Ta jima tsugune a zauren babu wanda ya fito daga cikin gidan kuma babu wanda ya shiga, tana hango cikin gidan saidai tsoro ya hanata shiga.
Zama tayi tana jiran tagame zai faru da ita a wannan gidan? Zasu amsheta ne ko kuwa zasu koreta? Idan ta fita ina zata je?
'karan mashin taji wanda ya sanya gabanta fad'uwa, tana gani ana shigar da mashin d'in cikin gidan amma bata ko motsa ba.
"Subhanallahi" wanda ya shigo da mashin d'in ya ambata, sake 'kulewa tayi a bango cikin tsoro domin bata sani ba ko shima mugu ne irin wad'anda suka bata abinci.
"Aisha!!" Ya fad'a cikin d'aga murya, saida ya sake maimaita sunan sau biyu sannan wata mace ta bayyana daga cikin gidan fuskarta d'auke da kwalliya tana sanye da riga da wando.
"Kingani, ina shigowa na ganta anan".
A tsorace Aisha ta ma'kale bayan mijunta tace "na shiga uku my dear menene wannan? Me takeyi anan?"
"Shine na kiraki na tambayeki ai, shigowa nayi na sameta anan gida kuma a bud'e" yanda suka zuba mata ido ya sanyata takurewa, matse cikin jikinta takeyi amma bata damu ba domin ba shine gabanta ba, makwanci take nema inda zata samu tayi bacci cikin kwanciyar hankali.
"Saida nace ki dinga rufe gida gashinan kingani da ace muguwa ce da Allah kad'ai yasan abinda zatayi".
"Yanzunnan muka shigo fa daga makarantar su Shahid hijabina kawai na ajiye, yanzu abban Shahid ka taimaka ka kirawo mutane a fitar min da ita tun kafin duhu yayi sosai".
Zumbur ta mi'ke jin ance za'a fiddata, 'ko'kari take ta bud'e bakinta ta nemi alfarmarsu su barta ko a nan zauren ne ta kwana saidai babu kalmar da tak fita daga bakinta, cikin tsananin gajiya da sarewa ta dur'kusa inda take hawaye na zuba daga idanunta, da hannu take musu alamun su tausaya mata.
Kallonta baban Shahid yayi cikin tsanaki sannan yace "Aisha gani nake kamar ba mahaukaciya bace, da alamu tana bu'katar taimako".
"Taimakon me? Taimako d'aya zamu mata a kira samari su fitar da ita su kaita gidan me unguwa shine kawai".
Zama tayi a 'kasa baban Shahid yace "Aisha d'ebo mata ruwa tasha, idan da abinci ma kawo mata naga tana cikin wahala".
Wani mugun kallo Aisha ta wurgawa mijinta tace "au mahaukaciyar ma kallonta kakeyi ko? Ba mamaki da manufa biyu kace mu taimaka mata to bazan bata ba".
Ranshi a 'bace ya kalli matar tasa, ya rasa masifar kishi irin nata ba damar ko gaisawa da yaran makwabta 'yammata ta dinga masifa kenan, yanzu akan mahaukaciya tana neman 'bata masa rai, dukda ransa a 'bace yake saida ya tausasa muryarsa yace "haba Aisha wace magana kike haka? Saboda macece ita bazan kalleta na tausaya mata ba? Baku da zance sai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, amma nace ki taimaki 'yar uwarki mace kince a'a".
"Wata macen ba, mata nawa na taimakawa masu bu'katar taimako? Ta Yaya zaka zubawa mace kamar wannan ido babu mayafi a jikinta babu d'ankwali ka 'kurawa jikinta ido sannan kace na taimaka mata? Ka d'auke wannan abin daga gidana bana son ganinta kuma tsinke na bazan bata ba, idan ka fita ka siya mata" Ta 'kare maganar a fusace.
"Aisha ko juna biyun jikinta bazaki duba ki bata ruwan sha ba?"
Ri'ke 'kugu Aisha tayi tace "au har ka lura tana da ciki ko? To wa ya sani ko kai kayi mata?"
Cikin 'kunar rai yayi parking d'in mashin d'insa ya fita sallar magriba ba tareda ya sake kallon inda matarsa take ba.
Yana fita Aisha ta nufi inda wannan baiwar Allah ke tsaye, cikin 'karfi ta janyota ta tankad'a ta waje sannan tace "ki tafi ki nemi inda zaki zauna ba gidana ba, Allah kad'ai yasan sharrin da kika aikata wannan bala'in ya sameki kije ki nemi bola itace ta dace dake".
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...