ad dinta suke ?
Ta lumshe idanunta  ahankali sakamakon gefen kanta dayayi mata nauyi  kmr kowani lokaci idan ta zafafa tunaninta akan fu'ad da nasreen.
    idanunta sun kad'e sunyi jajir  tsabar kukan datake akan rashin sanin madafar rayuwarsu  da rashin sanin takamaiman halin da fu'ad da nasreen  suke ciki .
Suhailat ce tashigo d'akin kawo mata abinci ta tsaya daidai saman kanta "ya dai ?
"Lafiya aunty ko wani gurin ke miki ciwo ?
Kallon kanwar tata tayi inda take ganinta dishi dishi ,"wallahi  hailat da ba Dan kar nayi sa'bo ba Dana ce  nagaji da rayuwar duniya, da abubuwan dake faruwa dani ,narasa me ke damun zuciyar dady...
Komai ya tsaya min banasamun sukuni da walwalar zuciya, bazance miki when Dana tsinci kaina cikin farinciki ba ..suhailat ta ajiye tiren hannunta akan bedside sannan tace  "Kiyi hakuri aunty ki d'auki wad'an nan abubuwan dake faruwa dake amatsayin kaddararki,   da sannu komai zai zo ya wuce ,kin kuwa samu abban nasreen a waya kuwa ?

'YANCINKIWhere stories live. Discover now