30

1.1K 29 1
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
FAIZA HAMMADU BARAU
         (YAR NUMAN)

Page 78

........tsaye tayi acikin bathtub din ,ruwa na  tsiyaya akanta zuwa sansar jikinta,Wanda ke saukar mata da natsuwa kad'an saboda    har wannan lokacin bakinciki abinda sajida da fu'ad ke shirin yi mata, yaki barin zuciyarta da gangar jikinta, "ta yaya zata iya sharing din fu'ad dinta da wata macen ,macen ma aminiyarta da suka taso tare... ?
"Suke yin komai nasu  tare sannan babu abinda bata sani ba na sirrukan rayuwarta....
"A gurinta Fu'ad ba kmr sauran maza bane ,daban yake acikin mazan datake kallo , sannan natsatse ne kamili Wanda yasan ciwon kansa ,tana son shi fiyye da rayuwarta sai dai bata jin zata iya ganinsa yana rayuwa  tare da wasu matan byn ita,tafin son duk runtsi duk wuya su kasance tare suka k'arasa rayuwarsu .
Ahankali take tuna moment dinsu dashi ,duk da ba wani  bashi had'in kai  takeyi ba  ,amman hkn baya hanata jin dadin abinda yake mata. "Anya kuwa zata iya rabuwa dashi kmr yadda ta fad'a tayi rayuwarta ita kad'ai sai yarinyarta?
"Anya kuwa ba wata cutar Kan zata sake yiwa rayuwarta ba ?
Tayiwa kanta tambayar tana jin jikinta yana sauyawa, ahankali take jin feelings dinsa na bijiro mata  duk da bata tsamaci zata ji hkn ba akansa, a wannan tsayuwar datake komai na rayuwarsu  ke dawo mata  daki daki cikin kwakwaluwarta  ,yanzu ace agida ne kuma suna zaune lafiya dashi  zai  shigo bayin ,ya tsura mata kyawawan  idanunsa masu maseefar burgeta da tsaya mata arai ,yana kare mata kallo ko kifta idanunsa baya son yi daga karshe kuma ya k'araso gareta  ya riko kugunta yana me had'eta da jikinsa tare da shafa kirjinta yana goga mata gashin dake zagaye da fuskarsa zata lafe akirjinsa , koda kuwa bai yi niyyar yin wanka ba ko kwanciyar aure daita ba ,ganinta tsaye babu kaya  zai janyoshi  yayi koda kuwa acikin bayi ne yayinda ita kuma zata shiga  tutturesa tana kukan shagwaba ita tagaji bazata iya da jarabarsa Amman ba zai  ta'ba  kyaleta ba har sai yacima burinsa akanta duk yadda tayi ta yakice tunaninsa abun yaci tura haka tayi ta tunaninsa ..

ganin tunaninsa daya d'arsu a zuciyarta yaki barin tayi abinda  yashigo daita ,yasa ta sauke  naunayen ajiye  zuciya  sannan tasoma  sa'bawa jikinta sabulu ,sai dai duk inda ta gogo sabulu ajikinta  sai taji kmr tafin hannunsa ne ke yawo ajikinta Dan haka tayi
Shap shap tayi wanka ta d'auro alwala ta fito ,koina a d'akin ya kama  kamshi room freshener da'akayi amfani dashi  .
   jakar kayanta ta bud'e ta ciro doguwar riga ta sanyawa jikinta ta k'arasa inda pray mate yake ta tada sallah byn ta idar da sallah s ta janyo akwatin kayansu ta fiddosu daya bayan daya tasoma jerawa cikin wardrobe nasreen na tayata miko mata, wasu suna hirarsu cikin farinciki duk da ita ba wai  nufinta tayi hkn ba ,Amman ya zame mata dole ko dan kwanciyar hankalin diyarta da lafiyarta  ,batayi sha'awar kunna  makeken TV dake makale da bangon d'akin ba ,Amman   saboda ta d'bewa nasreen kewa yasa ta tashi taje ta kuna  ta dawo tacigaba da aikin jera kayan.

byn tagama jira kayansu ta tmbyi nasreen ko zata ci abinci Dan ita bata jin cin komai ,yarinyar tace " ba yanzu ba sai zuwa anjima momy , Dan kafin me'ad ta yanke shawarar zuwansu hotel ta sai mata snacks taci a mota .

