019

1K 98 10
                                    

Dedicated to @maichantiaicha, thanks for the amazing comments

Matarnan tana barin store d'in Mardiyya suka bita, tabbas tasan aikinta domin saida ta sauka wuri hud'u sannan ta nufi gida, abin mamaki gidansu a can cikin gari yake layin da ta shiga ma mota bata shiga.

Mardiyya sauka tayi ta bi bayanta cikin dabara har saida taga ta shiga wani gida da alamu gidansu ne sannan ta juya.

Plan d'in Mardiyya a yanzu ya sake tsauri domin tasan zai iya fitar da kansa daga wannan plan A d'in nata, a yanzu burinta shine ta had'ashi da ma'aikatansa na Wannan kamfanin. Haka kuwa tayi saida ta zauna ta shirya labari na yanda Mansur ke 'ko'karin d'aurawa ma'aikatansa laifi ta hanyar zamewa ya barsu da bincike sannan kuma ya barsu babu wani aikin yi, sosai tayi emphasizing akan halin da ma'aikatan zasu shiga idan har wannan kamfani ya lalace. Maganganu ne da duk wanda yaci Karo dasu sai yayi waswasi akan Mansur saida ta tabbatar ta had'ashi fad'a da ma'aikatan kamfanin sannan ta tura sa'kon zuwa duniya.

Fitar wannan sa'ko ya sake janyowa Mansur matsala yayin da ma'aikatan da kansu suke confessing yanda suke had'a lemukan bogi cike da 'kazanta da abubuwa masu cutar da lafiya, da farko an fara sau'ka'kawa Mansur binciken amma tunda wad'annan maganganu suka fara fitowa abubuwan suka sake yawa.

Kamfaninsa na kebbi ta koma da bincike saidai shi babu wani illegal activity dake faruwa Banda saye da sayarwa sa akeyi a ciki, kamfanin bashida wani girma haka kayan cikin kamfanin ma sayosu sukeyi su saidawa mutane.

Kafin tayi binciken Cocaine dealing da yakeyi ta fara bin bayan wannan mata da ta gani a store, binciken da tayi ta gano wannan yarinyar tana huld'a ne da manya-manyan mutane wanda yawancinsu one night stand ke had'ata dasu, ma'ana had'uwar dare d'aya, zata je ta biya musu bu'katarsu ne na lokaci d'aya saidai babu wanda ya santa a cikin wad'annan mutanen domin bata bari su 'kare mata kallo tafi ma cin business d'inta idan dare ya tsala.

Shi kansa wannan information da 'kyar Mardiyya ta sameshi domin yarinyar tana aikinta cikin sirri, wani da yake had'ata da mutane Mardiyya ta samu ya d'an fad'a mata wad'annan informations bayan ta rantse Masa taimako take nema daga wajen matar da batada suna, shi dai wannan saurayi yana kiranta ne da LADY.

Mardiyya na kwance a cinyar Mu'azzam tana aikinta yana ta mitar next mission nashi da zai 'badda kama ya koma mai shayi.

Hannunta ta d'aga ta shafi sumar fuskarsa tace "Hubby nifa banga laifin hakan ba dad'i ma nakeji, kaga na farko kana garinnan babu inda zakaje, na biyu aikinnan gaba d'aya wata uku ne kuma zaka dinga zuwa gida at least sau d'aya a sati, to menene na mita?"

Fuskarta ya shafa zuwa kafad'arta yace "kinsan dalili Dee-dee na, ko kwana d'aya banaso nayi ba tare dake ba kuma a wannan time kikayi al'kawarin zamu making baby ko kuwa? Daga ni har ke bamuda wasu cikakken dangi ya kamata ace mun fara gina big family amma aurenmu mun fita daga 3rd year babu baby gida daga ni sai ke....."

Shiru mardiyya tayi domin gaskiya ya fad'a, ya kamata ace zuwa yanzu sun Haifa suma sun ajiye ko dan suga Suma sun fara creating nasu family d'in, saidai ita dama can ba mai son yara bace sannan gani take samun ciki zai kawo mata cikas a wannan tafiya tata, bata san yaushe zata kawo 'karshen mansur ba amma tafi bu'katar ta haifi yaya cikin kwanciyar hankali.

Idanunta kawai ya kalla ya karanci abinda ke yawo a cikin ranta, kissing goshinta yayi ta lumshe ido tace "da zarar ka gama wannan aikin na maka al'kawarin zamuyi making Babies ba ma baby ba".

"Allah ya yarda, ita kuma lady fa ya binciken nata yake?"

Tashi tayi ta sunkuya gaban system d'inta strapless dress d'in dake jikinta ta d'an zame, hannu ya sanya ya gyara mata tace "abinda na lura sana'arta itace barazana ga masu hannu da shuni, zata kwana da mutum.ne kwana d'aya tal kafin ya farka ta gudu, tana d'aukan videos da pictures nata da wannan mutumin da zarar bu'katarta ta tashi ta nemi ya bata kud'i ko ta tona, yanzu yanda zanyi ta bani pictures d'innan shine abin ji, sannan inaso before a gama wannan case d'in mu fidda business d'in Cocaine da yake yi, wannan aikinka ne kasan duk yanda zaka samo sauran evidence kuma ba a 'boye yake sana'ar ba yana yi ne a fili".

HASKEN RANA✔️Where stories live. Discover now