13

953 28 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
      MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)

Page 51 to 52

.......kwance take akan makeken gadonta kiran italy tana kallon saman d'akinta ,sosai tayi zurfi cikin tunanin lamarinta da fu'ad tare da neman mafutar yadda zatayi, ahankali ta mike  zaune ta koma gefen gadonta ta zauna tare da lullu'be kanta da hannuwanta duka sakamakon bugawar da zuciyarta keyi akansa ,tamabayoyi tashiga jerewa kanta d'aya byn d'aya  "me yasa fu'ad yaki amincewa da tarin soyayyata garesa?"me yasa ya mareni akan nace ina sonshi? "Kodai Malik ya gaya masa abinda ya faru ne da hkn yazamo silar d'aukar fansa gareni ta hanyar disgani cikin bayanar nasi..."ga shan mari har uku ga rashin amincewa da soyayyata da bai yi ba... "yanzu ya zanyi da rayuwata ?  Ta sake jehowa kanta tmby.
" ina bukatar fu'ad arayuwata kuma zanyi komai akansa domin naga na mallakesa. wani abu ne data samu yazo wa zuciyata shine sake jin fu'ad datayi ajikinta yana yawo cikin jinin jikinta, tayi saurin goge hawayen da suka cicciko a kwarnin idanunta ya kawowa kuncinta ziyara, tasa hannunta ta dango d'igan  hawayen tana kallo "yau itace ke kuka akan nmj?"nmj ma d'an talakawa wanda ba kowa  bane...mikewa tayi ta isa gaban dress mirror dinta ta tsaya tana karewa kanta kallo daga samanta har k'asa "meye tarasa ajikinta kyau ne ko me da har fu'ad yake mata kallon ita bakowa bace?
Ahankali take karewa  cikar halitar da Allah yayi mata, tayi imani ko ita ta isa tasa fu'ad ya fuskanci lamarinta yasota fiyye da yadda take masa, sai alokacin ta lura da irin yadda gashin kanta data d'aure duk ya wargaje a saman kafad'unta  adalilin tunaninsa ,hannuta ta kai kan wayarta tasoma neman layinsa, Amman yaki d'auka, kasa hakuri tayi tacigaba da kiransa har sai data yi masa kira yafi sau goma bai d'auka ba sannan ta nemi layin malik kira daya biyu malik ya d'auka, bayan sun gaisa tace "malik kuna tare da fu'ad ne ka had'ani dashi?
" a,a ina gurin kallon ball, na dai barshi tare dasu kabeer a gida.

"Okay idan bazaka damu ba  zanyi maka wasu 'yan tambayoyi, amman ina bukatar jin gsky daga bakinka ."uhmmm ina sauraranki?

"Ka ta'ba  gayawa fu'ad abubuwa da suka dinga faruwa atsakaninmu da kai har zuwa kan marin danayi maka?
sai daya ja naunayen ajiyar zuciya ya sauke da kyar sannan yace"alahakikanin gsky wasu Abubuwan yasani sai dai batu na mari bai sani ba, dan ban gaya masa ba, wani abu ne ya faru da har kikayi tmby?

"Nothing  ,Amman yanzu wani  irin taimako zaka min malik akan abokinka?"na maseefar kwadaituwa da aurensa, ina son shi  sosai kuma zan iya yin komai akansa matsawar zan sameshi, ka taimakawa rayuwata malik nasamu fu'ad, nayi maka alk'awarin zan maka komai ciki kuwa har da samammaka aiki a karkashin ikona tunda shi yaki amsa daga gareni ..?

Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare kana yace "zaki iya mallakar zuciyar fu'ad cikin sauki dashi kansa gbdy, bisa dalilin abu daya da sauri ta katse Shi ta hanyar cewa"meye shi malik ka fad'a  meye shi zan iya yin komai akansa "meye zanyi fu'ad yasoni?

"Bawani abu bane daya wuce kyautatawa, fu'ad na matukar son kyautatawa ,da km kyautatawa wanda ya cancanta most especial mara shi,ina tabbatar miki matukar kika kasance daya daga cikin masu kula da kyautatawa zaki mallaki zuciyar fu'ad cikin sauki batare wata matsala ba, ni kaina ina miki sha,awar aurensa domin idan kika sameshi amatsayin miji ina me tabbatar miki zaki yi alfahari samun miji kmrsa "shikenan malik nagode sosai da shawararka, km InshaAllahu zanyi kok'arin naga na kasance cikin masu kyatatawa mutane, gobe karka  manta kasameni a oil and gas.

" InshaAllahu bazan  manta ba Na gode sosai Allah ya mallaka miki zuciyar fu'ad "ameen nima nagode da wannan adduar taka sai mun had'u goben ta katse kiran ta   koma gadonta ta zauna inda zuciyarta take bata umarnin me zai hana ta tura masa ko da sakon text message ne tunda yaki d'aukar wayarta hannuwanta duka tasa ta rike wayar tasoma rubutu sako  kmr hk.

'YANCINKIWhere stories live. Discover now