Kwanciya tayi akan gadon tabar nasreen na kallo ,ahankali ta runtse idanunta domin ta samu hutu da natsuwar zuciya, Kafin lokacin sallar magri tayi ,tunanin mijinta ne ya sake  sanyo kai cikin zuciyarta dama gangar jikinta, wani irin sabon yanayi ta tsinci gangar jikinta ciki yayinda wani feelings dinsa yashiga bijiro mata idanunta har sun sauya, da kyar tasamu ta yakice shi ta Mike   ta janyo system dinta data  jona a caji ta kunna tasoma dudduba sakonin da aka turo mata ,cikin haka kiran chairman din company din datake aiki yashigo wayarta, take gabanta yashiga dukan uku uku ,da kmr karta d'auka Dan bata son K'arin tashin hankali akan Wanda take ciki ,ammam ta sanshi tasan halinsa shima ba kwanwar lasa bane ,Akan company dinsa babu abinda bazai iya yi ba ,Dan HK tayi saurin sanyawa  jikinta kuzari ta d'auka ta manna wayar a kunnaneta tana gaisheshi a natse ya amsa tare da cewa "muna bukatar ganinki gobe by 10 :am atakaice tare da katse kiran ,jikinta yayi sanyi kmr wace akayiwa wanka da ruwan sanyi ,gbdy takasa cigaba da operating system din dake gabanta, ta ture system din gefe ta janyo nasreen ta rungume ajikinta hawaye na gangarowa daga cikin kwarnin idanunta ,"jikinta na bata aikinta ya kusan zuwa karshe.....har aka kira sallah magariba tana makale da nasreen tana jin karfin gwiwa a duk sanda ta rungumeta yayinda take cikin damuwa,ahankali ta zameta daga jikinta ta kwantar a saman cinyarta ta tsura mata ido kawai tana kallonta wani irin kaunar yarinyar nabin jikinta bacci take har lokacin tana sauke numfashi ahankali, ta Mike ta tashi taje tayi alwala bayan ta idar da sallah bata tashi ba tacigaba da zama  tana lazami tarenda kaiwa Allah kukanta.
*********
Misalin karfe tara na dare mumy ta samu dady ad'akinsa cikin yanayi na rarrashi take ce masa "dady sam  abinda kayi bai kamata ba ,yakamata kabi komai ahankali hannunka baya ru'bewa kace zaka yanke ka yar duk abinda me'ad tayi maka duk lalacewarta  bazaka ta'ba canzata amatsayin diyarka ba ,kalaman daka furta mata a yau  din nan yayi muni dayawa.....
  dady yasoma magana cikin 'bacin rai  "ina amfaninta arayuwata?
"Meye amfanin D'an da bai jin maganar iyayensa da yi musu biyayya?
"Ni tsine mata ma naso yi tabi uwa duniya kowa ya huta ,dady yana fad'ar hk numfashinsa ya fara sama sama sai faman haki yake ,mummy tana ganin hk ta fara salati game da waige waigen  Kafin kace me tuni dady ya fara fita haiyacinsa ,mummy tayi matukar rud'ewa sakamakon numfashinsa daya tsaya a matukar gigice ta kwallawa suhailat kira itama tashigo d'akin a rud'e tayo gurin momy dake  jijigasa , tare da taimakon sulahait suka dawo da dady parlour'n, ruwa sanyi mummy ta dinga shafa masa sannan ya dawo haiyacinsa  ya jike sharkaf da ruwa  kwance ya ganshi ajikin momy wacce idanuwanta tuni sun dade da yin luhu luhu saboda kuka, dady ya d'ago idanunsa ya kalli momy da take faman tofa masa adduoi, da kyar dady  ya iya bud'e bakinsa "wai ,abinda nake tunanin ne ya  faru..?

'YANCINKIWhere stories live. Discover now