29

925 24 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  
FAIZA HAMMADU BARAU
         (YAR NUMAN)

Page 77 

......nasreen taji abinda momy'ta ta fad'a sarai amman taki motsawa daga inda take zaune, illa idanun data tsurawa momy'nta tana kallonta cike da tambayoyi.
ahankali Me'ad ta zagayo inda  take zaune tana kallonta "bby let's go now tana me kamo tafin hannunta ta fito daita daga cikin motar, sa'an nan ta meida murfin motar ta  rufe, tasoma tafiya rike da hannun ta.
  yayinda ma'aikatan gidan suka shiga gaisheta cike da girmamawa, hannunta kawai ta iya  d'aga musu tacigaba da tafiyarta batare da juyowa ba,
Momy tana zaune a parlour'n tana waya Me'ad tasanyo kai cikin parlour'n a matukar birkice bakinta d'auke da sallama, momy  na ganinta tayi saurin katse kiran saboda yanayin data ganta ,wujiga wujiga tamkar wace  tayi shekara tana jinya.
"me'ad lafiya kuwa naganki haka kmr wacce ta tashi a jinya?
"ko kuma kunyi Abind kuka saba ne da mijinki kika kwaso jiki zuwa gida?
momy tajirowa me'ad  wannan tambyar Tana dubanta a matukar tsorace me'ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune batare da tace mata komai ba, illa wani tashin hankali data tsinci kanta ciki.
NASREEN ta isa gurin momy tashige jikinta tana gaisheta ,momy ta rungumeta ajikinta tsam kana tace "ykk nasreen?
"yana ji jikin naki da zafi ko bakida lfy ne?
Naunayen ajiyar zuciya me'ad ta sauke kana tace "fitowarmu kenan daga hospital yau kwananmu uku NASREEN babu lafiya Tak'arasa mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka.
momy tayi Shiru tana kare mata kallo had'e da nazarin yarinyarta, a kallon da take mata ta fuskaci tana cikin matsananci damuwa da tashin hankali, yayinda ita kuma me'ad din tashiga share hawaye wasu na gangaro mata...

"To meye kuma abun kuka ?
" ko ciwon ne yayi tsanani?
Me'ad ta girgiza mata kanta wasu sabbin hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta.
"  meke damunki me'ad dan banji dadin ganin yanayinki ba ? " sannan meye damuwarki  ahalin yanzu da kike zubda hawaye ko duk akan matsalar ciwon  NASREEN ne?
ta sake girgiza kai kawai tana share hawaye, momy ta fuskanceta sosai hankalinta a matukar tashe "ke me'ad ki bud'e idanunki ,ki saka cikin nawa ni mahaifiyarki ce da duk  duniya  baki da kmr ni  kuma nice nazama dole nasan damuwarki da abinda ya kawoki gida adaidai wannan lokacin daya kamata ace kina gurin aiki ne ko gidan aurenki "ki sanar dani damuwarki da abinda ke damunki domin  Nasan mataki  d'auka..

me'ad ta kalli momy fuskarta cike da tsantsar damuwa da tashin  hankali still hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta tace "momy  ina cikin babbar matsala ,ina cikin damuwa da tashin hankali, momy na cuci kaina da kaina na yaudari kaina,na zalinci kaina, na jawo kaina maseefar datafi karfina.... Momy nayi aure batare da farincikinku ba ,most especial dady, banyi muku biyayya akan aurena da fu'ad ba , gashi ayau an wayo gari komai na neman  ta'bar'bare min, narasa gane komai nawa ,rayuwa na neman juya min baya , 
"ahalin yanzu na dawo gida ne saboda bana jin zan iya cigaba da rayuwar aure da fu'ad .......
jin wannan maganar yasa jikin momy yayi sanyi ta gyara zamanta tana duban me'ad cike da matsanancin  tashin hankali, sannan tace "amman  meye dalilinki na fad'ar duk  wad'an nan maganganun  hk  ?
"abinda akayi shi tsawon shekarun goma sha meye na dawo shi ahalin yanzu?
"sannan meye dalilinki na cewar bazaki sake rayuwar aure da fu'ad ba wani mummunar abun yayi miki ? Momy ta tambayeta jikinta na wani irin rawa haka zalika gabanta na fad'uwa ..

me'ad ta kalli momy ganin damuwa kwance akan fuskarta ,yasa wani irin tausayin mahaifiyarta ya saukar  mata, ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kwashe duk abinda ya faru  ta gayawa momy.

momy tayi wata irin zabura daga zaunen datake rungume da nasreen ta mike tsaye kana ta zaunar da nasreen  jikinta na d'aukar kyarma , dan maganar ta bugi zuciyarta matukar ,  ahankali tasoma kai kawo acikin parlour'n, lokaci guda kuma  ta koma ta  zauna ta kalli me'ad tace" yanzu ina najma  take sannan a wani hali Sajid take ciki?
"momy nagaya miki na barsu agidan ,dan tunda abun nan  ya faru ban sake taka kafata cikin gidan ba ,kinga sai suji dadin yin aurensu da tushe .
"shikena me'ad to yanzu meye abun yi?
me'ad tayi murmushi me tattare da takaici abinda sajida tayi mata ,sannan tace "momy kada ki damu ni nasan yadda zanyi   da Sajida ,wallahi Momy sai tayi datasani tunanin auren fu'ad arayu....

'YANCINKIWhere stories live. Discover now