34

1.2K 27 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  

*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI NE , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI  GARENI ALLAH YA BARMU TARE*🤝🏻🤝🏻🤝🏻

Page 83

........d'aya daga cikin abokan ango ne ke tsaye bisa kafafunsa rike da abun magana ,yasoma karanto tahirin khalid da makarantar da yayi ,har zuwa kan matakin da yake yanzu, inda yake  bayyana kwalayensa da matsayin na mataimakin sajida  .
yace "khalid uwar d'akinsa ya aura saboda kankaba da tsaurin ido  irin nasa gashin nan sai yanga da yauki ake masa .......
dariya gabadaya hall din ya d'auka tare tafa masa hannu  hamza yacigaba da magana kmr hk  "sai dai mu agurinmu  musan mace bata fi karfin namiji ba, matukar namijin  ya amsa sunansa nmj,da kuma yadda namijin yasan kansa  dan haka ta wannan fannin zan iya cewa abokina bayi tsaurin ido had'e da kankaba ba ......
aka sake kwashewa dariya "Allah yasanyawa rayuwar aurensu albarka yadda muka taru anan Allah ya hadamu mun zo suna haka .
mc ya amshi abun magana yana dry " ameen sai dai kuma gasky wannan abokin naka baiyi kankaba saboda kowa da irin ra'ayinsa  ..
 
Ita kuwa sajida tun da  ta zauna Kan kujerar da
ta ke mallakinta amatsayinta na amarya, hankalinta yasoma barin gangar jikinta, gabadaya tunaninta ya azzara ne akan burin zuciyarta," wannan karon ma irin zaman rayuwar datayi da emran zatayi da khalid kenan,
tayiwa  kanta mgnr  zuciyarta na kokawa ....
Dan a yanzu har tasoma hasasho yanayin zaman nasu  , Dan sam bata ji zuciyarta zata amince ta hakura ta amsa  rayuwa dashi amatsayin miji gareta .
a halin yanzu hankalinta a matukar tashe yake tana sake mamakin yadda khalid  ya makalewa aurenta dole, yayinda ga en mata nan birjik a gari da suka fita komai ,"ayanzu datasani take da bata zauna ta hakura da auren emran ba, ga kuma  abinda karshenta ya dawo ta bige da auren jinjiri "wace irin rayuwa ce hk ?
"wace irin kaddarar ce  haka ta giftawa rayuwarta?
gabadaya komai ya rigada ya cakud'ewa mata tarasa nemowa kanta mafuta "yanzu ya zatayi da rayuwarta?
sosai  tayi zurfi cikin tunani Dan kwata kwata ita zantuttukan hamza abokinsa baa shi ga kunnunwata ,hankalinta da tunaninta suna can ga fu'ad dinta ,tana jin ina ma wannan ranar ta kasance ranar aurensu ce da fu'ad dinta sanyin idanunta, hasken zuciyarta, lizamin rayuwarta ,bugun zuciyarta...
  "ina ma mafarki take, ba'a gaske bane duk abinda ke faruwa daita? har sanda khalid ya lalu'bo tafin hannuta cikin nasa  fuskarsa cike da matsanancin farinciki batasani ba  ,Yayinda ta koina acikin hall din murya mc ne ya karad'e gurin  ,inda yace "ana son ganin  ango da amarya a flow, waigowa Khalid yayi ahankali yana  dubanta fuskarsa na sake fad'ad'a farincikinsa.
Amman  ganin yanayinta al'amun tashiga duniyar tunanin yasa take murmushin dake fuskarsa d'aukewa cak zuwa wani malolon bakinciki da tarin damuwa, ransa yasoma 'baci zuciyarsa tashiga rawa rawa Dan ko  ba'a gaya masa ba yasan wani tunani take yi daban  wanda ba nashi bane .
  "shi kuma wulakancin da bazai  ta'ba lamunta dashi ba kenan yana zaune ana tunanin waninsa ,ransa a matukar  'bace ya kai  bakinsa  daidai saitin kunneta had'e  da tausasa muryarsa tmkr bai so yin mgnr  yace  "ke  tsohuwar kawai  kiyi maza ki  dawo cikin  haiyacinki da natsuwarki ana bukatar ganinmu yanxu Dan kin wani shantake atunanin iska .... tunanin abinda bazai ta'ba fissheki ba .....
yana gama fad'ar  hk ya mike tsaye tare daita yana kirkiro fara'r dole zuciyarsa a dagule, alokacin shi kad'ai yasan tashin hankali da zuciyarsa take ciki ..
Ahankali yake rike da hannunta yana tafiya  ,ita kuma tana biye dashi abaya masu d'aukar hoto da masu d'aukar video suka matso  kusa dasu sosai suka shiga  aikinsu ,na d'aukarsu har sanda suka sauko daga mazauninsu zuwa tsakiyar hall ,inda  mutane suka sake rud'ewa gurin d'aukarsu hoto, sauti na musamman aka sakar musu Amman sajida tayi tsaye ta kasa motsa koda D'an yatsanta ne ,ganinta sam bata ga wani  abun rawa ba......
Idan ma rawa zatayi ta rasa Wanda   zata tsaya yi rawa dashi sai Khalid ..?
"Ina  wannan abun kunyar ba da ita za'a yi ba ,ganinsa take agabanta tmkr mazuru ne agaban  zaki ....

'YANCINKIWhere stories live. Discover now