💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)page 61 to 62
washegari har karfe 11:00 na safiyar ranar me'ad bata fito daga cikin d'akin ba, tana kwance akan gadonta tana kuka, tare da tunanin maganganun fu'ad akan safwan,ahankali komai ke dawo mata daki daki, "ita ba rabu da safwan din ne bazata iya ba ,illa tashin hankali dashi fu'ad yake ciki, tana son shi bilhaki da gasky ta yarda ta amincewa zuciyarta ko bai da sisin kobo zata auresa tayi rayuwa dashi,cikin wannan tunanin zazzafan zazzabin da yayi kokarin kamata tun yammancin jiya, ya saukar mata take jikinta ya d'auki kyarma tmkr mazari, shiru shiru momy bata ga saukowarta ba har sun gama break fast,yasa momy cewa suhailat taje ta dubota anya kuwa lafiya take,da har yanxu bata sauko ba?" Duk da week end ce amman bata ta'ba kaiwa wannan lokacin bata sauko ba.
suhailat dake zaune akan kujera tana assign din da'aka basu a makaranta, ta ajiyei litafin hannuta ta nufi d'akin me'ad, da sallamarta tashiga amman shr ,Dan haka tayi kokari k'arasa shiga d'akin ,nan ta isketa can karshen gadonta kudundune cikin bargo tana rawar d'ari da sauri ta karasa" aunty me'ad lfy yau baki fito ba?
cikin dasashiyar murya tace "hailat sake rufa min bargon can sanyi make ji sosai ,a raunane suhailat tace "sanyi aunty? a wannan uban zafin da'ake ko dai baki da lfy ne? dan kusan ruwa jiya da'akayi tadda zafi yayi .
ta kasa ce mata komai illa lumshe idanunta datayi takaraso ta d'aura hannuta akan goshinta zafin daya kaiwa tafin hannuta ziyara ne,yasa tayi saurin cire hannuta wuyanta ta ta'ba nan ma zafi rau kmr an jonata da wutar lantarki.
da sauri ta fita daga d'akin ta gayawa momy ai wata uwar zabura momy tayi tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun atare suka dawo d'akin momy ta hau saman gadon duk ta rud'e tare da rungumota jikinta"bakida lfy me'ad shine ko waya bazakiyi ba ki sanar?
" sai ki zauna ke kad'ai cikin d'aki idan wani abu ya faru dake fa, me kike tunanin zai samemu..?me'ad tayi shiru taki mgn sai numfashi take fitarwa ahankali ahankali jikinta na sake d'aukar kyarma "ke suhailat d'auko mukulli mota muje hospital sai sannan me'ad tayi mgn da kyar "no momy kibani paracetamol kawai ya isa ba sai muje koina ba "its just tension...... momy da suhailat suka kmr zasuyi mata kukan halin tashin hankali datake ciki, sannan suhailat taje ta had'a mata ruwan wanka da taimakon momy ta iya yin wanka aka kawo mata breakfast,hadaddiyar jolof din Shinkafa dataji nama kasa zuku zuku byn ta fito daga wanka momy da suhailat suka sata atsakiya da roko da rarrashi sannan suka samu taci hawaye nabin kuncinta sannan suka tsiyaya mata ruwan roba mara sanyi acikin cup ta amsa tasha magani ta koma ta jingina jikinta da abun gadon, ta runtse idanunwata gam zuciyarta na buguwa daf..daf..suhailat ta fita daga d'akin amman sam momy ta kasa fita tabar diyarta cikin halin damuwa dan tasan ciwon diya mace na diya mace ne.
"me'ad momy taki kira sunanta a sanyaye "kibi ahankali karki bari wata cutar ta kamaki , lamarina zaki duba ba dady dinki ba, ku biyu gareni acikinku bana son na rasa ko daya ahannuna....
"akan aurenki da fu'ad ni dai na yarda na amince kuma ina farinciki dashi ,sai dai amatsayina na mahaifiyarki ina baki shawara kiyi addua akan lamarin, matukar rabonki ne fuad zaki auresa."sai dai ki duba wani abu guda acikin matsalar nan mahaifinki yafi karfin komai agurinki mead yana sonki yana son farincikinki,sai dai yafi son da bukatar auranki da safwan," me zai hana ki hakura da fu'ad ki auri zabinsa domin zaman lafiyarmu gabadaya...
ta bud'e idanunta da kyar ta saukesu kan mahaifiyarta dake zaune kusa daita, muryarta na rawa ta fara magana "momy me yasa daddy yake kin talakawa ne?
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.