28

1K 26 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
FAIZA HAMMADU BARAU
         (YAR NUMAN)

Page 76 

........ wani irin k'ara ta saka tare da d'aura hannuwanta duka saman kanta "shikenan tawa tasameni nasreen Dina  zata mutu  tabarni ...."wayyohlly nasreen ki taimaki mamanki ki tashi karki ki mutu kubarni cikin wannan halin damuwar danake ciki ,idan kika mutu wazan kama  naji  dadi? "wayyohlly Allah,"nashiga uku nah ... "help me to carry her to hospital this man, ka tashi ka  wani zauna kana kallonta saboda kasan idan ta mutu baka da hasara zaka  kuma samun madadinta ni kuwa fa wazan kama...?
a rud'e fu'ad ya d'auki nasreen da bata numfashi ya sa'bata akafad'arsa yasoma tafiya daita cikin sauri sauri, me'ad ma ta mike azumbur ta biyosa abaya rike da gefen rigarta tana wani irin kuka me ta'ba zuciya.
A haukace ya isa inda motarsa take parke ya bud'e gidan baya ya kwantar daita, me'ad tayi saurin shiga ta d'aga kanta ta zauna ta meida kanta saman cinyarta tana wani irin kuka jikinta banda kirma babu abinda yake ,shi kuma ya zagaya cikin sauri yashiga gaban motar ya zauna ya kunna motar yana mai danna  hon da karfi ........
me gadin gidan da tun sanda rikicin yasoma  faruwa akan idanunsa yashige d'akinsa ya boye ya leko ta window, ganin motar fu'ad ne yayi saurin fitowa ya bud'e masa get sannan fu'ad ya figi motar aguje ya bar gidan .
wani irin gudu yake shararawa akan titi wanda yaja hankalin  mutane dayawa kansa ,domin duk wanda yaga irin gudun dayake sai ya tsaya yabi bayan motar da kallo, cikin lokaci kankani ya isa asibiti tun  bai gama daidaita tsayuwar motar ba me'ad ta fito jikinta na rawa tana ihun kiran  nurse....nurse!! shima ya fito a kid'ime batare daya tsaya rufe motar ba, ya sake d'aukar nasreen dake kwance babu alamun numfashi atare daita.
sautin muryar me'ad yasa
wasu daga cikin likitoci  fitowa da hanzari suna tura gadon marasa lfy domin sunsa duk me irin ihun nan hk a matukar bukace yake da taimako,batare da 'bata lokaci ba aka kwantar da nasreen.
kai tsaye d'akin likita aka nufa daita aka akwantar daita akan gado sannan aka soma bata taimakon gaugawa ,likitoci kusan guda biyar ne suka rufa akanta domin k'ok'arin dawo da numfashinta ,wanda da kyar aka samu numfashinta ya dawo daidai sai dai bata farka ba.
Yayinda fu'ad da me'ad  gabadayansu sun fita haiyacinsu ,sai zariya suke suna kai kawo a reception, most especial me'ad da hawaye yaki tsayuwa acikin kwarnin idanunta, kuka take sosai kmr wace akace mata tarasa nasreen din, ahankali fu'ad ya waigowa gefen datake zariya tana kuka ya tsura  mata ido yana duban yadda gbdy ta gama birkicewa  ta hargitse ta dawo abar tausayi ,matsalarta kenan a duk sanda nasreen ke cikin wani hali gbdy zata rasa sukuni da kwanciyar hankali Amman ta zauna domin kula daita da lfyr ce bazata iya ba ...
ahankali ya d'auke idanunsa akanta had'e da Jan tsaki... shi kansa cike yake da matsanancin fargabar abinda likita zai fito ya sanar musu,cikin hk  suka  hango fitowa wata nurse   daga d'akin da'aka  kwntar da nasreen ,gbdy sukayo kanta "how is she?
suka furta atare cike da matsanancin tashin hankali?
"she's feeling better now ta basu amsa atakaice cike da tausaya musu sannan tacigaba da mgn "doctor is already attending to her,  Dan haka kusamu natsuwa ku kwantar da hankalinku InshaAllahu babu abinda zai  faru da yarinyar ku....."you said doctor is with her  inji cewar fu'ad?"haka ne likita nabata kulawa just keep praying for her, everything will be fine okay.
sannan ta barsu tashiga wani d'akin opposite dinsu.
suna nan tsaye ta sake dawo ta wucesu cikin sauri tashige d'akin .
me'ad ta k'arasa jikin bango ta d'aura kanta tana wani irin kuka ..., sai alokacin abubuwa suke dawo mata daki daki , "sajida aminiyarta, aminiyar datafi yarda daita a duk cikin aminanta, wai itace yau aka wayi gari take son mijinta har take burin mallakar aurensa, wannan wace irin cin amana ce ...?
"Sajida kin cuceni kin ci amanar yarda da amince dana miki ,kin cuceni kin yaudareni, kin ha'inceni.. Amman nasan Allah bazai barki haka ba ,da yarda Allah sai allah ya nuna miki illar cin amanar wanda ya aminta da dake , matukar yarda  da na miki ta tsakani da Allah ce sai Allah ya nuna miki atafin hanuna, saboda daidai da rana daya ban ta'ba tunanin zaki yi min hk ba ,na yarda dake kin cutarda dani ...na aminta dake kin ha'inceni "me na miki kika za'bi ki min haka?
"Duk duniya ki rasa wanda zaki so sai mijina..kuka take sosai tana maganar ashe har maganar ta fito fili batasani ba .
Tausayinta ne yashiga ratsashi ,da bin lungu da sako na sansar jikinsa  , jiki a sanyaye yak'araso zuwa inda take ya kai hannunsa ya dafa kafad'arta, da sauri tayi wata irin juyowa  tana kallonsa cike da zallar tsana da 'bacin rai sannan ta cire hannunsa tayi jifa dashi "karka sake kai hannunka jikina mayaudari maci amanar kauna.......abinda ta iya fad'a kenan ta bar gurin zuwa harabar asibiti tana kuka kmr wata zautaciya..." yau tazo mata da abubuwa daban daban wanda kowane daga cikinsu akwai d'aci da muni gareta, mijinta ke son me aikinta da aminiyarta.... alhalin tana raye bata mutu ba wannan abu da matukar ciwo .."why fu'ad ?"ban cancanci hk daga gareka ba ,bansa zaka min haka ba ,Amman tunda wannan shine besty solution dakake ganin zaka d'auka akaina I will live you for them wallahi na hakura da kai nabar musu kai ta karasa mgnr tana kuka ahankali ta durkushe kasa tare da d'aura kanta saman gwiwowinta tacigaba da kuka .....

'YANCINKIWhere stories live. Discover now