💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)page 74
.....sunkuyar da kanta tayi kasa sosai ,sannan ahankali tasoma takowa zuwa inda yake zaune xuciyarta na wani irin luguden bugu da karfi sakamakon idanunsa dataji suna yawo a gbdy sansar jikinta.
har tak'araso kanta na sunkuye akasa batayi kok'arin d'agowa balle ta samu damar kallon idanunsa dake tsare daita,cike da matsanancin sanyi jiki ta samu guri ta zauna a gefensa a takure tana fargaba kada uwar d'akinta tasameta zaune kusa da rabin ranta tashiga uku .
Tsawon minti biyar bai ce daita komai ba illa idanunsa datake ajikinta, jin shirun yayi yawa ne yasa najma tace "zan iya tafiya saboda tsoro nake ji wallahi.....
wannan furucin nata yasa fu'ad yin firgigib dan ya tafi duniyar tunanin ya saukar da numfashi da kyar yana lasar lips dinsa na kasa sannan yace "uhm dama so nake in miki wata tmby, da fatan zan samu gamshiyar amsa?Muryarta na cracking tace "kar..karka damu kayi duk wata tambayarka sai dai wallahi a matukar tsorace nake takarasa mgnr kmr zatayi kuka ......
"Ki saki jikinki babu abinda zai faru, kafin nace komai yaya sunanki?
"sunana najma ta fad'i hkn tana sake dukar da kanta kasa sosai dan gabadaya wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki da bata ta'ba jin irinsa ba.
"najma ya sake maimaita sunan acikin zuciyarsa ,saboda dad'insa da yaji , muryarsa a tausashe yace "amman ba real name dinki bane ko......?
"uhmmmm hauwa shine asalin sunana"ok hauwa nayi matukar mamakin dana ganki a cikin irin wannan yanayin wanda sam bai dace da yarinyar k'arama kamarki ba, Amman sai gashi na tsinceki acikinsa."karka damu da yanayin daka ganni ciki domin duk rayuwar 'yan gidanmu a haka ta faro, kuma babu mamakin a haka zamu k'are muna aikin bauta Dan tallafawa rayuwarmu, najma ta fad'i hk cikin murya mai rawa ala'mun tana son yin kuka.
fu'ad yaji ya sake narkewa akan kogin tausayinta, dan kamarta kamata yayi ace tana tare da iyayenta ko tana makaranta gurin d'aukar darasi, ko kuma tana d'akin aure amman yanzu gata a wulakance tana aikin bauta a inda bai zama dole asan yancinta ba .
Hakika talakawa na matukar shan wahalar rayuwa, idan ma sun dogara da karatu, sai suyi karatun su gama aiki ya zamemusu wata jarabawa ta musamman me tsananin wuya....
Najma ta matsu ya sallameta kafin me'ad tasanyo kai ta iskesu tare Amman yaki bata dama sai ma idanunsa da tsura mata yana kallonta..
sautin muryar me'ad taji ta kwalla mata Kira dan haka a matukar zabure ta mike tsaye ta fita aguje ta nufi inda take ,dan wani irin maseefaffen tsoron me'ad din takeyi kmr rai da ajali, fu'ad yabi bayanta da kallo cikin tausayawa har ga Allah yake jin tausayinta wanda kusan da wannan zuciyar ya taso na tausayawa talaka 'yanuwansa ,Sam arayuwarsa bai ta'ba zai aure diyar me kudi ba sai ta Allah takasance dashi ya rikitacciyar matarsa.Tana isa gurin me'ad wata uwar harara ta banka mata "dan ubanki me nasaki kiyi da kika je kika zauna ko kin tsaya kalle min miji ne yau ma?
da sauri najma tace "wallahi aunty ban kalleshi ba shi... "yi min shiru zaman uwar me kika tsaya yi kmr keda gidan ubanki wannan talaka........."talaka ai mutun ne mai godiya ga duk yanayin daya tsinci kansa dan yafi mai yin zamba cikin aminci sau d'ari, kuma yadda gidan nan bana ubanta bane kema haka zalika bana naki uban bane, dan haka babu wani me tutiya dashi balle har wani ya gorantawa wani....
tare suka juyo me'ad da najma duk da me'ad tasan mai yin wannan maganar amman ta kasa hakuri gara dai ta juyo ta sake tabbatarwa zuciyarta.
fu'ad ne tsaye kafin daga baya yakaraso zuwa inda suke fuskarsa a d'aure ..ya Matso gareta kmr zai shige cikin jikinta ya kai bakinsa cikin kunnenta.
"Yarinya zaki gane kuskurenki da kuskuren abinda kika shukawa idan lokacin hkn ya kusa yayi mgnr kasa sosai ta yadda yasan ita kad'ai ce zataji abinda yace .
me'ad tayi shiru tana kallon fu'ad abinda bai ta'ba mata ba kenan yi mata fad'a gaban kowa balle gaban me aikinta ,dan haka cikin 'bacin rai da daga murya tace "ke jeki kiyi abinda ya kawoki gidan nan da kika yi wani tsaye akanmu kina kallonmu kmr wata tsohuwar mayya......
najma da daman abinda take jira kenan ta bar gurin jikinta na rawa.....
YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.