💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
JIDDATULKHAIRI
MARUBUCIYAR
MATAR DATTIJOPage 79
......Jikinsa ne yacigaba tsuma , kansa gaba ɗaya ya kulle, yayi mamakin jin abinda mai gidansa ya fad'a mishi, hankakinsa gaba daya yagama tashi ,xuciyar sa ta shiga rud'ani, "wai me surukin nashi yake nufi da shi, ?
"wane irin zato surukin nasa yake masa, ?
"me yasa ya gwammace kar'bar auren sajeeda alhalin lokacin da zai aure me'ad kin amincewa yayi ? Tambayoyin da ya rika yiwa xuciyarsa kenan .
"Yasan zai yi hkn ne Dan kawai ya bak'antawa me'ad rai .. ..A fusace ya mike zai bar parlour'n, cikin natsuwa mai gidansa ya kira shi "fu'ad ina zaka je haka,? Tsayawa yayi yana haki batare dayace masa komai ba .
" me yasa naga yanayinka gaba daya ya canja? Dawo ka zauna"A hankali cikin nutsuwa fu'ad ya dawo ya zauna yana fuskantar mai gidansa. "Gaya min menene damuwar ka fu'ad, naga daga yin wannan Maganar gaba daya ka canja daga farin ciki zuwa akasinsa, hankalinka ya tashi damuwa ta bayyana a idanunka, fad'a min idan akwai wata matsala ne musan yadda zamu shawo kanta "
Sunkuyar da kai fu'ad yayi sannan ya fara yin magana cike da ladabi da girmama ga mai gidan sa
"Yalla'bai shi fa wannan mutumin da zai kar'bi auren sajeeda ba kowa bane face mahaifin me'ad"Wani irin shock mai gidan nasa yayi lokacin da yaji wannan maganar, "mahaifin me'ad fa ?" Ya maimaita yana kallon fu'ad cike da neman K'arin bayani
"Kwarai kuwa yalla'bai mahaifin me'ad ne ,"Abinda yake ƙara d'aure min kai shi ne ta yadda zai yi ya amshi auren sajeeda alhalin a da can baya lokacin da xan auri me'ad 'ke'kashe ƙasa yayi yace baxan aureta ba, to yanzu kuma wane dalili ne zai sa ya amince na auri sajeeda tabbas nasan akwai wata manufa a cikin zuciyar shi".
Shiru mai gidansa yayi yana nazarin Wad'annan maganganun da fu'ad ya fad'a masa, bayan sun kammala maganar da zasu yi ne suka yi sallama fu'ad ya tashi ya bar me gidansa zaune yana mamakin abinda ke shirin faruwa.
Yana fitowa harabar gidan Motar shi ya bud'e ya shiga sai yaji kamar baxai iya yin driving din ba saboda wannan Maganar da aka yi masa ,tambayar kansa ya shiga yi me Mahaifin me'ad yake nufi da wannan batun da da'akazo masa da shi da rana tsaka, ?
tunani ya rika yi gami da nazari, ba ƙaramin caji ƙwaƙwalwarsa ta rika yi ba a haka har ya isa gida wanka yayi ya sake fita neman me'ad sai bai samu ganinta bai yi tunanin zuwa gurin aikinta ba ,saboda yasan halinta ,kad'an daga cikin halinta su siyar da hali agurin shi kuma abinda bazai so faruwarsa kenan ba .A ɓangaren me'ad kuma, har yanzu tana fama da matsalar da ita kanta bata san asalinta ba, ba kuma ta san dalilin da yasa ta tsinci kanta a wannan halin ba,sannan har wannan lokacin bata daina tunanin hakunci da chairman din office din su ya fara tunanin yanke mata ba ,ta hanyar dakatar da ita amma sbd kwarewar ta ga iya aikin da jajircewa wajen tsayawa tayi aikin yadda ya kamata yasa ya d'aga mata kafa gabadaya ta fige ta rame tafita haiyacinta ban da kuka babu abinda take ..
Hankalinta kullun sake tashi yake ganin yadda kullum matsalarta gaba take yi bata baya ,hkn yasa ta sake dagewa da addu'a da sadaka da kiyamullaili a kan Allah ya kawo mata karshen wannan matsalar da take ciki, duk da wannan jajircewar da take wajen addu'a da sadaka still dai har yanzu bata iya xama a office dinta domin gudanar da aikinta kamar yadda yakamata ,yayinda tsakanin su mudansir da tahir amintarsu ta dawo sama sama ko nace ta kusan Yankewa, saboda kusan kowa yanzu harkar gabansa yake sai dai a kasan zuciyar mudansir yana jin cewar bazai iya barin tahir hk ba sai ya bisa da bita da kulle.
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.